Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?

Shaidun Jehobah suna ko’ina a dukan duniya kuma sun fito daga kabilu dabam dabam. Me ya sa suna da hadin kai haka?

Mene Ne Nufin Allah Ga Mutane?

Allah yana so a san nufinsa a duniya baƙi daya. Mene ne wannan nufin allah ga mutane, kuma su wane ne suke koyarwa wasu game da shi?

LESSON 1

Su Wane Ne Shaidun Jehobah?

Shaidun Jehobah guda nawa ne ka sani? Mene ne ainihi ka sani game da mu?

LESSON 2

Why Are We Called Jehovah’s Witnesses?

Consider three reasons why we adopted this name.

LESSON 3

Ta Yaya Aka Sake Gano Gaskiyar da ke Cikin Littafi Mai Tsarki?

Ta yaya za mu iya tabbata cewa mun fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa sosai?

LESSON 4

Me Ya Sa Muka Fitar da Juyin Littafi Mai Tsarki Mai Suna New World Translation

Mene ne wannan fassarar Kalmar Allah ta yi fice?

LESSON 5

Mene Ne Za Ka Gano a Taronmu na Kirista?

Muna haɗuwa wuri ɗaya tare don mu yi nazarin Nassosi kuma mu ƙarfafa juna. Za a marabce ka da hannu bibiyu!

LESSON 6

Yaya Yin Tarayya da ’Yan’uwanmu Kiristoci Zai Amfane Mu?

Kalmar Allah ta ƙarfafa yin tarayya ta Kirista. Ka koya yadda za ka amfana daga irin wannan tarayyar.

LESSON 7

Yaya Ake Gudanar da Taronmu?

Shin ka taɓa yin la’akari da abin da ake yi a taronmu kuwa? Babu shakka, irin koyarwar Littafi Mai Tsarki da za ka samu a wurin za ta burge ka.

LESSON 8

Me Ya Sa Muke Saka Tufafin da Ya Dace Zuwa Taronmu?

Shin Allah yana la’akari da irin tufafin da ado da muke yi? Ka koya ƙa’idodin Nassosi da muke bi wajen zaɓan tufafi da ado

LESSON 9

Ta Yaya Za Mu Yi Shiri Sosai Kafin Mu Halarci Taro?

Shirya taro tun da wuri zai sa ka amfana sosai daga taron.

LESSON 10

Mece Ce Bauta ta Iyali?

Ka koya yadda wannan tsarin zai taimake ka ka kusaci Allah kuma ka ƙarfafa dangantakar iyalinka.

LESSON 11

Me Ya Sa Muke Halartan Manyan Taro?

A kowace shekara, muna yin wasu taro na musamman guda uku. Ta yaya za ka amfana daga waɗannan taron?

LESSON 12

Yaya Ake Tsara Wa’azin da Muke Yi Game da Mulki?

Muna bin hanyoyin yin wa’azi da Yesu ya tsara sa’ad da yake duniya. Yaya waɗannan hanyoyin yin wa’azi suke?

LESSON 13

Wane Ne Majagaba?

Wasu Shaidun Jehobah suna yin amfani da sa’o’i 30 ko 50 ko sama da haka kowane wata a yin wa’azi. Mene ne yake motsa su?

LESSON 14

Wace Makaranta Ce Aka Shirya don Majagaba?

Wace irin ilimatarwa ta mussamman ce aka tanadar wa wadanda suke yin wa’azi na cikakken lokaci?

LESSON 15

Yaya Dattawa Suke Hidima a Ikilisiya?

Dattawa suna da dangantaka mai kyau da Allah kuma suna ja-gorar ikilisiya. Wane taimako ne suke tanadarwa?

LESSON 16

Mene Ne Aikin Bawa Mai Hidima

Bayi masu hidima suna taimakawa don abubuwa su gudana sumul-sumul a ikilisiya. Ka ga yadda ayyukansu suke amfanar waɗanda suka hallara.

LESSON 17

Yaya Masu Kula Masu Ziyara Suke Taimaka Mana?

Me ya sa masu kula masu ziyara suke ziyartar ikilisiyoyi? Ta yaya zaka amfana idan suka ziyarce ku?

LESSON 18

Yaya Muke Taimaka Wa ’Yan’uwanmu da Bala’i Ya Shafa?

Sa’ad da bala’i ya auko, muna yin shiri nan da nan don a tanadar musu da bukatunsu kuma a ta’azantar da Littafi Mai Tsarki. Ta yaya ake yin hakan?

LESSON 19

Wane Ne Bawan Nan Mai Aminci Mai Hikima?

Yesu yayi alkawari cewa zai naɗa wani bawan da zai yaɗa koyarwar Allah. Ta yaya ake yin hakan?

LESSON 20

Yaya Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah Take Gudanar da Ayyukanta a Yau?

A ƙarni na farko, ƙaramin rukunin manzanni da dattawa ne suke hidima a matsayin hukumar da ke kula da ikilisiyar Kirista. Su wane ne suke yin hakan a yau?

LESSON 21

Wane Irin Wuri Ne Bethel?

Bethel wuri ne na musamman da ke ma wani maƙasudi mai muhimmanci sosai. Ka koya gami da waɗanda suke hidima a wurin.

LESSON 22

Mene Ne Ake Yi a Ofishin Reshe?

A kowane ofishin reshenmu ana marabtar baƙi da ke so su yi yawon zagaya. Muna gayyatarka ka yi hakan!

LESSON 23

Yaya Ake Rubuta da Fassara Littattafanmu?

Muna buga littattafai a harsuna fiye da 600. Me ya sa muke sa ƙwazo haka?

LESSON 24

Yaya Muke Samun Kuɗin Gudanar da Ayyukanmu a Faɗin Duniya?

Me ya sa ƙungiyarmu ta bambanta da wasu addinai a batun samun kuɗin gudanar da ayyukanta?

LESSON 25

Me Ya Sa Ake Gina Majami’un Mulki Kuma Yaya Ake Yin Ginin?

Me ya sa ake kiran wuraren da muke ibada Majami’un Mulki? Ka bincika yadda wannan ginin ke taimakawa ikilisiyoyinmu.

LESSON 26

Yaya Za Mu Taimaka Wajen Kula da Majami’ar Mulki?

Majami’ar Mulki mai tsabta kuma ana kula da shi a kai a kai tana sa a yabi Allah. Waɗanne shirye-shirye ne aka shimfiɗa don tsabtace Majami’ar Mulki?

LESSON 27

Yaya Laburaren da ke Majami’ar Mulki Zai Amfane Mu?

Za ka so ka yi bincike don ka daɗa sanin Littafi Mai Tsarki? Ka ziyarci laburaren Majami’ar Mulki!

LESSON 28

Waɗanne Bayanai Ne Za Ka Iya Samu a Yanar Gizonmu?

Za ka iya koyo game da mu da imaninmu da kuma amsoshin tambayoyin da kake da shi a Littafi Mai Tsarki.

Za ka so ka yi nufin Jehobah?

Jehobah Allah yana ƙaunarka sosai. Ta yaya za ka faranta masa rai a rayuwarka ta yau da kullum?