Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 3

Jehobah Ya Bayyana Nufinsa

Jehobah Ya Bayyana Nufinsa

MANUFAR WANNAN BABIN

Jehobah yana bayyana nufinsa da sannu-sannu, amma ga waɗanda suke masa biyayya ne kaɗai

1, 2. Ta yaya Jehobah ya bayyana nufinsa ga ’yan Adam?

 IYAYE masu ƙaunar ’ya’yansu suna neman ra’ayin ’ya’yan sa’ad da suke so su tsai da shawarar da za ta shafi iyalin. Amma ba dukan abu ba ne suke tattaunawa da su. Bisa ga shekarun yaransu, iyayen sukan faɗa musu abubuwan da suke ganin za su iya fahimta ne kawai.

2 Hakazalika, Jehobah ya bayyana nufinsa ga ’yan Adam da sannu-sannu. Amma ya yi hakan a lokacin da ya ga cewa ya dace. Ka yi la’akari da yadda Jehobah ya bayyana gaskiya game da Mulkin cikin shekaru da yawa da suka shige.

Me Ya Sa Ake Bukatar Mulkin?

3, 4. Shin Jehobah ya ƙaddara abin da zai faru da ’yan Adam ne? Ka bayyana.

3 Da farko, ba nufin Jehobah ne ya kafa Mulkin da Yesu zai yi sarauta ba. Me ya sa? Domin Jehobah bai ƙaddara abubuwan da za su faru ga ’yan Adam ba. Ya halicci ’yan Adam da ’yancin yin zaɓi kuma ya gaya wa Adamu da Hawwa’u nufinsa ga mutane, sa’ad da ya ce: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta.” (Far. 1:28) Ƙari ga haka, Jehobah ya bukace su su bi dokokin da ya kafa game da nagarta da mugunta. (Far. 2:16, 17) Amma sun ƙi kasancewa da aminci ga Jehobah. Da a ce su da ’ya’yansu sun kasance da aminci, da ba a bukaci Mulkin da Kristi zai yi sarauta don ya cika nufin Allah ba. Da a yanzu hakan, duniya tana cike da kamiltattun mutane da suke bauta wa Jehobah.

4 Tawayen da Shaiɗan da Adamu da kuma Hawwa’u suka yi bai sa Jehobah ya watsar da nufinsa na sa kamiltattun mutane su mamaye duniya ba. Maimakon haka, Jehobah ya kirkiro wata hanya don ya cika nufinsa. Nufin Jehobah ba ya kama da jirgin ƙasa da yake bukatar yin tafiya a kan hanya ɗaya kawai kafin ya kai inda za shi. Mutane za su iya sa jirgi ya goce hanyarsa amma ba hakan yake da nufin Jehobah ba. Da zarar Jehobah ya faɗi nufinsa, babu abin da zai iya hana shi cika shi. (Karanta Ishaya 55:11.) Idan Jehobah ya ga cewa wani abu yana so ya hana shi cika nufinsa, zai yi amfani da wata hanya dabam. a (Fit. 3:14, 15) Idan ya ga ya dace, yana gaya wa amintattun bayinsa sabuwar hanyar da zai yi amfani da ita don cika nufinsa.

5. Wane mataki ne Jehobah ya ɗauka bayan tawayen da aka yi a gonar Adnin?

5 Bayan Adamu da Hawwa’u sun yi tawaye a gonar Adnin, Jehobah ƙudura niyyar kafa Mulki. (Mat. 25:34) A wannan lokacin da kamar dai ’yan Adam ba su da mafita, Jehobah ya bayyana abin da zai yi amfani da shi don ya cece su kuma ya magance dukan matsalolin da Shaiɗan ya jawo saboda son iko. (Far. 3:14-19) Duk da haka, Jehobah bai bayyana kome game da Mulkin farat ɗaya ba.

