Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Mece ce “maganar Allah” da littafin Ibraniyawa 4:12 ta ce tana da rai da kuma ƙarfin aiki?
Wannan ayar ta nuna cewa manzo Bulus yana magana ne game da nufin Allah da Littafi Mai Tsarki yake magana a kai.
A littattafanmu, ana yawan ambata littafin Ibraniyawa 4:12 don a nuna cewa Littafi Mai Tsarki yana iya gyara rayuwar mutane, kuma hakan gaskiya ce. Amma yin nazari a kan ainihin abin da Ibraniyawa 4:12 take magana a kai za ta taimaka mana sosai. Bulus yana gaya wa Kiristoci Ibraniyawa cewa su riƙa yin nufin Allah. A cikin Littafi Mai Tsarki an bayyana abin da nufin Allah yake nufi. Bulus ya ba wa Kiristocin misalin Isra’ilawan da aka ceto daga ƙasar Masar. Waɗannan Isra’ilawan suna da begen shiga ƙasa “mai-zubar da madara da zuma,” inda za su huta da kuma ji daɗin rayuwa.—Fit 3:8; K. Sha. 12:9, 10.
Wannan shi ne nufin Allah ga Isra’ilawa. Amma daga baya, sun yi rashin biyayya kuma ba su nuna bangaskiya ba. Hakan ya sa yawancinsu ba su shiga ƙasar alkawari ba. (Lit. Lis. 14:30; Josh. 14:6-10) Amma Bulus ya ce har yanzu da akwai “alkawari na shiga cikin hutun [Allah].” (Ibran. 3:16-19; 4:1) Wannan ‘alkawarin’ yana ɗaya daga cikin nufin Allah. Mu ma muna bukatar mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki don mu san nufin Allah kuma mu yi biyayya kamar yadda Kiristoci Ibraniyawa suka yi. Ƙari ga haka, Bulus ya yi ƙaulin wani sashen littafin Farawa 2:2 da kuma Zabura 95:11 don ya nuna cewa wannan alkawarin yana cikin Littafi Mai Tsarki.
Hakika, ya kamata mu yi farin cikin sanin cewa an “bar mana alkawari na shiga cikin hutun [Allah].” Mun gaskata cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da shiga cikin hutun Allah gaskiya ce, kuma muna yin iya ƙoƙarinmu don mu shiga wannan hutun. Amma ba ta wajen bin dokar da Allah ya ba wa Musa ko kuma ta yin wasu ayyuka dabam don Jehobah ya amince da mu ne za mu shiga cikin hutunsa ba. Maimakon haka, muna yin biyayya ga Jehobah da kuma nufinsa domin muna da bangaskiya. Ƙari ga abin da aka ambata ɗazu, miliyoyin mutane a faɗin duniya sun soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki don su san nufin Allah. Hakan ya sa yawancinsu sun canja salon rayuwarsu, sun kasance da bangaskiya kuma suka yi baftisma. Wannan canjin da suka yi ya nuna cewa “maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa kuma.” Kamar yadda aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, nufin Allah tana shafan rayuwarmu kuma za ta ci gaba da gyara rayuwarmu.