BABI NA 10
“Ku Ɗauki Misali Daga Wurin Allah” Wajen Amfani da Iko
1. Ga wane tarko ne mutane ajizai suke faɗāwa ciki da sauƙi?
“BABU ikon da ba shi da tarko.” Waɗannan kalmomin zabiya ta ƙarni na 19 sun jawo hankali ga haɗari da ke ɓoye: yin ɓarna da iko. Abin baƙin ciki, mutum ajizi ba wuya ya faɗā cikin wannan tarkon. Hakika, a duk cikin tarihi, ɗan Adam “yana da iko a kan waɗansu.” (Mai-Wa’azi 8:9) Nuna iko ba tare da ƙauna ba ya kai ga wahalar da babu iyaka na ’yan Adam.
2, 3. (a) Mene ne abin ban mamaki game da nuna iko na Jehobah? (b) Mene ne ikonmu ya ƙunsa, kuma yaya ya kamata mu nuna dukan irin waɗannan ikon?
2 Amma ba abin mamaki ba ne cewa Jehobah Allah, wanda yake da iko marar iyaka, bai taɓa ɓarna ba da ikonsa? Kamar yadda muka lura a babobi da suka shige, yana amfani da ikonsa—ko na halitta ne, ko na halaka, ko na kāriya, ko na maidowa—cikin jituwa da nufe-nufensa na ƙauna. Sa’ad da muka yi tunani game da yadda yake nuna ikonsa, mun motsa mu kusace shi. Hakan kuma zai motsa mu mu “ɗauki misali daga wurin Allah” wajen amfani da iko. (Afisawa 5:1) Amma wane iko mu mutane raunanu muke da shi?
3 Ka tuna cewa an halicci mutum cikin “kamannin Allah” da kuma siffarsa. (Farawa 1:26, 27) Saboda haka, muna da iko—aƙalla ɗan kaɗan. Ikonmu zai haɗa da iyawarmu mu cim ma abubuwa, mu yi aiki; iko bisa wasu; iyawarmu mu rinjayi wasu, musamman ma waɗanda suke ƙaunarmu; ƙarfi na jiki; ko kuma arziki. Game da Jehobah, mai Zabura ya ce: “Kai ne maɓuɓɓuga mai ba da ruwan rai.” (Zabura 36:9) Saboda haka, ko kai tsaye ko a’a, Allah shi ne tushen kowane iko mai kyau da muke da shi. Saboda haka, muna so mu yi amfani da shi a hanya mai kyau da zai faranta masa rai. Ta yaya za mu yi wannan?
Ƙauna Ita ce Mabuɗi
4, 5. (a) Mene ne mabuɗin nuna iko yadda ya dace, kuma yaya misalin Allah kansa ya nuna haka? (b) Ta yaya ƙauna za ta taimake mu mu yi amfani da ikonmu yadda ya dace?
4 Mabuɗin nuna iko yadda ya dace ƙauna ce. Misalin Allah bai nuna haka ba ne? Ka tuna da tattauna halayen Allah huɗu na musamman—iko, shari’a, hikima, da kuma ƙauna—a cikin Babi na 1. A cikin halayen huɗu, wanne ne ya fi? Ƙauna. “Allah ƙauna ne,” in ji 1 Yohanna 4:8. Hakika, Jehobah kansa ƙauna ne; tana rinjayar dukan abin da yake yi. Saboda haka, dukan nuna ikonsa ƙauna ce take motsa shi kuma domin amfanin waɗanda suke ƙaunarsa ne.
5 Ƙauna za ta taimake mu mu yi amfani da ikonmu yadda ya dace. Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ƙauna tana da “kirki” kuma “ba ta ƙin kula da yadda waɗansu za su ji.” (1 Korintiyawa 13:4, 5) Saboda haka, ƙauna ba za ta ƙyale mu mu yi zafin hali ko mugunta ba ga waɗanda muke da ɗan iko a kansu. Maimakon haka, za mu bi da wasu da daraja kuma mu saka muradinsu da kuma yadda suke ji gaba da namu.—Filibiyawa 2:3, 4.
