Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yaya Ainihin Kamanin Yesu Yake?

Yaya Ainihin Kamanin Yesu Yake?

Babu wanda yake da ainihin hoton Yesu. Sa’ad da yake duniya, bai taɓa ɗaukan hoto ba kuma ba a taɓa zana shi ba. Duk da haka, shekaru da yawa yanzu, masu zane-zane sun zana hotunansa da dama.

Gaskiya ne cewa waɗannan masu zane-zanen ba su san ainihin kamanin Yesu ba. Yawancinsu sukan zana shi ne bisa al’adarsu, wasu kuma bisa ga imaninsu. Har ila, wasu suna zana shi yadda wanda yake bukatar hoton ya gaya musu su yi. Amma, yadda suke zana Yesu yana iya sa mutane su yi tunanin da bai dace ba game da shi da kuma koyarwarsa.

Wasu masu zane suna zana Yesu kamar mutumin da ba shi da ƙarfi kuma yake da dogon suma da gemu ko kuma yake baƙin ciki. A wasu zane-zanen kuma, ana zana Yesu a matsayin wanda yake da iko sosai ko yake da tsarki ko kuma wanda ba za mu iya kusantar sa ba. Shin waɗannan zane-zanen suna nuna ainihin kamanin Yesu ne? Ta yaya za mu san ainihin kamaninsa? Hanya ɗaya da za mu iya sanin hakan shi ne ta wajen bincika wasu bayanan da ke Littafi Mai Tsarki da za su iya taimaka mana mu san yadda kamaninsa yake. Bayanan za su sa mu kasance da ra’ayin da ya dace game da shi.

“KĀ TANADAR MINI JIKI”

Wataƙila a lokacin da Yesu yake yin baftisma ne ya yi waɗannan kalaman. (Ibraniyawa 10:​5, Littafi Mai Tsarki; Matta 3:​13-17) Yaya jikin da aka tanadar masa yake? Shekaru 30 kafin Yesu ya yi baftisma, mala’ika Jibra’ilu ya gaya wa Maryamu cewa: “Za ki yi ciki, za ki haifi ɗa, . . . Ɗan Allah.” (Luka 1:​31, 35) Don haka, Yesu kamiltaccen mutum ne kamar yadda Adamu yake sa’ad da aka halicce shi. (Luka 3:38; 1 Korintiyawa 15:45) Yesu yana da siffa mai kyau kuma wataƙila yana da wasu halaye irin na Mahaifiyarsa Maryamu wadda Bayahudiya ce.

Yesu yana da gemu bisa ga al’adar Yahudawa, kuma gemunsa ba kamar na Romawa ba ne. A lokacin, ana daraja mutumin da ke da gemu. Amma ba gemun da ya yi tsayi ko kuma aka ƙi gyarawa ba. Hakika, Yesu yana gyara gemunsa kuma yana kula da sumarsa. Banaziri kamar Samson ne kaɗai ba sa aski.​—Littafin Lissafi 6:5; Alƙalawa 13:5.

A cikin shekaru 30 da muka ambata ɗazun, Yesu ya yi aikin kafinta. Ya yi aikin ba tare da yin amfani da kayayyakin aiki na zamani ba. (Markus 6:⁠3) Haka ya nuna cewa Yesu mutum ne mai ƙarfi sosai. Bayan Yesu ya soma hidimarsa, ‘ya kori duka masu canjin kuɗi daga haikalin, har da tumakin da shanun, ya kuma watsar da kuɗin ’yan canjin, ya birkice teburorinsu.’ (Yohanna 2:​14-17, LMT) Mutum mai ƙarfi ne kaɗai zai iya yin hakan. Yesu ya yi amfani da jikin da Allah ya tanadar masa don ya yi aikin da Allah ya ba shi. Yesu ya ce: ‘Dole in kai bishara ta Mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.’ (Luka 4:43) Yesu ya je dukan yankunan Falasɗinu da kafa don ya yi wa’azi. Hakan na bukatar ƙarfi sosai.

“KU ZO GARE NI, . . . NI KUWA IN BA KU HUTAWA”

Yesu mai fara’a ne sosai, shi ya sa ya kasance wa talakawa da “masu-nauyin kaya” sauƙi su amince da gayyatarsa. (Matta 11:​28-30) Yadda yake yin fara’a da kuma alheri ya nuna cewa zai iya biyan bukatun duk waɗanda suke so su koya daga gare shi. Har yara ƙanana ma suna marmarin zuwa wurinsa, domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya rungume su.”​—Markus 10:​13-16.

