TARIHI
“Na Koyi Abubuwa da Yawa Daga Wurin ’Yan’uwa!”
NI MATASHI ne sa’ad da aka tilasta mini in shiga aikin soja a Faransa. Mun ya da zango a tuddai a ƙasar Aljeriya, wurin da ake yaƙi sosai. Wata rana da daddare, ina gadi ni kaɗai, riƙe da bindiga tsakanin buhuna cike da ƙasa. Sai na ji wani yana takowa kuma hakan ya sa na tsorata sosai. Ni matashi ne a lokacin, ba na so a kashe ni, kuma ba na so in kashe kowa. Sai na roƙi Allah ya taimaka mini.
Wannan abin ban-tsoro da ya faru ya canja rayuwata, domin a lokacin ne na soma ƙoƙari in san Allah. Kafin in ba ku labarin abin da ya faru a daren nan, zan so in gaya muku abubuwan da suka faru da ni a lokacin da nake yaro, da suka sa na so in koya game da Allah.
ABUBUWAN DA NA KOYA DAGA MAHAIFINA
An haife ni a shekara ta 1937 a Guesnain, wani birni da ake haƙa ma’adinai a arewacin Faransa. Na koyi muhimmancin yin aiki a wurin mahaifina wanda yake haƙa ma’adinai. Mahaifina ya koya mini in tsani rashin adalci. Ya ga cewa ana wulaƙanta ma’aikata a wurin haƙa ma’adinan kuma ana sa su su yi aiki a yanayi mai haɗari. Don ya taimaka musu, sai mahaifina ya shiga ƙungiyoyin da suke kāre hakkin ma’aikatan. Ƙari ga haka, munafuncin da limamai suke nunawa ya sa mahaifina fushi. Da yawa cikinsu suna da abubuwan biyan bukata, amma duk da haka, suna karɓan kuɗi da abinci daga hannun ma’aikata talakawa a wurin haƙa ma’adinan. Abubuwan da limaman suke yi ya ɓata wa mahaifina rai, shi ya sa bai koya mini kome game da Allah ba. Bai taɓa faɗin kome game da addini ba.
Ni ma na tsani rashin adalci sa’ad da nake girma. Wannan rashin adalci ya ƙunshi bambanci da wasu ke nuna wa baƙin haure da ke zama a ƙasar Faransa. Nakan buga ƙwallo tare da yaran baƙin haure kuma na ji daɗin yin wasa da su. Ban da haka, mahaifiyata ’yar ƙasar Polan ce ba ’yar Faransa ba. Na yi alla-alla dukan mutane su riƙa zaman lafiya da juna kuma su daina nuna bambanci.
NA SOMA TUNANI SOSAI GAME DA RAYUWA
Gwamnati ta tilasta mini in shiga aikin soja a shekara ta 1957. Yadda na sami kaina a tuddan ƙasar Aljeriya cikin daren da na ambata ɗazu ke nan. Sa’ad da na “roƙi Allah ya taimaka mini,” sai na ga cewa ba ƙarar taƙun mutum ba ne, amma na jakin daji ne! Sai hankalina ya kwanta! Duk da haka, abin da ya faru da kuma yaƙin da ake yi ya sa ni tunani sosai game da rayuwa. Na yi tambayoyi kamar, ‘Me ya sa Allah ya halicce mu? Allah ya damu da mu kuwa? Za mu taɓa samun kwanciyar hankali kuwa?’
Daga baya, sa’ad da na ziyarci iyayena, na haɗu da wani Mashaidin Jehobah. Ya ba ni Littafi Mai Tsarki juyin La Sainte Bible wanda ’yan Katolika suka fassara zuwa Faransanci. Na soma karanta littafin sa’ad da na koma Aljeriya. Ayoyin da suka ratsa zuciyata su ne Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4. Wurin ya ce: “Wurin zaman Allah yana tare da ’yan Adam! . . . Zai share musu dukan hawaye daga idanunsu. Babu sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun ɓace.” Ban taɓa karanta ayoyin nan ba. Na tambayi kaina, ‘Hakan zai taɓa faruwa kuwa?’ A lokacin, kusan ban san kome game da Allah ko Littafi Mai Tsarki ba.
Bayan na bar aikin soja a shekara ta 1959, na haɗu da wani Mashaidi mai suna François kuma ya koya mini abubuwa da yawa a Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ya nuna mini a Littafi Mai Tsarki cewa Allah yana da suna kuma sunansa Jehobah ne. (Zab. 83:18) Ƙari ga haka, ya nuna mini cewa a nan gaba, Jehobah zai sa a yi adalci a duniya, zai mai da ita aljanna kuma zai cika annabcin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4.