6, 7. (a) Mene ne tsoron Allah ya ƙunsa, kuma me ya sa wannan halin zai taimake mu mu guji yin ɓarna da iko? (b) Ka kwatanta dangantakar da take tsakanin tsoron mu ɓata wa Allah rai da kuma ƙaunar Allah.
6 Ƙauna tana da dangantaka da wani hali da zai taimake mu mu guji yin ɓarna da iko: tsoron Allah. Mene ne muhimmancin wannan halin? “Ta wurin tsoron Yahweh kuma, mutum yakan kauce wa mugunta,” in ji Karin Magana 16:6. Yin ɓarna da iko hakika yana cikin mugunta da ya kamata mu rabu da ita. Tsoron Allah zai hana mu zaluntar waɗanda muke da iko a kansu. Me ya sa? Abu ɗaya shi ne, mun san cewa Allah zai yi mana hisabi game da yadda muka bi da irin waɗannan. (Nehemiya 5:1-7, 15) Amma tsoron Allah ya ƙunshi fiye da haka. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya danganta tsoro da ƙaunar Allah. (Maimaitawar Shari’a 10:12, 13) Wannan daraja Allah ta haɗa da tsoro da ya dace na ƙin baƙanta wa Allah rai—ba domin muna tsoron sakamakon hakan ba amma domin muna ƙaunarsa da gaske.
7 Alal misali: Ka yi tunanin dangantaka mai kyau tsakanin yaro da ubansa. Yaron zai fahimci cewa ubansa yana ƙaunarsa. Amma yaron ya san abin da ubansa yake bukata a gare shi, kuma ya san cewa ubansa zai yi masa horo idan ya yi rashin hankali. Yaron ba zai razana ba idan ya ga ubansa. Maimakon haka, zai yi ƙaunar ubansa ƙwarai da gaske. Matashin yana farin ciki wajen yin abin da zai kawo yardan ubansa. Haka yake da tsoron Allah. Domin muna ƙaunar Jehobah, Ubanmu na sama, muna tsoron yin abin da zai sa shi baƙin ciki. (Farawa 6:6) Maimakon haka, muna so mu sa ya yi farin ciki. (Karin Magana 27:11) Abin da ya sa ke nan muke so mu nuna ikonmu yadda ya dace. Bari mu bincika yadda za mu yi hakan.
A Cikin Iyali
8. (a) Wane iko magidanta suke da shi bisa iyali, kuma ta yaya za su nuna ikon? (b) Ta yaya maigida zai nuna cewa yana girmama matarsa?
8 Da farko, ka yi la’akari da iyali. “Miji shi ne kan matarsa,” in ji Afisawa 5:23. Ta yaya maigida zai nuna ikon da Allah ya ba shi? Littafi Mai Tsarki ya gaya wa magidanta su zauna da matansu “tare da tunani,” kuma su “girmama su, da yake su ba su da ƙarfi.” (1 Bitrus 3:7) Kalmar suna ta Helenanci da aka fassara “girmamawa” tana nufin “tamani, . . . daraja.” Wasun wannan kalmar an fassara su “kyauta” da kuma “daraja.” (Ayyukan Manzanni 28:10; 1 Bitrus 2:7) Maigida da yake girmama matarsa ba zai taɓa bugunta ba; ko kuma ya ƙasƙantar da ita, ya sa ta ji ba ta da amfani. Maimakon haka, zai fahimci tana da tamani kuma ya bi da ita da daraja. Zai nuna cikin kalmomi da kuma ayyuka—a ɓoye da a fili—tana da tamani. (Karin Magana 31:28) Irin wannan maigida ba kawai matarsa za ta yi ƙaunarsa kuma ta yi masa ladabi ba, amma mafi muhimmanci, zai sami yardar Allah.
9. (a) Wane iko mata suke da shi a cikin iyali? (b) Mene ne zai taimaki mace ta yi amfani da iyawarta ta tallafa wa mijinta, kuma da wane sakamako?