Ko da yake Yesu ya sha wahala kafin ya mutu, bai nuna cewa yana baƙin ciki a kullum ba. Alal misali, Yesu ya ba da gudummawarsa a wurin wani biki da aka yi a Kana sa’ad da ya mayar da ruwa zuwa ruwan inabi. (Yohanna 2:​1-11) A wasu taro kuma, Yesu ya koyar da darussa masu muhimmanci.​—Matta 9:​9-13; Yohanna 12:​1-8.

Fiye da haka ma, wa’azin da Yesu ya yi ya sa masu sauraronsa sun sami begen yin rayuwa har abada. (Yohanna 11:​25, 26; 17:3) A lokacin da almajiransa guda 70 suka kawo masa labarin wa’azin da suka yi, ya yi “murna” kuma ya ce: “Ku yi murna saboda an rubuta sunayenku cikin sama.”​—Luka 10:​20, 21.

“AMMA KU BA HAKA ZA KU YI BA”

A zamanin Yesu, shugabannin addinai suna yawan sa mutane su ɗaukaka su kuma ba sa bi da mutane yadda ya kamata. (Littafin Lissafi 15:​38-40; Matta 23:​5-7) Yesu bai yi hakan ba, shi ya sa ya umurci manzanninsa cewa kada su yi “sarauta” a kan mutane. (Luka 22:​25, 26) Yesu ya gargaɗe su cewa: “Ku yi hankali da marubuta, masu-son yawo da riguna masu-tsawo, a kuwa yi masu gaisuwa cikin kasuwai.”​—Markus 12:38.

Akasin haka, Yesu yana tarayya da mutane sosai, shi ya sa a wasu lokuta ba a iya gane shi sa’ad da yake cikin mutane. (Yohanna 7:​10, 11) Da kyar ake iya gane shi in yana tare da almajiransa 11 masu aminci. Hakan ne ya sa Yahuda ya yaudari Yesu da sumba a matsayin “alamar” da za ta sa mutane su gane Yesu.​—Markus 14:​44, 45.

Ko da yake ba mu da cikakken bayani game da kamanin Yesu, amma gaskiyar ita ce, Yesu ba ya kama da yadda mutane suke zana shi a yau. Abin da ya fi ainihin kamaninsa muhimmanci shi ne yadda muke ɗaukan sa yanzu.

“SAURA ƊAN LOKACI KAƊAN DUNIYA BA ZA TA ƘARA GANINA BA”

Yesu ya mutu jim kaɗan bayan ya faɗi waɗannan kalaman, kuma aka binne shi. (Yohanna 14:​19, LMT) Ya ba da ransa a matsayin “abin fansar mutane da yawa.” (Matta 20:28) Bayan kwana uku, Allah ya ta da shi “cikin ruhu” kuma ya “yarda ya bayyana” ga wasu mabiyansa. (1 Bitrus 3:18; Ayyukan Manzanni 10:​40, LMT) Yaya kamanin Yesu yake sa’ad da ya bayyana ga mabiyansa? Kamaninsa a lokacin ya bambanta da yadda yake kafin ya mutu domin mabiyansa ma ba su gane shi da sauri ba. Da Maryamu Magdaliya ta fara ganinsa, ta zata mai kula da kabarin ne. Wasu mabiyansa guda biyu da suke zuwa Immawus kuma sun ɗauka shi baƙo ne a garin.​—Luka 24:​13-18; Yohanna 20:​1, 14, 15.

Yaya ya kamata mu riƙa ɗaukan Yesu a yau? Bayan shekara 60 da Yesu ya mutu, manzo Yohanna ya ga wasu wahayoyi game da Yesu. Yohanna bai ga Yesu a kan giciye ba. Maimakon haka, ya ga “Sarkin Sarakuna, da Ubangijin Iyayengiji” da kuma Sarkin Mulkin Allah, wanda zai halaka dukan maƙiyan Allah. Bayan haka, zai albarkace dukan ’yan Adam masu aminci a duniya.​—Ru’ya ta Yohanna 19:16; 21:​3, 4.