Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA TARA

Shin Karshen Duniya Ya Kusa?

Shin Karshen Duniya Ya Kusa?

1. Wane littafi ne zai iya sa mu san abin da zai faru a nan gaba?

KA TAƁA kallon labarai a talabijin kuma ka ce, ‘Kai! Haka duniya ta lalace yanzu?’ Bala’i da kuma mugunta sun cika ko’ina kuma hakan ya sa mutane da yawa sun amince cewa ƙarshe ya kusa. Hakan gaskiya ne? Zai yiwu mu san abin da zai faru a nan gaba? Ƙwarai kuwa! Ko da yake mutane ba za su iya sanin abin da zai faru a nan gaba ba, amma Jehobah ya sani. Ya gaya mana a Littafi Mai Tsarki game da abin da zai faru da mu da kuma yadda duniya za ta kasance a nan gaba.—Ishaya 46:10; Yaƙub 4:14.

2, 3. Mene ne almajiran Yesu suka so su sani, kuma wace amsa ce Yesu ya ba su?

2 Idan Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da ƙarshen duniya, ba ya nufin ƙarshen doron ƙasa, amma ƙarshen mugunta. Yesu ya koya wa mutane cewa Mulkin Allah zai mallaki duniya. (Luka 4:43) Almajiran Yesu sun so ya gaya musu lokacin da Mulkin Allah zai zo, shi ya sa suka tambaye shi: ‘Ka faɗa mana, yaushe waɗannan abubuwa za su zama? mene ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?’ (Matta 24:3) Yesu bai faɗi ainihin ranar ba, amma ya gaya musu abubuwan da za su faru kafin ƙarshen wannan duniyar ya zo. Abubuwan da Yesu ya ambata suna faruwa a yau.

3 A wannan babin, za mu tattauna alamun da suke nuna cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe. Da farko, za mu tattauna game da yaƙin da aka yi a sama don hakan zai taimaka mana mu san dalilin da ya sa abubuwa suka yi muni sosai a duniya.

YAƘIN DA AKA YI A SAMA

4, 5. (a) Me ya faru a sama bayan da aka naɗa Yesu Sarki? (b) Me ya faru bayan an jefo Shaiɗan zuwa duniya kamar yadda Ru’ya ta Yohanna 12:12 ta nuna?

4 Mun koya a Babi na 8 cewa an naɗa Yesu Sarki a sama a shekara ta 1914. (Daniyel 7:13, 14) Littafin Ru’ya ta Yohanna ya gaya mana abin da ya faru cewa: “Yaƙi ya tashi a sama, Mika’ilu [wato, Yesu] da mala’ikunsa suna yaƙi da macijin nan [Shaiɗan]; macijin kuma da mala’ikunsa suka yi ta yaƙi.” * Shaiɗan da aljanunsa ba su yi nasara ba kuma hakan ya sa an jefo su zuwa duniya. Babu shakka, mala’iku masu aminci sun yi farin ciki sosai! Mutanen da ke duniya kuma fa? Littafi Mai Tsarki ya ce mutane za su sha wuya sosai. Me ya sa? Domin Iblis yana fushi sosai, “ya san lokacinsa ya ƙure.”—Ru’ya ta Yohanna 12:7, 9, 12, Littafi Mai Tsarki.

5 Iblis yana iya ƙoƙarinsa don ya jawo matsaloli a duniya. Yana fushi don lokacin da Allah zai halaka shi ya kusa. Bari mu tattauna abin da Yesu ya ce zai faru a kwanaki na ƙarshe.—Ka duba Ƙarin bayani na 24.

KWANAKI NA ƘARSHE

6, 7. Ta yaya yaƙi da kuma yunwa suke shafan mutane a yau?

6 Yaƙi. Yesu ya ce: “Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki kuma za ya tasa wa mulki.” (Matta 24:7) An fi kashe mutane yanzu a yaƙi fiye da dā. Wani rahoto ya nuna cewa daga shekara ta 1914, an kashe mutane fiye da miliyan 100 a yaƙi. A tsakanin shekara ta 1900 da 2000, wato a cikin shekara 100 da suka shige, mutanen da aka kashe sun fi waɗanda aka kashe a cikin shekara 1,900 da suka gabata sau uku. Babu shakka, miliyoyin mutane suna shan wahala da kuma azaba sanadiyyar yaƙi.

7 Yunwa. Yesu ya ce: “Za a yi yunwa.” (Matta 24:7) Ko da yake ana noman abinci yanzu fiye da dā, duk da haka, mutane da yawa ba su da isashen abinci. Me ya sa? Domin ba su da isashen kuɗin sayan abinci ko kuma ba su da gonakin da za su yi noma. Mutane fiye da biliyan ɗaya ba su da isashen kuɗin biyan bukatunsu. Ƙungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ce miliyoyin yara suna mutuwa kowace shekara don ba sa samun isashen abinci.