Jehobah Ya Soma Bayyana Gaskiya Game da Mulkin

6. Wane alkawari ne Jehobah ya yi, amma mene ne bai bayyana ba?

6 A annabci na farko da ke cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya yi alkawari cewa wata ‘zuriya’ za ta halaka macijin. (Karanta Farawa 3:15.) Amma, ba a bayyana ko waye ne zuriyar macen da kuma na macijin a lokacin ba. Hakika, an yi wajen shekara dubu biyu kuma Jehobah bai ba da ƙarin haske a kan batun ba. b

7. Me ya sa Allah ya zaɓi Ibrahim, kuma wane darasi mai muhimmanci ne hakan ya koya mana?

7 Daga baya, Jehobah ya ce zuriyar za ta fito ta wajen Ibrahim. An zaɓi Ibrahim domin ya ‘yi biyayya da maganar [Jehobah].’ (Far. 22:18) Wane darasi mai muhimmanci ne za mu koya daga hakan? Jehobah yana bayyana nufinsa ga waɗanda suke tsoronsa da gaske.—Karanta Zabura 25:14.

8, 9. Waɗanne bayanai ne Jehobah ya yi wa Ibrahim da Yaƙubu game da zuriyar da aka yi alkawarinta?

8 Sa’ad da Jehobah yake tattaunawa da abokinsa Ibrahim ta hanyar mala’ika, a lokaci na farko, Ya bayyana wani abu mai muhimminci game da zuriyar. Ya ce zuriyan zai zama mutum. (Far. 22:15-17; Yaƙ. 2:23) Amma ta yaya wannan mutumin zai halaka macijin? Wane ne macijin? An ba da ƙarin haske game da waɗannan tambayoyin daga baya.

9 Jehobah ya ce zuriyar da aka yi alkawarinta za ta fito daga wani jikan Ibrahim mai suna Yakubu wanda ya kasance da bangaskiya sosai ga Allah. (Far. 28:13-22) Ta bakin Yakubu, Jehobah ya annabta cewa zuriyar za ta fito daga ɗan Yakubu, wato Yahuda. Yakubu ya annabta cewa ɗan Yahuda zai karɓi ‘sandar mulki,’ wadda take wakiltar ikon mai sarauta kuma “biyayyar al’ummai za ta nufa” wajensa. (Far. 49:1, 10) Ta hanyar wannan annabcin, Jehobah ya bayyana cewa Zuriyar zai zama sarki.

10, 11. Me ya sa Jehobah ya bayyana nufinsa ga Dauda da kuma Daniyel?

10 Shekaru 650 bayan zamanin Yahuda, Jehobah ya ba da ƙarin haske a kan nufinsa ga Sarki Dauda, wanda zuriyar Yahuda ne. Jehobah ya ce, Dauda mutumi ne “wanda yake so.” (1 Sam. 13:14; 17:12, Littafi Mai Tsarki; A. M. 13:22) Jehobah ya yi wa Dauda alkawari cewa wani zuriyarsa zai yi sarauta har abada. Me ya sa ya yi masa wannan alkawarin? Domin Dauda yana tsoron Allah da dukan zuciyarsa.—2 Sam. 7:8, 12-16.

11 Bayan wajen shekara 500, Jehobah ya sa annabi Daniyel ya faɗi shekarar da Shafaffen ko Almasihu zai bayyana a duniya. (Dan. 9:25) Daniyel “ƙaunatacce ne ƙwarai” ga Jehobah. Me ya sa? Domin Daniyel yana daraja Jehobah sosai kuma yana bauta masa babu fashi.—Dan. 6:16; 9:22, 23.

12. Me aka gaya wa Daniyel ya yi, kuma me ya sa?

12 Ko da yake Jehobah ya yi amfani da annabawa masu aminci kamar Daniyel wajen rubuta bayanai masu yawa game da zuriyar, wato Almasihu, amma lokaci bai yi ba tukun da zai sa bayinsa su fahimci ma’anar abin da ya hure su su rubuta. Alal misali, bayan Jehobah ya saukar wa Daniyel da wahayi game da kafawar Mulkin, ya ce masa ya hatimce annabcin har sai lokacin da ya ƙayyade ya yi. Idan lokacin ya yi, ilimi na gaske “za ya ƙaru.”—Dan. 12:4.

