ƘARIN BAYANI NA 1
Gaskiyar da Muke Jin Dadin Koya wa Mutane
Yesu ya ce idan masu zuciyar kirki suka ji gaskiya, za su gane ta. (Yoh. 10:4, 27) Shi ya sa duk lokacin da za mu yi wa mutum waꞌazi, zai dace mu gaya masa wata gaskiya daga Littafi Mai Tsarki mai sauƙin fahimta. Za ka iya somawa da tambayar mutumin cewa: “Ka san cewa . . . ?” ko “Ka taɓa ji cewa . . . ?” Saꞌan nan ka yi amfani da aya ko ayoyin da ke ƙasa da suka dace da batun, ka yi masa bayani. Idan ka koya wa mutum abu ɗaya kawai daga Kalmar Allah kuma ya fahimta, kamar ka shuka iri ne a zuciyarsa, kuma Allah zai iya sa irin ya yi girma!—1 Kor. 3:6, 7.
RAYUWA A NAN GABA
-
1. Munanan abubuwa da suke faruwa, sun nuna cewa kome ya kusan gyaruwa.—Mat. 24:3, 7, 8; Luk. 21:10, 11; 2 Tim. 3:1-5.
-
2. Ba za a taɓa hallaka duniyar nan ba.—Zab. 104:5; M. Wa. 1:4.
-
3. Wata rana yanayi zai yi kyau a koꞌina kuma duniya za ta zama aljanna.—Isha. 35:1, 2; R. Yar. 11:18.
-
4. Kowa zai sami koshin lafiya.—Isha. 33:24; 35:5, 6.
-
5. Za ka iya yin rayuwa har abada a duniya.—Zab. 37:29; Mat. 5:5.
ZAMAN IYALI
-
6. Mai gida “ya ƙaunaci matarsa kamar kansa.”—Afis. 5:33; Kol. 3:19.
-
7. Mace ta girmama maigidanta sosai.—Afis. 5:33; Kol. 3:18.
-
8. Ya kamata mata da miji su zama masu riƙon amana.—Mal. 2:16; Mat. 19:4-6, 9; Ibran. 13:4.
-
9. Yaran da suke girmama iyayensu kuma suke yi musu biyayya, za su yi nasara a rayuwa.—K. Mag. 1:8, 9; Afis. 6:1-3.
ALLAH
-
10. Allah yana da suna guda ɗaya.—Zab. 83:18; Irm. 10:10.
-
11. Allah yana magana da mu.—2 Tim. 3:16, 17; 2 Bit. 1:20, 21.
-
12. Allah yana yin gaskiya kuma ba ya nuna bambanci.—M. Sha. 10:17; A. M. 10:34, 35.
-
13. Allah yana so ya taimake mu.—Ps. 46:1; 145:18, 19.
ADDUꞌA
-
14. Allah yana so mu dinga yin adduꞌa gare shi.—Zab. 62:8; 65:2; 1 Bit. 5:7.
-
15. Littafi Mai Tsarki ya koya mana yadda za mu yi adduꞌa. —Mat. 6:7-13; Luk. 11:1-4.
-
16. Mu dinga yin adduꞌa sau da yawa.—Mat. 7:7, 8; 1 Tas. 5:17.
YESU
-
17. Yesu ya iya koyarwa sosai kuma a koyaushe, shawararsa tana amfanar mutane. —Mat. 6:14, 15, 34; 7:12.
-
18. Tun dā, Yesu ya ce abubuwa da muke gani a yau za su faru.—Mat. 24:3, 7, 8, 14; Luk. 21:10, 11.
-
19. Yesu Ɗan Allah ne.—Mat. 16:16; Yoh. 3:16; 1 Yoh. 4:15.
-
20. Yesu ba shi ne Allah Maɗaukaki ba.—Yoh. 14:28; 1 Kor. 11:3.
MULKIN ALLAH
-
21. Mulkin Allah sarauta ce kamar gwamnati a sama.—Dan. 2:44; 7:13, 14; Mat. 6:9, 10; R. Yar. 11:15.
-
22. Mulkin Allah zai ɗauki matsayin gwamnatocin duniyar nan.—Zab. 2:7-9; Dan. 2:44.
-
23. Mulkin Allah ne kaɗai zai magance matsalolin kowa da kowa.—Zab. 37:10, 11; 46:9; Isha. 65:21-23.
WAHALA
-
24. Ba Allah ne yake jawo mana wahaloli ba.—M. Sha. 32:4; Yak. 1:13.
-
25. Shaiɗan ne yake iko da duniyar nan.—Luk. 4:5, 6; 1 Yoh. 5:19.
-
26. Allah ya damu da wahalar da kake sha.—Zab. 34:17-19; Isha. 41:10, 13.
-
27. Nan ba da daɗewa ba, Allah zai sa a daina shan wahala. —Isha. 65:17; R. Yar. 21:3, 4.
MUTUWA
-
28. Waɗanda suka mutu ba su san kome ba, kuma ba sa shan azaba.—M. Wa. 9:5; Yoh. 11:11-14.
-
29. Wanda ya mutu ba zai iya taimakon mu ko ya yi mana illa ba.—Zab. 146:4; M. Wa. 9:6, 10.
-
30. Za a ta da waɗanda suka mutu.—Ayu. 14:13-15; Yoh. 5:28, 29; A. M. 24:15.
-
31. Za a daina mutuwa. —R. Yar. 21:3, 4; Isha. 25:8.
ADDINI
-
32. Ba dukan addinai ne suke faranta wa Allah rai ba.—Irm. 7:11; Mat. 7:13, 14, 21-23.
-
33. Allah ba ya son munafunci.—Isha. 29:13; Mik. 3:11; Mar. 7:6-8.
-
34. Za a gane addini na gaskiya ne ta yadda mabiyansa suke ƙaunar juna.—Mik. 4:3; Yoh. 13:34, 35.