8, 9. Me ya nuna cewa annabcin Yesu game da girgizan ƙasa da kuma cuta suna cika?

8 Girgizar ƙasa. Yesu ya annabta cewa: ‘Za a yi manyan rayerayen duniya [girgizar ƙasa].’ (Luka 21:11) Ana fama da girgizan ƙasa a kowace shekara. Mutane fiye da miliyan biyu sun mutu sanadiyyar girgizan ƙasa tun shekara ta 1900. Ko da yake ilimin zamani yana sa a gane wuraren da wataƙila za a yi girgizar ƙasa, duk da haka, tana kashe mutane da yawa.

9 Cuta. Yesu ya annabta cewa za a yi “annoba,” wato cuta. Cututtuka masu tsanani za su riƙa yaɗuwa da sauri kuma su kashe mutane da yawa. (Luka 21:11, LMT) Ko da yake likitoci sun san maganin cututtuka da yawa, har ila, akwai cututtukan da suka fi ƙarfinsu. Wani rahoto ya nuna cewa miliyoyin mutane suna mutuwa kowace shekara sanadiyyar cututtuka kamar su tarin fuka da zazzaɓin cizon sauro da kuma amai-da-gudawa. Ban da haka ma, a cikin shekaru 40 da suka shige, likitoci sun gano wasu sababbin cututtuka fiye da 30 kuma wasu cikin su ba su da magani.

HALAYEN MUTANE A KWANAKI NA KARSHE

10. Ta yaya 2 Timotawus 3:1-5 yake cika a yau?

10 Littafin 2 Timotawus 3:1-5 ya ce: “Amma sai ka san wannan, cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu za su zo.” Manzo Bulus ya faɗi yadda halin mutane da yawa zai kasance a kwanaki na ƙarshe. Ya ce mutane za su zama

  • masu son kai

  • masu son kuɗi

  • marasa biyayya ga iyaye

  • marasa tsarki

  • waɗanda ba sa ƙaunar iyalinsu

  • marasa kamewa

  • masu faɗa da zafin hali

  • masu son jin daɗi fiye da ƙaunar Allah

  • masu yi kamar suna ƙaunar Allah amma ba sa masa biyayya

11. Me zai faru da miyagun mutane kamar yadda Zabura 92:7 ta nuna?

11 Shin mutanen da ke yankinku suna da irin waɗannan halayen kuwa? Babu shakka, mutane da yawa a duniya suna da waɗannan halayen. Amma nan ba da daɗewa ba, Allah zai ɗauki mataki. Ya ce: ‘Lokacin da masu-mugunta suna tsiro kamar ciyawa, sa’anda dukan masu-aikin mugunta suna ƙaruwa: domin su halaka ke nan har abada.’—Zabura 92:7.

YIN BISHARA A KWANAKI NA ƘARSHE

12, 13. Mene ne Jehobah ya koya mana a kwanaki na ƙarshe?

12 Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa wahala da kuma matsaloli da dama za su cika duniya a kwanaki na ƙarshe. Amma ya kuma ce abubuwa masu kyau ma za su faru a kwanaki na ƙarshe.

“Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya.”—Matta 24:14

13 Fahimtar Littafi Mai Tsarki. Annabi Daniyel ya ce game da kwanaki na ƙarshe: “Ilimi kuma za ya ƙaru.” (Daniyel 12:4) Allah zai taimaka wa mutanensa su fahimci Littafi Mai Tsarki fiye da dā. Jehobah ya yi hakan musamman daga shekara ta 1914. Alal misali, ya koya mana muhimmancin yin amfani da sunansa da kuma nufinsa ga duniya. Ƙari ga haka, ya koya mana gaskiya game da fansar Yesu da abin da yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu da kuma tashin matattu. Mun koya cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai kawo ƙarshen matsalolinmu. Ban da haka ma, mun koya yadda za mu yi farin ciki da kuma faranta wa Allah rai. Amma mene ne bayin Allah suke yi da abubuwan da suka koya? Wani annabcin Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar wannan tambayar.—Ka duba Ƙarin bayani na 21 da 25.

