DARASI NA 6
Ka Bayyana Nassin da Ka Karanta
Yohanna 10:33-36
ABIN DA ZA KA YI: Kada ka karanta nassi kuma ka ci gaba da magana ba tare da ka bayyana nassin ba. Ka sa masu sauraronka su ga yadda nassin ya jitu da abin da kake gaya musu.
YADDA ZA KA YI HAKAN:
-
Ka ambata muhimman kalmomi. Bayan ka karanta nassi, ka ambata kalmomin da suka shafi abin da kuke tattaunawa. Kana iya yin hakan ta wajen maimaita kalmomin da ke cikin nassin ko kuma ka yi tambayar da za ta sa masu sauraronka su ga batun da kake so su fahimta.
-
Ka nanata batun da kake so a fahimta. Idan ka gabatar da wani nassi kuma ka faɗi dalilin da ya sa kake so ka karanta, ka bayyana musu yadda kalmomin da ke nassin suka goyi bayan dalilin.
-
Ka sa bayaninka ya zama da sauƙin fahimta. Kada ka riƙa yin bayani a kan abubuwan da ba su shafi batun da kake tattaunawa ba. Ka yi tunani a kan abin da masu sauraronka suka riga suka sani game da batun, domin hakan zai sa ka san abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ka bayyana musu.