Jehobah ya yi amfani da amintattun mutane kamar Daniyel don ya rubuta bayanai game da Mulkin Almasihu

Yesu Ya Yi Ƙarin Haske a Kan Nufin Allah

13. (a) Wane ne zuriyan da aka yi alkawari? (b) Ta yaya Yesu ya yi ƙarin haske a kan annabcin da ke Farawa 3:15?

13 Jehobah ya bayyana sarai cewa Yesu ne zuriyan da aka yi alkawari, wato zuriyan Dauda da zai zama sarki. (Luk 1:30-33; 3:21, 22) Sa’ad da Yesu ya soma hidimarsa, ya ba da ƙarin haske sosai a kan nufin Allah. (Mat. 4:13-17) Alal misali, Yesu ya kawar da duk wata shakka game da ko waye ne ‘macijin’ da aka ambata a littafin Farawa 3:14, 15. Ya kira Iblis “mai-kisan kai” da kuma “uban ƙarya.” (Yoh. 8:44) A wahayin da Yesu ya saukar wa Yohanna, ya ce “babban maciji, wato tsohon macijin nan” shi ne “Iblis da Shaitan.” c (Karanta Ru’ya ta Yohanna 1:1; 12:9.) A wannan wahayin, Yesu ya nuna yadda shi, wato zuriyar da aka yi alkawarinta, zai cika annabcin da aka yi a gonar Adnin kuma zai ƙuje Shaiɗan har ya mutu.—R. Yoh. 20:7-10.

14-16. Shin almajiran Yesu a ƙarni na farko sun fahimci dukan koyarwarsa ne? Ka yi bayani.

14 Kamar yadda muka tattauna a Babi na 1na wannan littafin, Yesu ya yi magana sosai game da Mulkin. Amma ba ya yawan gaya wa almajiransa dukan abin da suke so su sani. Ko ma a lokacin da ya yi wasu bayanai, almajiran ba su fahimta ba sosai sai bayan ƙarnuka da yawa. Ka yi la’akari da wasu misalai.

15 A shekara ta 33 a zamaninmu, Yesu ya nuna sarai cewa za a zaɓi waɗanda za su taya shi sarauta a matsayinsa na Sarkin Mulkin Allah daga duniya kuma za su zama ruhohi a sama. Amma, almajiransa ba su fahimci abin da yake nufi a lokacin ba. (Dan. 7:18; Yoh. 14:2-5) A wannan shekarar, Yesu ya yi amfani da kwatanci don ya bayyana cewa ba za a kafa Mulkin a lokacin ba sai bayan ya koma sama. (Mat. 25:14, 19; Luk 19:11, 12) Almajiran ba su fahimci wannan muhimmin bayani ba kuma bayan an ta da Yesu daga mutuwa, sai suka sake tambayarsa cewa: “A wannan lokaci ne kake mayar wa Isra’ila da mulki?” (A. M. 1:6, 7) Yesu ya kuma koyar da cewa akwai “waɗansu tumaki,” waɗanda ba za su kasance cikin “ƙaramin garke” da za su yi sarauta tare da shi ba. (Yoh. 10:16; Luk 12:32) Mabiyan Kristi ba su fahimci rukuni biyu da Yesu ya ambata sosai ba sai bayan da aka kafa Mulkin a shekara ta 1914.

16 Da Yesu ya gaya wa almajiransa abubuwa masu yawa sa’ad da yake duniya, amma ya san cewa ba za su iya fahimta ba. (Yoh. 16:12) Babu shakka, an bayyana abubuwa da yawa game da Mulkin a ƙarni na farko. Amma lokaci bai yi ba tukuna da ilimi na gaskiya zai ƙaru.