9 Mata ma suna da ɗan iko a cikin iyali. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da mata masu ibada waɗanda ba tare da taka dokar shugabanci ba, suka rinjayi mazansu zuwa hanya mai kyau ko kuma suka taimake su suka guje wa yin kuskure. (Farawa 21:9-12; 27:46–28:2) Wataƙila mace ta fi mijinta fahimi, ko kuma tana da wasu halaye da ba shi da su. Duk da haka, ta “girmama mijinta” kuma ta “miƙa kanta” gare shi ‘yadda take yi wa Ubangiji.’ (Afisawa 5:22, 33) Tunanin tana so ta faranta wa Allah rai zai iya taimakon matar ta yi amfani da iyawarta ta tallafa wa mijinta, maimakon raina shi ko kuma ƙoƙarin ta shugabance shi. Irin wannan “mace mai hikima” tana ba da haɗin kai ga mijinta su gina iyalinsu. Ta haka za ta kasance da salama da Allah.—Karin Magana 14:1.
10. (a) Wane iko Allah ya ba wa iyaye? (b) Mene ne ma’anar kalmar nan “horo,” kuma yaya ya kamata a yi shi? (Dubi hasiya.)
10 Iyaye suna da ikon da Allah ya ba su. Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Ku ubanni, kada ku sa ’ya’yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da horo da gargaɗi ta hanyar Ubangiji.” (Afisawa 6:4) A cikin Littafi Mai Tsarki, “horo” yakan nufi “reno, koyarwa, umurni.” Yara suna bukatar horo; sun fi farin ciki in aka kafa musu ƙa’ida, da iyaka. Littafi Mai Tsarki ya nasabta horo, ko umurni, da ƙauna. (Karin Magana 13:24) Saboda haka, kada a yi ɓarna da “bulalar horo” —a motsin rai ko kuma a jiki. a (Karin Magana 22:15; 29:15) Horo mai tsanani ba tare da ƙauna ba ɓarna ne da iko na iyaye kuma zai raunana ruhun tuba na yaro. (Kolosiyawa 3:21) A wani ɓangare kuma, horo da ya dace idan aka yi shi yana nuna wa yara cewa iyayensu suna ƙaunarsu kuma sun damu da irin mutane da za su zama.
11. Ta yaya yara za su yi amfani da ikonsu yadda ya dace?
11 Yara kuma fa? Ta yaya za su yi amfani da ikonsu yadda ya dace? “Darajar matasa tana cikin ƙarfinsu,” in ji Karin Magana 20:29. Hakika babu wata hanya da ta fi cewa matasa su yi amfani da ƙarfinsu da kuzari fiye da bauta wa ‘Mahaliccinmu.’ (Mai-Wa’azi 12:1) Ya kamata matasa su tuna cewa abin da suke yi zai shafi iyayensu. (Karin Magana 23:24, 25) Idan yara suka yi wa iyayensu masu ibada biyayya suka bi hanya mai kyau, suna faranta wa iyayensu zuciya. (Afisawa 6:1) Irin wannan hali “yakan faranta wa Ubangiji rai.”—Kolosiyawa 3:20.
A Cikin Ikilisiya
12, 13. (a) Yaya dattawa ya kamata su ɗauki ikonsu a cikin ikilisiya? (b) Ka kwatanta dalilin da ya sa dattawa ya kamata su kula da tumakin da kyau.
12 Jehobah ya yi tanadin dattawa su yi ja-gora a cikin ikilisiyar Kirista. (Ibraniyawa 13:17) Waɗannan ƙwararrun mutane ya kamata su yi amfani da ikon da Allah ya ba su, su ba da taimako kuma su ba da gudummawa domin lafiyar garken. Shin matsayinsu na dattawa don su yi sarauta ne bisa ’yan’uwa masu bi? A’a! Dattawa suna bukatar su fahimci daidai matsayinsu cikin tawali’u a ikilisiya. (1 Bitrus 5:2, 3) Littafi Mai Tsarki ya gaya wa dattawa: “Ku kuma ci gaba da kiwon jama’ar masu bi waɗanda Allah ya samo wa kansa da jinin Ɗansa.” (Ayyukan Manzanni 20:28) Wannan babban dalilin ya sa ya kamata a bi da kowanne cikin garken da kyau.
