Jehobah Yana Ja-gorar Mutanensa Zuwa ga Rai na Har Abada
“Wannan ita ce hanya, ku bi ta.”—ISHAYA 30:21.
WAƘOƘI: 65, 48
1, 2. (a) Wace alama ce ta ceci rayukan mutane da yawa? (Ka duba hoton da ke wannan shafi.) (b) Wace ja-gora ce Allah yake tanadarwa da za ta sa mutanensa su sami ceto?
AN SAKA wata alama da ke ɗauke da kalaman nan: “Ka Tsaya, Ka Duba Kuma Ka Saurara” a mahaɗan hanyar jirgin ƙasa da hanyar mota a Amirka ta Arewa kusan fiye da shekaru 100 da suka shige. Me ya sa? Domin kada jirgin ƙasa ya buge motoci yayin da suke ƙoƙarin haye hanyar. Mai da hankali ga wannan alamar ya ceci rayukan mutane da yawa.
2 Jehobah yana tanadar mana da abin da ya fi alamun da ke kāre rayuka. Yana ja-gorar mutanensa don su sami rai na har abada kuma yana kāre su daga haɗarurruka. Jehobah yana kama da makiyayi mai ƙauna da ke ja-gorar tumakinsa da kuma sanar da su kada su shiga wuraren da zai sa ransu cikin haɗari.—Karanta Ishaya 30:20, 21.
JEHOBAH YANA JA-GORAR MUTANENSA A KOYAUSHE
3. Ta yaya ‘yan Adam suka gāji mutuwa?
3 Tun daga lokacin da Jehobah ya halicci ‘yan Adam, yana Farawa 2:15-17) Amma Adamu da Hawwa’u sun yi watsi da umurnin da Ubansu mai ƙauna ya ba su. Hawwa’u ta bi shawarar wani halitta. Ta ɗauka cewa maciji ne ya ba ta wannan shawarar. Bayan haka, Adamu ya saurari matarsa. Mene ne sakamakon? Dukansu sun sha wahala kuma suka mutu ba tare bege ba. Ƙari ga haka, saboda rashin biyayyarsu, ‘yan Adam gaba ɗaya sun gāji mutuwa.
ba su umurni ko kuma yi musu ja-gora. Alal misali, a lambun Adnin, Jehobah ya tanadar da umurnin da zai sa ‘yan Adam su yi farin ciki kuma su sami rai na har abada. (4. (a) Me ya sa Allah ya ba da ƙarin dokoki bayan Rigyawa? (b) Ta yaya sabon yanayi ya sa ‘yan Adam suka san ra’ayin Allah?
4 Allah ya ba wa Nuhu umurni da ya ceci rayuka. Bayan Rigyawar, Jehobah ya umurci ‘yan Adam kada su ci ko kuma su sha jini. Me ya sa? Don Jehobah ya ba su izini su soma cin nama. Saboda wannan sabon yanayin, sun bukaci wannan sabuwar doka: “Sai dai nama tare da ransa, watau jininsa ke nan, wannan ba za ku ci ba.” (Farawa 9:1-4) Wannan dokar ta bayyana mana yadda Allah ya ɗauki rai. Shi ne Mahalicci kuma shi ya ba mu rai. Saboda haka, yana da iko ya kafa doka da ta shafi rai. Alal misali, ya kafa doka cewa kada mutum ya yi kisa. A gaban Allah, rai da jini suna da tsarki kuma zai hukunta dukan wanda ya ƙi bin umurnin da ya bayar a kan wannan batun.—Farawa 9:5, 6.
5. Mene ne za mu tattauna yanzu, kuma me ya sa?
5 Bayan zamanin Nuhu, Allah ya ci gaba da yi wa mutanensa ja-gora. Za mu tattauna wasu misalai game da yadda Jehobah ya yi hakan a wannan talifin. Wannan nazarin zai ƙarfafa mu mu bi shawarar da muka tsai da na bin ja-gorar Jehobah daga yanzu har lokacin da za mu shiga sabuwar duniya.