Koyarwar ta ratsa zuciyata, amma ta sa na yi fushi sosai da limaman coci kuma na so in nuna wa kowa cewa ina tir da koyarwarsu da ba sa cikin Littafi Mai Tsarki! Da yake na ɗauki ra’ayin mahaifina, na so in yaƙi rashin adalci nan da nan!
François da sauran abokaina Shaidu sun taimaka mini in kame kaina. Sun bayyana mini cewa bai kamata Kiristoci su shari’anta mutane ba, amma su taimaka musu ta wajen yi musu wa’azi game da Mulkin Allah. Abin da Yesu ya yi ke nan kuma abin da ya ce mabiyansa su yi ke nan. (Mat. 24:14; Luk. 4:43) Ban da haka, na koyi yadda zan riƙa yi wa mutane magana cikin ladabi da kuma basira, ko da ban amince da abin da suka yi imani da shi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada mai hidimar Ubangiji ya zama mai yawan gardama, amma dai ya zama mai kirki ga kowa.”—2 Tim. 2:24.
Na yi canje-canje a rayuwata kuma na yi baftisma a wani taron da’ira a shekara ta 1959. A taron, na haɗu da wata ’yar’uwa mai suna Angèle kuma na soma son ta. Sai na soma zuwa taro a K. Mag. 19:14.
ikilisiyar da take kuma muka yi aure a shekara ta 1960. Angèle mace ce mai hankali kuma ita kyauta ce daga Jehobah.—NA KOYI ABUBUWA DA YAWA DAGA ’YAN’UWA MASU HIKIMA
A cikin shekarun da suka shige, na koyi darussa masu muhimmanci daga ’yan’uwa maza da suka manyanta. Abu mafi muhimmanci da na koya shi ne: Za mu yi nasara a dukan ayyukan da muke yi idan mu masu sauƙin kai ne kuma muka bi shawarar da ke Karin Magana 15:22. Ayar ta ce: “Tare da shawara mai yawa, akwai cin nasara.”
A shekara ta 1964, na bukaci in bi shawarar da ke wannan ayar. A shekarar, na soma yin hidimar mai kula da da’ira, ina ziyartar ikilisiyoyi don in ƙarfafa ’yan’uwa kuma in taimaka musu su kusaci Jehobah. Ni ɗan shekara 27 ne a lokacin kuma ban iya aikin sosai ba. Saboda haka, na yi kurakure sosai, amma na koyi darussa daga kurakuraina. Ƙari ga haka, na koyi darussa masu kyau daga mashawarta da suka manyanta.
Na tuna wani abu da ya faru sa’ad da na soma hidimar mai kula da da’ira. Bayan na ziyarci wata ikilisiya a birnin Paris, wani ɗan’uwa da ya manyanta ya ce yana so ya yi magana da ni, sai na ce “to.”
Ya ce, “Ɗan’uwa Louis, wane ne likita yake ziyarta a gida?”
Sai na ce, “Marar lafiya.”
Ya ce: “Gaskiya ne. Amma na lura cewa ka fi zama tare da waɗanda suke da dangantaka mai kyau da Jehobah, kamar dattawa. A ikilisiyarmu, akwai ’yan’uwa da yawa da suka yi sanyin gwiwa da sababbi ko kuma waɗanda suke jin kunya. Za su yi farin ciki sosai idan kana kasancewa tare da su ko ziyartar gidajensu don ka ci abinci tare su.”
Shawarar wannan ɗan’uwan tana da kyau sosai. Ganin yadda yake ƙaunar bayin Jehobah ya ratsa zuciyata sosai. Duk da cewa ya yi mini wuya in amince cewa na yi kuskure, na bi shawararsa. Ina godiya ga Jehobah domin irin waɗannan ’yan’uwa.
A shekara ta 1969 da 1973, an ba ni aikin kula da Sashen Abinci a taron ƙasashe da aka yi a yankin Colombes da ke Paris. A taron da aka yi a shekara ta 1973, mun bukaci mu ciyar da mutane wajen 60,000 na kwana biyar! Ban san yadda za mu yi hakan ba. Amma abin da ke Karin Magana ya taimaka mana mu magance wannan matsalar, ayar ta ce mu nemi shawara daga wasu. Na nemi shawara daga ’yan’uwan da suka manyanta kuma suka daɗe suna sana’ar abinci. Wasu a cikinsu mahauta ne da manoma da masu dafa abinci da kuma masu saye-saye. Tare da waɗannan ’yan’uwan, mun yi nasara a wannan aiki mai wuya. 15:22
A shekara ta 1973, an ce ni da matata mu soma hidima a Bethel a Faransa. Aiki na farko da aka ba ni yana da wuya sosai, wato in riƙa kai wa ’yan’uwa a ƙasar Kamaru da ke Afirka littattafai. A shekara ta 1970 da 1993, an saka wa aikinmu takunkumi a ƙasar. Na ɗauka ba zan iya yin wannan aikin ba. Wataƙila ɗan’uwan da ke kula da aikinmu a Faransa a lokacin ya lura cewa ina ganin ba zan iya yin wannan aikin ba, sai ya ƙarfafa ni, ya ce: “’Yan’uwanmu a Kamaru suna bukatar littattafan sosai. Muna bukatar mu kula da su!” Abin da muka yi ke nan.