Ilimi na Gaskiya Yana Ƙaruwa a “Kwanakin Ƙarshe”

17. Mene ne ya kamata mu yi idan muna so mu san gaskiya game da Mulkin, amma mene ne kuma muke bukata?

17 Jehobah ya yi wa Daniyel alkawari cewa a “kwanakin ƙarshe; mutane da yawa za su kai da kawo” kuma ilimi na gaskiya game da nufin Allah zai ƙaru. (Dan. 12:4) Dole ne mutanen da suke son wannan ilimin su yi aiki tuƙuru don su same shi. Wani littafin bincike ya nuna cewa furucin nan “kai da kawo” yana da alaƙa da yin binciken littafi a hankali kuma cikin natsuwa. Duk da haka, kome ƙoƙarin da muka yi na bincika Littafi Mai Tsarki, ba za mu iya fahimtar gaskiya game da Mulkin ba sai da taimakon Jehobah.—Karanta Matta 13:11.

18. Ta yaya waɗanda suke tsoron Jehobah suke nuna bangaskiya da tawali’u?

18 Kamar yadda Jehobah ya bayyana gaskiya game da Mulkin kafin shekara ta 1914, ya ci gaba da yin hakan a waɗannan kwanaki na ƙarshe. A Babi na 4da 5na wannan littafin, za mu tattauna gyaran da bayin Jehobah suka yi a yadda suka fahimci nassosi a cikin shekara 100 da suka shige. Shin hakan yana nufin cewa Jehobah ba ya goyon bayansu ne? Hakika, yana goyon bayansu! Me ya sa? Domin mutanen da ke tsoron Jehobah sun nuna halaye biyu da yake so. Waɗanne halaye ke nan? Bangaskiya da tawali’u. (Ibran. 11:6; Yaƙ. 4:6) Bayin Jehobah suna da bangaskiya cewa dukan alkawuran da ke cikin Kalmar Allah za su cika. Suna nuna tawali’u sa’ad da suka amince cewa ba su fahimci ainihin yadda waɗannan alkawura za su cika ba. Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 1925, ta nuna yadda suka kasance da tawali’u. Ta ce: “Mun san cewa Ubangiji ne yake bayyana Kalmarsa da kansa kuma zai yi hakan a hanyar da ta dace kuma a lokacin da yake so.”

“Mun san cewa Ubangiji ne yake bayyana Kalmarsa da kansa kuma zai yi hakan a hanyar da ta dace kuma a lokacin da yake so”

19. Mene ne Jehobah ya sa muka fahimta yanzu, kuma me ya sa?

19 Sa’ad da aka kafa Mulkin a shekara ta 1914, bayin Jehobah ba su da cikakken sani a kan yadda annabci game da Mulkin za su cika. (1 Kor. 13:9, 10, 12) A marmarin da muke yi na ganin yadda Allah zai cika alkawuransa, a wasu lokatai mun yi kurakurai a bayanan da muka yi. A cikin shekarun nan, bayanan da aka yi a cikin Hasumiyar Tsaro da aka yi ƙaulinsa a sakin layi na 18 sun kasance gaskiya. Talifin ya ce: “Kamar dai wannan ce ƙa’ida mafi kyau da za mu bi. Ba za mu iya fahimtar annabcin ba sai ya cika ko yana kan cika.” Yanzu da ƙarshe ya yi kusa sosai, wasu annabci game da Mulkin sun cika, wasu kuma suna kan cika. Jehobah ya sa bayinsa su daɗa fahimtar nufinsa domin suna da tawali’u kuma ba sa ƙin gyaran da aka yi musu. Ilimi na gaskiya ya ƙaru ƙwarai!

Gyara a Fahimta Sun Gwada Bayin Allah

20, 21. Ta yaya gyaran da aka yi a yadda muka fahimci gaskiya ya shafi Kiristoci na ƙarni na farko?