SABUWAR AL’UMMA DA SABABBIN DOKOKI
6. Me ya sa ya zama wajibi wa mutanen Allah su bi dokokin da aka ba su ta hannun Musa, kuma wane ra’ayi ne ya kamata Isra’ilawa su kasance da shi?
6 A zamanin Musa, Jehobah ya ba wa mutanensa dokoki game da ɗabi’a da kuma ibada. Me ya sa? An sake samun canjin yanayi. Isra’ilawa sun yi sama da shekara ɗari biyu suna zaman bauta a ƙasar Masar. Mutanen ƙasar Masar suna bauta wa matattu da gumaka, kuma suna yin wasu abubuwa da yawa da ba sa girmama Allah. Sa’ad da Allah ya ‘yantar da mutanensa daga ƙasar Masar, sun bukaci sababbin dokoki. Za su zama al’ummar da ke bin umurnin Jehobah. Wasu littattafan bincike sun nuna cewa kalmar nan “doka” a Ibrananci tana da alaƙa da wata kalmar da ke nufin “ka ja-goranci, ka bishe, ka umurci.” Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa ya kāre Isra’ilawa daga zina da kuma addinan ƙarya na al’ummai da ke kewaye da su. Isra’ilawa suna samun albarka sa’ad da suka bi umurnin Allah. Amma idan suka ƙi bi, suna fuskantar munanan sakamako.—Karanta Kubawar Shari’a 28:1, 2, 15.
7. (a) Ka bayyana dalilin da ya sa Jehobah ya ba wa mutanensa dokoki. (b) Ta yaya Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta zama ja-gora ga al’ummar Isra’ila?
7 Akwai wani dalili kuma da ya sa Isra’ilawa suka bukaci sababbin dokoki. Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta shirya Isra’ilawa don wani abu mai Galatiyawa 3:19; Ibraniyawa 10:1-10) Ƙari ga haka, Dokar ta kāre zuriyar Almasihu kuma ta taimaka wa Isra’ilawa su gane shi sa’ad da lokacin ya yi. Hakika, Dokar ta kasance kamar ja-gora kuma ta ‘tsare’ su har lokacin zuwan Kristi.—Galatiyawa 3:23, 24.
muhimmanci, wato zuwan Almasihu, Yesu Kristi. Dokar ta tuna wa Isra’ilawa cewa su ajizai ne. Ban da haka, ta taimaka musu su san cewa suna bukatar fansa, wato hadaya marar aibi da zai kawo ƙarshen zunubi gaba ɗaya. (8. Me ya sa muke bukata mu bi ƙa’idodin da ke cikin dokar da aka ba da ta hannun Musa?
8 A matsayinmu na Kiristoci, mu ma za mu amfana daga dokokin da aka ba wa Isra’ilawa. Ta yaya? Za mu iya tsayawa kuma mu duba ƙa’idodin da ke cikin waɗannan dokokin. Ko da yake ba a bukace mu mu bi waɗannan dokokin, za mu iya bin ƙa’idodin a harkokinmu na yau da kullum da kuma a ibadarmu ga Jehobah. Jehobah ya sa an rubuta waɗannan dokokin a cikin Littafi Mai Tsarki don mu koyi darussa cikinsu, mu bi ƙa’idodinsu kuma mu fahimci cewa koyarwar Yesu ta fi waɗannan muhimmanci. Alal misali Yesu ya ce: “Kun ji aka faɗi, Ba za ka yi zina ba: amma ni ina ce muku, dukan wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” Wannan yana nufin cewa muna bukatar mu guji zina, kuma mu daina yin tunanin banza da sha’awar banza.—Matta 5:27, 28.
9. Wane sabon yanayi ne ya sa Allah ya ba da sababbin dokoki?
9 Bayan Yesu ya zo a matsayin Almasihu, Jehobah ya ba da sababbin dokoki kuma ya ba da ƙarin bayani game da nufinsa. Me ya sa aka bukaci hakan? A shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, Jehobah ya yi watsi da al’ummar Isra’ila kuma ya zaɓi ikilisiyar Kirista a matsayin mutanensa. Hakan ya sa yanayin mutanen Allah ya sake canjawa.
