Fansa “Cikakkiyar Kyauta” Ce Daga Jehobah
‘Kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta daga . . . wurin Uban ne.’
WAƘOƘI: 148, 109
1. Waɗanne albarka muka samu saboda fansa?
HADAYAR fansa da Yesu ya yi ya sa mutane za su sami albarka sosai, kuma hakan zai sa dukan ‘ya’yan Adamu masu adalci su zama ‘ya’yan Allah. Ƙari ga haka, fansar ta ba mu zarafin yin rayuwa har abada. Ban da sa ‘yan Adam su kasance da bege a nan gaba, mutuwar da Yesu ya yi ta sa mun san gaskiya game da wasu batutuwa masu muhimmanci.
2. (a) Waɗanne batutuwa masu muhimmanci ne aka ambata a addu’ar da Yesu ya koya wa almajiransa? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Me za mu bincika a wannan talifin?
2 Shekaru biyu kafin Yesu ya ba da ransa fansa, ya koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a. Ya ce: ‘Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.’ (Mat. 6:
“A TSARKAKE SUNANKA”
3. Mene ne sunan Jehobah yake wakilta, kuma ta yaya Shaiɗan ya ɓata wannan suna mai tsarki?
3 A addu’ar da Yesu ya koya wa almajiransa, tsarkake sunan Allah ne abu na farko da ya ambata. Sunan Jehobah yana wakiltar shi da kansa da martabarsa da ikonsa da kuma adalcinsa. A wani wuri kuma Yesu ya kira shi “Uba mai-tsarki.” (Yoh. 17:11) Da yake Jehobah mai tsarki ne, duk ƙa’idodi da dokoki da ya bayar suna da tsarki. Duk da haka, Shaiɗan ya yi ƙarya a gonar Adnin cewa bai kamata Jehobah ya kafa wa ‘yan Adam dokoki ba. Wannan ƙaryar da Shaiɗan ya yi ne ya ɓata sunan Jehobah mai tsarki.
4. Ta yaya Yesu ya tsarkake sunan Allah?
4 Yesu yana son sunan Jehobah sosai. (Yoh. 17:
5. Ta yaya za mu tsarkake sunan Allah?
5 Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar sunan Jehobah? Ta wurin halinmu. Jehobah yana son mu zama masu tsarki. (Karanta 1 Bitrus 1:
6. Ko da yake mu ajizai ne, me ya sa Jehobah yake ganinmu a matsayin masu adalci?
6 Jehobah yana gafarta ma waɗanda suke ba da gaskiya gare shi ta wurin fansar da Yesu ya bayar. Jehobah yana amincewa da waɗanda suke so su bauta masa kuma yana ɗaukansu a matsayin bayinsa. Ƙari ga haka, yana ɗaukan shafaffun Kiristoci a matsayin ‘ya’yansa, “waɗansu tumaki” kuma a matsayin abokansa. (Yoh. 10:16; Rom. 5:
“MULKINKA SHI ZO”
7. Wane albarka ne za a samu sa’ad da Mulkin Allah ya soma sarauta?
7 Abu na biyu da Yesu ya roƙa a addu’arsa shi ne: “Mulkinka shi zo.” Ta yaya fansa take da alaƙa da Mulkin Allah? Fansar ta taimaka wajen tattara mutane 144,000 da za su yi sarauta a matsayin sarakuna da firistoci da Yesu a sama. (R. Yoh. 5:
8. (a) Ta yaya Yesu ya taimaka wa almajiransa su san muhimmancin Mulkin Allah? (b) Ta yaya muke tallafa wa Mulkin a yau?
8 Nan da nan bayan Yesu ya yi baftisma, ya taimaka wa almajiransa su san muhimmancin Mulkin Allah. Yesu ya yi “bishara ta mulkin Allah” a duk wuraren da ya je. (Luk. 4:43) Kafin Yesu ya koma sama, ya gaya wa almajiransa su riƙa yin bishara har “iyakan duniya.” (A. M. 1:
“ABIN DA KAKE SO, A YI SHI”
9. Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah zai cika nufinsa ga mutane?
9 Abu na uku da Yesu ya roƙa a addu’arsa shi ne: “Abin da kake so, a yi shi.” Me yake nufi sa’ad da ya yi furucin nan? Da yake Jehobah shi ne mahalicci, idan ya ce wani abu zai faru, kamar abun ya riga ya faru ne. (Isha. 55:11) Tawayen da Shaiɗan ya yi ba zai hana Allah ya cika nufinsa ga ‘yan Adam ba. Tun farko, Jehobah ya so Adamu da Hauwa’u su haifi kamiltattun yara da za su mamaye duniya. (Far. 1:28) Da a ce Adamu da Hauwa’u ba su haifi yara ba, da nufin Jehobah cewa mutane su mamaye duniya bai cika ba. Shi ya sa bayan da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, Jehobah ya bar su su haifi yara. Ta wurin fansa, Allah ya ba mutanen da suka ba da gaskiya a gare shi zarafin zama kamiltattu kuma su yi rayuwa har abada. Jehobah yana ƙaunar mutane kuma yana son waɗanda suke masa biyayya su yi irin rayuwar da yake so mutane su yi.
