Mene Ne Nufin Allah Ga Mutane?
Allah yana so mu zauna lafiya, cike da farin ciki a Aljanna a duniya, har abada!
Amma, kana iya cewa, ‘Hakan ba zai yiwu ba!’ Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa hakan zai yiwu a ƙarƙashin Mulkin Allah, kuma Allah yana so dukan mutane su koya game da wannan Mulkin da kuma nufin Allah a gare mu.—Zabura 37:11, 29; Ishaya 9:7.
Allah yana so mu amfana.
Kamar yadda mahaifin kirki yake yi wa ’ya’yansa fatan alheri, hakazalika, Ubanmu na sama yana so mu kasance masu farin ciki har abada. (Ishaya 48:17, 18) Ya yi alkawari cewa duk ‘wanda ya yi nufin Allah zai zauna har abada.’—1 Yohanna 2:17.
Allah yana so mu bi tafarkinsa.
In ji Littafi Mai Tsarki, Mahaliccinmu yana so ya “koya mana tafarkunsa” domin mu yi “tafiya cikin hanyoyinsa.” (Ishaya 2:2, 3) Allah ya tsara ‘wata jama’a domin sunansa,’ wadda za ta sanar da nufinsa a faɗin duniya.—Ayyukan Manzanni 15:14.
Allah yana so mu bauta masa cikin haɗin kai.
Maimakon ta jawo rashin jituwa a tsakanin mutane, bauta mai tsarki da muke yi wa Jehobah tana sa mutane su kasance da haɗin kai kuma su so juna. (Yohanna 13:35) Su wane ne a yau suke koya wa maza da mata a ko’ina yadda za su bauta wa Allah cikin haɗin kai? Muna ƙarfafa ka ka bincika amsar wannan tambayar a cikin ƙasidar nan.