JA-GORA GA ISRA’ILA TA ALLAH
10. Me ya sa aka tanadar wa ikilisiyar Kirista sababbin dokoki, kuma ta yaya waɗannan dokokin suka bambanta da waɗanda aka ba wa Isra’ilawa?
10 Jehobah ya ba wa Isra’ilawa doka ta hannun Musa don yana so su san yadda ya kamata su yi rayuwa da kuma ibada. Somawa daga ƙarni na farko, mutanen Allah sun ƙunshi mutanen da suka fito daga al’ummai da kuma al’ada dabam-dabam, kuma ana kiransu “Isra’ila ta Allah.” Suna cikin ikilisiyar Kirista a ƙarƙashin sabon alkawari. Jehobah ya ba su sababbin dokoki ƙarin umurni game da yadda za su yi rayuwa da kuma ibada. Hakika, “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.” (Ayyukan Manzanni 10:34, 35) Suna bin “shari’ar Kristi” da ke bisa ƙa’idodi da aka rubuta a zukatansu, ba a kan dutse ba. Wannan shari’a ko doka tana ja-gorar Kiristoci kuma tana amfanar su a duk inda suke zama.—Galatiyawa 6:2.
11. Waɗanne dokoki biyu ne da Yesu ya bayar suka shafi rayuwar Kirista?
11 Waɗanda suke cikin wannan sabuwar al’umma, wato ‘Isra’ila ta Allah’ sun amfana daga ja-gorar da Jehobah yake bayarwa ta wurin Yesu. Kafin Yesu ya gabatar da sabon alkawarin, ya ba su dokoki masu muhimmanci guda biyu. Na farko game da wa’azin bishara. Na biyu kuma game da yadda ya kamata Kiristoci su bi da juna. Waɗannan umurnin don dukan Kiristoci ne kuma sun shafe mu a yau, ko da muna da begen yin rayuwa har abada a sama ko kuma a duniya.
12. Ta yaya tsarin wa’azin bishara ya canja?
12 A dā mutanen al’ummai sukan je ƙasar Isra’ila don su bauta wa Jehobah. (1 Sarakuna 8:41-43) Amma daga baya, Yesu ya ba da umurnin da ke Matta 28:19, 20. (Karanta.) Yesu ya gaya wa almajiransa su “tafi,” wato su je su yi wa’azi wa dukan mutane. A Fentakos ta shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, Jehobah ya nuna cewa yana so a yi wa’azin bishara a dukan duniya. A ranar, ruhu mai tsarki ya sauko a kan almajirai wajen 120 na sabuwar ikilisiya da aka kafa kuma suka soma wa’azi wa asalin Yahudawa da wasu mabiyan addinin Yahudawa a harsuna dabam-dabam. (Ayyukan Manzanni 2:4-11) Bayan haka, suka soma yi wa Samariyawa wa’azin bishara. Sa’an nan, a shekara ta 36 bayan haihuwar Yesu, suka soma yin wa’azi ga mutanen al’ummai da ba a yi musu kaciya ba. Hakan yana nufin cewa suna bukata su yi wa’azin bishara wa kowane mutum da ke raye!
13, 14. (a) Mene ne bin “sabuwar doka” da Yesu ya bayar ya ƙunsa? (b) Mene ne muka koya daga misalin da Yesu ya kafa?
13 Ƙari ga haka, Yesu ya ba mu “sabuwar doka” game da yadda ya kamata mu bi da ‘yan’uwanmu maza da mata. (Karanta Yohanna 13:34, 35.) Wajibi ne mu nuna cewa muna ƙaunarsu a koyaushe. Muna bukata mu sadaukar da ranmu a madadinsu. Ba a ambaci hakan a dokar da aka wa Isra’ilawa ba.—Matta 22:39; 1 Yohanna 3:16.
14 Babu wanda ya nuna cewa yana ƙaunar mutane kamar Yesu. Ya so almajiransa sosai har ya mutu a madadinsu. Kuma ya bukaci dukan mabiyansa su yi hakan. Saboda haka, wajibi ne mu kasance a shirye don mu sha wahala ko kuma mu ba da ranmu a madadin ‘yan’uwanmu.—1 Tasalonikawa 2:8.