13 Za mu iya kwatanta shi a wannan hanyar. Aboki na kud da kud ya ba ka amanar abin da yake ƙauna ƙwarai. Kuma ka sani cewa abokinka ya sayi abin da tsada. Ba za ka kula da abin sosai ba kuma ka mai da hankali a kansa? Hakazalika, Allah ya ba wa dattawa hakkin kula da abin da yake so ƙwarai: ikilisiya, wadda waɗanda suke cikinta an kwatanta su da tumaki. (Yohanna 21:16, 17) Jehobah yana ƙaunar tumakinsa ƙwarai—yana ƙaunarsu ƙwarai da gaske, saboda haka ya saye su da jini mai tamani na Ɗansa makaɗaici, Yesu Kristi. Jehobah ya saye su da tsada ƙwarai. Dattawa masu tawali’u suna tuna da wannan kuma su kula da tumakin Jehobah da kyau.
“Harshen Mutum Yana da Ikon”
14. Wane iko harshe yake da shi?
14 “Harshen mutum yana da ikon rai da mutuwa,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Karin Magana 18:21) Hakika, harshe zai iya yin ɓarna ƙwarai. Waye a cikinmu bai taɓa yin baƙin ciki ba domin baƙar magana? Amma harshe kuma yana da ikon yin gyara. “Harshe mai hikima yakan kawo warkewa,” in ji Karin Magana 12:18. Hakika, kalmomi masu ƙarfafawa za su iya zama kamar man zuciya. Bari mu bincika wasu misalai.
15, 16. A waɗanne hanyoyi ne za mu yi amfani da harshenmu wajen ƙarfafa wasu?
15 “Ku ƙarfafa waɗanda ba su da ƙarfin zuciya,” yadda 1 Tasalonikawa 5:14 ta aririta. Hakika, har amintattun bayin Jehobah wani lokaci za su yi ta jimrewa da raunanniyar zuciya. Ta yaya za mu taimaki irin waɗannan mutane? Ka yi yabo takamamme na ƙwarai ka taimaka musu su ga suna da amfani a idanun Jehobah. Ka nuna musu ayoyin Littafi Mai Tsarki masu ƙarfi da suka nuna cewa Jehobah da gaske yana ƙaunarsu kuma yana kula da “waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa” da kuma waɗanda suka “fid da zuciya.” (Zabura 34:18) Idan muka yi amfani da ikon harshenmu muka ƙarfafa wasu, muna nuna cewa muna koyi da Allahnmu mai tausayi, wanda “yake ƙarfafa wanda ya fid da zuciya.”—2 Korintiyawa 7:6.
16 Mu ma za mu iya yin amfani da ikon harshenmu mu ba da ƙarfafa da wasu suke bukata. Wani ɗan’uwa mai bi ya yi rashin wani wanda yake ƙauna ne? Kalmominmu na ta’aziyya da suke nuna damuwarmu da kuma ƙauna za su iya ƙarfafa zuciya da take makoki. Wani ɗan’uwa ko wata ’yar’uwa yana ko tana jin ba a bukatarta? Mai maganar kirki zai iya tabbatar wa tsofaffi suna da tamani kuma ana ƙaunarsu. Akwai wanda yake fama da ciwo mai tsanani? Maganar alheri a tarho ko a wasiƙa ko kuma fuska-da-fuska za ta taimaka wa wanda yake ciwon. Mahaliccinmu zai yi murna idan muka yi amfani da ikon magana wajen furta magana da suke da “amfani domin ƙarfafawar juna”!—Afisawa 4:29.
17. A wace muhimmiyar hanya ce za mu iya amfani da harshenmu mu amfani wasu, kuma me ya sa za mu yi haka?
17 Babu wata hanya da ta fi muhimmanci wajen amfani da ikon harshe fiye da gaya wa wasu bisharar Mulkin Allah. “Kada ka janye alheri daga waɗanda sun cancanta a yi musu, sa’ad da ikon yin haka yana hannunka,” in ji Karin Magana 3:27. Wajibinmu ne mu gaya wa wasu bishara mai ceton rai. Ba zai dace ba mu rufe bakinmu ga saƙo na gaggawa da Jehobah ya ba mu hannu sake. (1 Korintiyawa 9:16, 22) Amma har yaya Jehobah yake so mu yi wannan aikin?