20 Sa’ad da Jehobah ya yi wasu gyara a yadda muka fahimci gaskiya, hakan yakan bayyana abin da ke zuciyarmu. Shin bangaskiya da tawali’u za su motsa mu mu amince da wasu canji da aka yi? Kiristoci da suka kasance a tsakiyar ƙarni na farko sun fuskanci irin wannan gwajin. Alal misali, a ce kai Kirista ne Bayahude a lokacin, kana daraja Dokar da aka ba da ta hannun Musa kuma kana alfahari da cewa kai Ba’isra’ile ne. Amma sai kurum manzo Bulus ya aika wasiƙa cewa Jehobah ya ce a daina bin Dokar kuma ya ƙi al’ummar Isra’ila. Wasiƙar ta kuma ce Jehobah zai tattara Isra’ila na Allah waɗanda suka ƙunshi Yahudawa da ’Yan Al’ummai. (Rom. 10:12; 11:17-24; Gal. 6:15, 16; Kol. 2:13, 14) Mene ne za ka yi?

21 Kiristoci masu tawali’u sun amince da bayanan da aka hure Bulus ya yi kuma Jehobah ya albarkace su. (A. M. 13:48) Wasu sun yi banza da wannan gyaran kuma sun bi na su ra’ayi. (Gal. 5:7-12) Idan waɗannan mutanen ba su canja ra’ayinsu ba, za su rasa gatan zama abokan sarautar Kristi.—2 Bit. 2:1.

22. Mene ne ra’ayinka game da ƙarin hasken da muka samu game da yadda muke fahimtar nufin Allah?

22 A shekarun baya bayan nan, Jehobah ya yi wasu gyara ga fahimtarmu ta koyarwa game da Mulkin. Alal misali, ya taimaka mana mu daɗa fahimtar lokacin da za a ware magoya bayan Mulkin daga waɗanda ba sa son Mulkin kamar yadda ake ware tumaki daga awaki. Ƙari ga haka, ya koya mana lokacin da adadin mutane 144,000 zai cika da ma’anar kwatanci game da Mulkin da Yesu ya yi da kuma lokacin da shafaffe na ƙarshe zai je sama. d Mene ne ra’ayinka game da waɗannan gyaran? Shin hakan ya ƙarfafa bangaskiyarka kuwa? Shin kana ɗaukan hakan a matsayin tabbaci cewa Jehobah yana ci gaba da ilimantar da bayinsa masu tawali’u? Bayanan da za a yi a cikin wannan littafin za su daɗa ƙarfafa imanin da ka yi cewa Jehobah yana bayyana nufinsa da sannu-sannu ga mutanen da suke tsoronsa.

a Sunan Allah fi’ilin Ibrananci ne, kuma yana nufin yana “zama.” Sunan Jehobah yana nufin cewa shi Mai cika alkawuransa ne. Ka duba akwatin nan “Ma’anar Sunan Allah,” a shafi na 43.

b Za mu iya ganin kamar wannan lokacin yana da tsawo sosai, amma ya kamata mu tuna cewa mutane suna daɗewa sosai a zamanin dā. Zamanin mutane huɗu zai ba mu wannan adadin. Lokacin da aka haifi mahaifin Nuhu, wato Lamech, Adamu bai mutu ba. An haifi ɗan Nuhu, wato Shem sa’ad da Lamech yake raye kuma an haifi Ibrahim sa’ad da Shem yake da rai.—Far. 5:5, 31; 9:29; 11:10, 11; 25:7.

c Sunan nan “Shaiɗan,” ya bayyana sau 18 a Nassosin Ibrananci. Amma, “Shaiɗan” ya bayyana fiye da sau 30 a Nassosin Helenanci na Kirista. Nassosin Helenanci bai mai da hankali ga Shaiɗan ba, amma ga Almasihu. Sa’ad da Almasihu ya zo duniya, ya fallasa Shaiɗan sosai kuma an rubuta hakan a cikin Nassosin Helenanci na Kirista.

d Don ƙarin bayani a kan waɗannan gyaran da aka yi a fahimtarmu, ka duba waɗannan talifofin Hasumiyar Tsaro: 1 ga Nuwamba, 1995, shafuffuka na 13-18; 15 ga Janairu, 2008, shafuffuka na 20-24; 15 ga Yuli, 2008, shafuffuka na 17-21; 15 ga Yuli, 2013, shafuffuka na 9-14.