YADDA JEHOBAH YAKE MANA JA-GORA A YAU DA KUMA A NAN GABA
15, 16. Wane sabon yanayi ne muka samu kanmu a ciki, kuma ta yaya Allah yake ja-gorarmu?
15 Yesu ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” domin ya ba mabiyansa “abincinsu a lotonsa.” (Matta 24:45-47) Wannan abincin ya haɗa da umurnai masu muhimmanci don mutanen Allah sa’ad da aka sami canjin yanayi. Ta yaya yanayinmu ya canja?
16 Muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe” kuma nan ba da daɗewa ba, za mu fuskanci ƙunci da ba a taɓa yi ba. (2 Timotawus 3:1; Markus 13:19) Ban da haka, an jefar da Shaiɗan da aljannunsa zuwa duniya kuma sun jawo azaba wa ‘yan Adam. (Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12) Ƙari ga haka, muna bin umurnin Yesu ta wajen yin wa’azi ga mutane da yawa a harsuna dabam-dabam fiye da yadda muke yi a dā!
17, 18. Wane mataki ne ya kamata mu ɗauka game da umurnan da muke samu yanzu?
17 Ƙungiyar Jehobah tana tanadar mana da kayayyakin aiki da suke taimaka mana mu yi wa’azin bishara. Shin kana amfani da su? Muna samun ja-gora game da yadda za mu yi amfani da waɗannan kayayyakin aiki da kyau a taron ikilisiya. Ya kamata mu ɗauki waɗannan umurnan a matsayin ja-gora daga wurin Jehobah.
18 Muna bukata mu saurari dukan umurnin da Jehobah yake tanadar mana Matta 24:21) Bayan haka, za a tanadar mana da sababbin dokoki don yin rayuwa a sabuwar duniya da babu tasirin Shaiɗan.
ta ƙungiyarsa. Idan muka yi biyayya yanzu, zai kasance mana da sauƙi mu bi umurnin da za a ba mu a lokacin “ƙunci mai-girma,” a lokacin da za a halaka duniyar Shaiɗan gaba ɗaya. (19, 20. Waɗanne littattafai ne za a buɗe, kuma mene ne sakamakon?
19 A zamanin Musa, al’ummar Isra’ila sun bukaci sababbin dokoki. Saboda haka, Allah ya ba su Doka ta hannun Musa. Daga baya, an bukaci ikilisiyar Kirista su bi “shari’ar Kristi.” Hakazalika, Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana cewa za a tanadar mana da littattafai da ke ɗauke da sababbin dokoki a sabuwar duniya. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 20:12.) Mai yiwuwa a lokacin, waɗannan littattafan za su bayyana abin da Jehobah yake bukata daga ‘yan Adam. Kuma dukan mutane, har da waɗanda aka ta da daga matattu za su san abin da Allah yake bukata daga gare su ta yin nazarin waɗannan littattafan. Ƙari ga haka, littattafan za su taimaka mana mu san ra’ayin Jehobah sosai. Za mu kuma ƙara fahimtar Littafi Mai Tsarki sosai. A Aljanna, za mu bi da juna cikin ƙauna, mutunci da kuma daraja. (Ishaya 26:9) Hakika, za mu koyi abubuwa da yawa kuma mu koya wa wasu a lokacin da Sarkinmu, Yesu Kristi ya soma sarauta a duniya!
20 Idan muka bi umurnin da aka “rubuta a cikin littattafan” kuma muka kasance da aminci ga Jehobah a lokacin gwaji na ƙarshe, zai rubuta sunayenmu a cikin “littafin rai.” Ta hakan, za mu sami rai na har abada! Saboda haka, muna bukata mu DAKATA don mu karanta abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, mu DUBA don mu fahimci abin da yake nufi a gare mu, kuma mu SAURARA ta wajen bin ja-gorar da Allah yake tanadar mana yanzu. Idan muka yi waɗannan abubuwan, za mu iya tsira a lokacin ƙunci mai girma kuma mu ci gaba da koyan abubuwa game da Allahnmu mai ƙauna mai hikima, Jehobah, har abada.—Mai-Wa’azi 3:11; Romawa 11:33.