14. A ina ake wa’azin bisharar Mulkin, kuma su waye ne suke wa’azin?

14 Yin wa’azi a faɗin duniya. Yesu ya yi magana game da kwanaki na ƙarshe, ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya.” (Matta 24:3, 14) Ana wa’azin nan na Mulki a ƙasashe sama da 230 kuma a harsuna dabam-dabam fiye da 700. Hakika, Shaidun Jehobah daga “cikin kowane iri da dukan kabilai” a faɗin duniya suna taimaka wa mutane su san Mulkin Allah da kuma abin da zai yi ma ’yan Adam a nan gaba. (Ru’ya ta Yohanna 7:9) Kuma suna yin hakan ba tare da an biya su kuɗi ba. Ko da yake mutane da yawa suna tsananta musu, amma babu wani abin da ya isa ya hana su yin wa’azi kamar yadda Yesu ya annabta.—Luka 21:17.

ME YA KAMATA KA YI?

15. (a) Shin ka gaskata cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe, kuma me ya sa? (b) Mene ne Allah zai yi wa masu biyayya da marasa biyayya?

15 Shin ka gaskata cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe? Annabci da yawa na Littafi Mai Tsarki game da kwanaki na ƙarshe suna cika. Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai dakatar da yin wa’azin bishara, sa’an nan “matuƙa” za ta zo. (Matta 24:14) Mece ce matuƙar? Lokaci ne da Allah zai yi amfani da yaƙin Armageddon wajen kawo ƙarshen mugunta. Jehobah zai yi amfani da Yesu da kuma mala’ikunsa masu iko don halaka duk wanda ya ƙi yin biyayya ga Jehobah da kuma Ɗansa. (2 Tasalonikawa 1:6-9) Bayan haka, Shaiɗan da aljanunsa ba za su yaudari mutane ba. Dukan waɗanda suke biyayya ga Allah kuma suka amince da Mulkinsa za su ga cikar alkawarin da Allah ya yi musu.—Ru’ya ta Yohanna 20:1-3; 21:3-5.

16. Me kake bukata ka yi da yake “matuƙa” ta kusa?

16 Nan ba da daɗewa ba, za a kawo ƙarshen wannan duniyar da Shaiɗan yake sarauta. Saboda haka, yana da muhimmanci mu yi wa kanmu wannan tambayar, ‘Mene ne nake bukatar yi?’ Jehobah yana so ka fahimci abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki sosai. Ya kamata ka ɗauki nazarinka da muhimmanci. (Yohanna 17:3) Shaidun Jehobah suna nazarin Littafi Mai Tsarki a kowane mako. Ka riƙa halartan taronsu a kai a kai. (Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.) Idan akwai wasu gyare-gyaren ya kamata ka yi, kada ka yi jinkirin yin hakan. Dangantakarka da Jehobah za ta yi danƙo yayin da kake yin waɗannan gyare-gyaren.—Yaƙub 4:8.

17. Me ya sa mutane da yawa za su sha mamaki sa’ad da ƙarshen ya zo?

17 Manzo Bulus ya ce ƙarshen zai zo a lokacin da mutane ba su yi tsammani ba, kamar “ɓarawo da dare.” (1 Tasalonikawa 5:2) Yesu ya annabta cewa mutane da yawa za su yi banza da alamun da suke nuna cewa muna kwanaki na ƙarshe. Ya ce: “Kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka nan kuma bayanuwar Ɗan Mutum za ta zama. Gama kamar yadda suna ci, suna sha, suna aure, suna auraswa a cikin kwanakin da ke gaban ruwan Rigyawa, har ran da Nuhu ya shiga cikin jirgi, ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka; hakanan kuma bayanuwar Ɗan mutum za ta zama.”—Matta 24:37-39.

18. Wane gargaɗi ne Yesu ya yi mana?

18 Yesu ya gargaɗe mu cewa kada mu bar “zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai” su raba hankalinmu. Ya ce ƙarshen zai zo “kamar tarko.” Ya ƙara da cewa ranar za ta zo kan “dukan mazaunan fuskar duniya.” Bayan haka, sai ya ce: “Amma a kowane loto sai ku yi tsaro, kuna yin roƙo [ko addu’a sosai don] ku sami ikon da za ku tsere wa dukan waɗannan al’amuran da za su faru, ku tsaya kuma a gaban Ɗan mutum.” (Luka 21:34-36) Me ya sa yake da muhimmanci mu mai da hankali ga wannan gargaɗin? Domin nan ba da daɗewa ba, za a halaka mugayen mutanen da ke wannan duniyar. Waɗanda Jehobah da Yesu suka amince da su ne kaɗai za su tsira wa ƙarshen wannan zamanin kuma su yi rayuwa a sabuwar duniya har abada.—Yohanna 3:16; 2 Bitrus 3:13.

^ sakin layi na 4 Mika’ilu wani suna ne na Yesu Kristi. Ka duba Ƙarin bayani na 23.