10. Ta yaya mutanen da suka mutu za su amfana daga fansar?
10 Biliyoyin mutanen da suka mutu ba tare da sun sami zarafin sanin Jehobah da bauta masa kuma fa? Fansar za ta sa a ta da su kuma Jehobah zai ba su damar koya game da shi kuma su sami rai na har abada. (A. M. 24:15) Jehobah ba ya son mutane su mutu amma su ci gaba da rayuwa. Da yake shi ne Mai ba da rai, zai zama Uba ga dukan waɗanda aka ta da daga mutuwa. (Zab. 36:9) Shi ya sa Yesu ya ce mu riƙa addu’a cewa: ‘Ubanmu wanda ke cikin sama.’ (Mat. 6:9) Jehobah ya ba Yesu ikon ta da matattu. (Yoh. 6:
11. Mene ne Allah zai yi wa “taro mai girma”?
11 Jehobah ba ya nuna karimci ga mutane kalilan kawai. Yesu ya ce: ‘Gama iyakar wanda za ya aika nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ‘yar’uwata, da uwata.’ (Mar. 3:35) Nufin
12. Ta yaya addu’ar da Yesu ya yi ta nuna nufin Allah ga mutane masu adalci?
12 Addu’ar da Yesu ya koyar ta nuna nufin Jehobah ga mutane masu adalci. Don haka, muna son mu yi iya ƙoƙarinmu don mu tsarkake sunan Jehobah. (Isha. 8:13) Sunan Yesu yana nufin “Jehobah Mai-ceto Ne.” Kuma ceton da muka samu ta wurin fansar yana ɗaukaka sunan Jehobah. Mulkin Allah ne zai sa mutane su sami albarkar da fansar ta tanadar. Babu shakka, addu’ar Yesu ta tabbatar mana cewa babu abin da zai hana Allah ya cika nufinsa.
KA NUNA WA JEHOBAH KANA GODIYA DON FANSA
13. Mene ne baftismar da muke yi take nufi?
13 Hanya ta musamman da za mu nuna cewa muna godiya don tanadin fansa da Jehobah ya yi mana ita ce ta wurin yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma yin baftisma. Baftismar da muke yi tana nuna cewa mu “na Ubangiji” ne. (Rom. 14:8) Ban da haka ma, hakan yana nuna cewa muna roƙon Allah ya ba mu zuciyar kirki. (1 Bit. 3:21) Jehobah yana amsa addu’ar nan ta wurin yin amfani da jinin da Yesu ya yi amfani da shi don ya fanshe mu kuma mu kasance da tsabta. Muna da tabbaci cewa zai cika dukan alkawarin da ya yi mana.
14. Me ya sa aka umurce mu mu riƙa ƙaunar maƙwabtanmu?
14 Ta wace hanya ce kuma za mu iya nuna godiya don fansa? Da yake Jehobah yana nuna ƙauna a duk sha’anin da yake yi da mutane, ya kamata dukan bayinsa su riƙa nuna ƙauna. (1 Yoh. 4:
FANSA TANA SA MU SAMI ALBARKA DAGA JEHOBAH
15. (a) Wane albarka muke samuwa daga Jehobah yanzu? (b) Wane albarka za mu samu a nan gaba?
15 An gafarta mana zunubanmu, don mun ba da gaskiya ga fansa. Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa za a iya “shafe” zunubanmu. (Karanta Ayyukan Manzanni 3:
16. Ta yaya fansar ta ‘yantar da mu?
16 Babu abin da Shaiɗan zai iya yi don ya hana mutanen da suka ba da gaskiya kasancewa cikin iyalin Allah. Yesu ya zo duniya kuma ya mutu ‘sau ɗaya’ kawai. Don haka, an fanshe mu har abada. (Ibran. 9:
17. Ta yaya ka amfana daga ƙaunar da Jehobah yake yi maka?
17 Mun tabbata cewa Allah zai cika alkawarin da ya yi mana. Kamar yadda tsarin halittun da Allah ya yi ba sa canjawa, Jehobah ba zai taɓa karya alkawarinsa ba. (Mal. 3:6) Ban da rai da Allah ya ba mu, ya ba mu wata kyauta kuma. Yana ƙaunarmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunar da Allah ke yi mana. Allah shi ne ƙauna.” (1 Yoh. 4:16, Littafi Mai Tsarki) Duniya za ta zama aljanna kuma kowane mutum a duniya zai riƙa nuna ƙauna. Bari dukanmu da mala’iku da ke sama mu ce: “Albarka, da ɗaukaka, da hikima, da godiya, da daraja, da iko, da ƙarfi, ga Allahnmu har zuwa zamanun zamanai. Amin.”