Na yi tafiya sau da yawa zuwa ƙasashen da ke maƙwabtaka da ƙasar Kamaru don in haɗu da dattawa da ke ƙasashen. Waɗannan ’yan’uwa masu hikima sun taimaka mini in sami hanyoyin tura littattafan don ’yan’uwa a Kamaru su riƙa samu a kan lokaci. Jehobah ya albarkaci aikinmu. An yi wajen shekara 20 ana kai wa ’yan’uwan da ke Kamaru Hasumiyar Tsaro da kuma littafin da muke taron tsakiyar mako da shi a lokacin, wanda ake kira Our Kingdom Service.
NA KOYI ABUBUWA DA YAWA DAGA MATATA
Tun daga lokacin da muka soma fita zance, na lura cewa Angèle tana da halaye masu kyau. Amma da muka yi aure ne na daɗa ganin yadda take nuna halayen nan. Alal misali, da yamma a ranar aurenmu, ta ce in yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mana mu bauta masa a hidima ta cikakken lokaci a matsayin ma’aurata. Jehobah ya amsa wannan addu’ar.
Ibran. 13:17) Na amince da abin da ta faɗa! Sai muka je Bethel yin hidima. Matata tana da hikima kuma tana ƙaunar Jehobah sosai. Waɗannan halayen sun ƙarfafa dangantakarmu kuma sun taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau.
Matata ta taimaka mini in dogara ga Jehobah sosai. Alal misali, a shekara ta 1973, a lokacin da aka ce mu je yin hidima a Bethel, ban so hakan ba domin ina jin daɗin hidimar da nake yi a matsayin mai kula da da’ira. Amma matata ta tuna min cewa mun yi alkawarin bauta wa Jehobah duk rayuwarmu. Ya kamata mu yi kowane aiki da ƙungiyar Jehobah ta ce mu yi. (Yanzu da mun tsufa, matata ta ci gaba da zama mace tagari kuma tana taimaka mini sosai. Alal misali, don in iya halartan makarantu a ƙungiyar Jehobah da ake yi da Turanci, ni da matata mun soma aiki tuƙuru don mu koyi yaren sosai. Hakan ya sa muka soma tarayya da ikilisiyar da ake Turanci duk da cewa mun ba shekara 70 baya a lokacin. Ya yi mini wuya in sami lokacin koyan wani yare, domin ayyukan da nake yi a matsayin memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah a Faransa. Amma ni da matata mun taimaka wa juna. Ko da yake yanzu mun ba shekaru 80 baya, muna yin nazari a Faransanci da kuma Turanci kafin mu je taro. Ƙari ga haka, muna yin ƙoƙari sosai don mu riƙa halartan taro da kuma fita wa’azi tare da ’yan’uwa a ikilisiyarmu. Jehobah ya taimaka mana mu koyi Turanci.
Mun sami wata albarka ta musamman a shekara ta 2017. Ni da matata mun sami gatan halartan Makaranta don Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah da Matansu, wanda ake yi a Cibiyar Koyarwa da Ke Patterson a jihar New York.
Jehobah Babban Malami ne. (Isha. 30:20) Don haka, ba abin mamaki ba ne cewa dukanmu, yara da tsofaffi, muna samun koyarwa mai kyau! (M. Sha. 4:5-8) Hakika, na ga cewa zai yiwu ’yan’uwa maza da mata su yanke shawara mai kyau a rayuwa kuma su bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsu. Littafin Karin Magana 9:9 ta ce: “Ka koya wa mai hikima, zai ƙara zama mai hikima. Ka koya wa mai adalci, zai ƙara karɓar koyarwa.”
A wasu lokuta, nakan yi tunani game da ranar nan da daddare a tuddan ƙasar Aljeriya wajen shekaru 60 da suka shige. A wannan daren, ban san cewa zan iya yin rayuwa mai inganci haka ba. Na koyi abubuwa da yawa daga wasu! Jehobah ya yi wa ni da matata albarka kuma ya ba mu rayuwa mai gamsarwa. Don haka, mun ƙuduri niyya cewa ba za mu taɓa daina koyan abubuwa daga Ubanmu na sama da ’yan’uwa maza da mata da suka manyanta kuma suke ƙaunar sa ba.