Ba da bishara—muhimmiyar hanya ce ta yin amfani da ikonmu
Bauta wa Jehobah da “Dukan Ƙarfinmu”
18. Mene ne Jehobah yake zato wajenmu?
18 Ƙauna da muke yi wa Jehobah tana motsa mu mu shagala cikin hidimar Kirista. Mene ne Jehobah yake bukata wajenmu game da wannan? Abin da dukanmu, ko yaya yanayinmu a rayuwa za mu iya bayarwa: “Duk abin da kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku kamar ga Ubangiji ne kuke yi wa, ba ga mutum ba.” (Kolosiyawa 3:23) Wajen faɗar doka mafi girma, Yesu ya ce: “Sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.” (Markus 12:30) Hakika, Jehobah yana bukatar kowannenmu ya yi ƙaunarsa kuma ya bauta masa da dukan ransa.
19, 20. (a) Tun da rai ya ƙunshi zuciya, da azanci, da kuma ƙarfi, me ya sa aka ambaci waɗannan a Markus 12:30? (b) Me yake nufi a bauta wa Jehobah da dukan rai?
19 Mene ne yake nufi a bauta wa Allah da dukan rai? Ran yana nufin mutumin ne ɗungum, da dukan iyawarsa na zahiri da basira. Tun da ran ya ƙunshi zuciya, azanci, da kuma ƙarfi, me ya sa aka lissafa su a Markus 12:30? Ka ga wannan misalin. A zamanin Littafi Mai Tsarki, mutum zai iya sayar da kansa (ransa) ga bauta. Amma, bawan ba zai bauta wa ubangidansa da dukan zuciyarsa ba; ba zai yi amfani da dukan ƙarfinsa ba ko kuma basirarsa don ya bunƙasa amfanin ubangidansa. (Kolosiyawa 3:22) Saboda haka, babu shakka Yesu ya lissafa waɗannan domin ya nanata cewa kada mu janye kome daga bauta wa Allah. Bauta wa Allah da dukan ranmu yana nufin ba da kanmu, yin amfani da ƙarfinmu cikakke a bautarsa.
20 Shin bauta da dukan ranmu yana nufi ne cewa dole mu ba da yawan lokaci ɗaya daidai da kowa da kuma ƙarfi a hidimarmu? Hakan da ƙyar zai yiwu, domin yanayi da kuma iyawa sun bambanta daga mutum zuwa mutum. Alal misali, saurayi mai ƙoshin lafiya da kuma ƙarfi zai iya ba da lokaci da yawa wajen wa’azi fiye da wanda tsufa ta ci ƙarfinsa. Wani da ba shi da hakkin iyali zai iya yin fiye da wanda yake da iyalin da zai kula da ita. Idan muna da ƙarfi kuma yanayi ya ƙyale mu mu yi aiki da yawa a hidima, ya kamata mu yi godiya! Hakika, ba ma son mu kasance da halin sūka, mu riƙa gwada kanmu da wasu a wannan. (Romawa 14:10-12) Maimakon haka, mu yi amfani da ikonmu mu ƙarfafa wasu.
21. Wacce ce muhimmiyar hanya da za mu yi amfani da ikonmu?
21 Jehobah ya kafa kamiltaccen misali wajen amfani da ikonsa yadda ya dace. Za mu so mu bi misalinsa gwargwadon iyawarmu mu mutane ajizai. Za mu iya yin amfani da ikonmu yadda ya dace ta wajen bi da wasu da daraja wasu da muke da ɗan iko a kansu. Bugu da ƙari, muna so mu yi bauta da dukan ranmu wajen yin aikin ceton rai na wa’azi da Jehobah ya ba mu. (Romawa 10:13, 14) Ka tuna, Jehobah yana farin ciki idan ka ba da abu mafi kyau da kai—ranka—zai iya bayarwa. Zuciyarka ba ta motsa ka ba, ka yi dukan abin da za ka iya wajen bautar irin wannan Allah mai fahimi da kuma ƙauna? Babu wata muhimmiyar hanya fiye da wannan da za mu yi amfani da ikonmu.
a A zamanin Littafi Mai Tsarki, kalmar Ibrananci na “bulala” tana nufin sanda, kamar wanda makiyayi yake amfani da shi wajen tsare tumakinsa. (Zabura 23:4) Hakanan, “bulalar” ikon iyaye yana nufin ja-gora cikin ƙauna, ba horo mai tsanani ba.