BABI NA 11
“Dukan Hanyoyinsa Gaskiya Ne”
1, 2. (a) Wane rashin adalci Yusufu ya fuskanta? (b) Ta yaya Jehobah ya gyara rashin adalcin?
RASHIN adalci ne ƙwarai. Kyakkyawan saurayi bai aikata laifi ba, amma sai ga shi a kurkuku, ana tuhumarsa da ƙoƙarin yin fyaɗe. Amma wannan ba shi ne rashin adalci na farko da ya fuskanta ba. Wasu shekaru kafin wannan, sa’ad da yake ɗan shekara 17, wannan saurayin, Yusufu, ’yan’uwansa suka ci amanarsa, suka kusa su halaka shi. Suka sayar da shi zuwa bauta a wata ƙasa. Can, ya ƙi rinjayar matar ubangidansa. Matar da ta fusata sai ta yi masa kissa, ta yi masa mugun sharri, haka abin ya faru da ya kasance a tsare. Abin baƙin ciki, kamar dai babu wanda zai yi roƙo domin Yusufu.
2 Amma, Allah wanda yake “son adalci da gaskiya” yana gani. (Zabura 33:5) Jehobah ya gyara rashin adalcin, ya juya abubuwa, kuma a ƙarshe aka ’yantar da Yusufu. Ƙari ga hakan, Yusufu, mutumin da aka jefa a kurkuku—a ƙarshe aka ɗora shi bisa hakki mai girma kuma na ɗaukaka mai girma sosai. (Farawa 40:15; 41:41-43; Zabura 105:17, 18) A ƙarshe, aka kunita Yusufu, kuma ya yi amfani da matsayinsa mai girma wajen ɗaukaka nufin Allah.—Farawa 45:5-8.
Yusufu ya fuskanci rashin adalci a kurkuku
3. Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa dukanmu muna son a yi mana adalci?
3 Irin wannan labarin yana sosa mana zuciya, ko ba haka ba? Waye a tsakaninmu bai taɓa ganin rashin adalci ba ko kuma ba a taɓa yi masa rashin adalci ba? Hakika, dukanmu muna so a yi mana adalci, babu son rai. Wannan ba abin mamaki ba ne, tun da Jehobah ya ba mu hali irin na mutuntakarsa, kuma shari’a tana cikin halayensa na musamman. (Farawa 1:27) Domin mu san Jehobah da kyau, muna bukatar mu fahimci shari’arsa. Sa’an nan za mu kai ga son hanyoyinsa na ban mamaki sosai kuma ta motsa mu mu matso kusa da shi.
Mene ne Adalci?
4. A ra’ayi na ’yan Adam, yaya aka fahimci adalci sau da yawa?
4 A ra’ayi na ’yan Adam, sau da yawa adalci ba ya shige amfani da ƙa’idodin doka ban da son zuciya. Littafin nan Right and Reason—Ethics in Theory and Practice ya ce “adalci yana da nasaba da doka, wajibi, hakki, da kuma ayyuka, kuma tana yanke shawararta babu son zuciya ko kuma ayyuka da suka cancanta.” Amma, adalcin Jehobah ya ƙunshi fiye da yin amfani kawai da abin da doka ta ce domin cewa wajibi ne.
5, 6. (a) Mene ne ma’anar asalin kalmar da aka fassara ta “adalci”? (b) Me ake nufi cewa Allah adali ne?
5 Faɗi da zurfin adalcin Jehobah za a fahimce shi sosai idan aka bincika kalmomi na asali da aka yi amfani da su cikin Littafi Mai Tsarki. A cikin Nassosin Ibrananci, an yi amfani da kalmomi uku na musamman. Kalmar da ana yawan fassara ta “adalci” za a iya fassara ta ‘abin da yake daidai.’ (Farawa 18:25) Sauran kalmomi biyun ana fassara su “adalci” ne. A cikin Nassosin Kirista na Helenanci, kalmar da aka fassara ta “adalci” an fassara ta da ma’anar “kasancewa da gaskiya ko kuma daidaita.” Saboda haka, adalci da shari’a suna da alaƙa.—Amos 5:24.
6 Idan Littafi Mai Tsarki ya ce Allah adali ne, yana gaya mana ne cewa yana yin abin da yake daidai ko da ba na tara ba kuma yana yin haka ko da yaushe, ba tare da wariya ba. (Romawa 2:11) Hakika, ya fi gaban fahimi a ce zai aikata abu akasarin haka. Elihu mai adalci ya ce: “Allah ba zai taɓa aikata mugunta ba! A wurin Mai Iko Duka babu kuskure!” (Ayuba 34:10) Hakika, ba zai yiwu Jehobah ya yi mugunta ba. Me ya sa? Domin dalilai biyu masu muhimmanci.
7, 8. (a) Me ya sa Jehobah ba zai iya rashin adalci ba? (b) Me yake motsa Jehobah ya yi adalci da gaskiya a sha’aninsa?
7 Na farko, yana da tsarki. Kamar yadda muka gani a Babi na 3, Jehobah tsarkinsa babu iyaka kuma adali ne. Saboda haka, ba zai iya yin rashin adalci ko rashin gaskiya ba. Ka yi la’akari da abin da wannan yake nufi. Tsarkakkar Ubanmu na sama ya ba mu dalilin tabbaci cewa ba zai taɓa zaluntar yaransa ba. Yesu ya kasance da wannan tabbacin. A rana ta ƙarshe na rayuwarsa a duniya, ya yi addu’a: “Ya Uba Mai Tsarki, ka lura da su [almajiran] da ikon sunanka.” (Yohanna 17:11) “Uba Mai Tsarki”—a cikin Nassosi laƙabi ne ga Jehobah shi kaɗai. Wannan ya dace, domin babu uba na jiki da za a gwada shi da Allah a tsarki. Yesu yana da cikakken tabbaci cewa almajiran suna kāre a hannun Uban, wanda yake da cikakken tsabta kuma yana da cikakken keɓewa daga zunubi.—Matiyu 23:9.
8 Na biyu, ƙauna marar son kai muhimmiya ce ga mutuntakar Allah. Irin wannan ƙauna ta motsa shi ya kasance adali a sha’aninsa da wasu. Amma, rashin adalci iri-iri ne—ya haɗa da ƙabilanci, wariya, da kuma son zuciya—sau da yawa hakan na tasowa ne daga haɗama da son kai, kishiyar ƙauna. Game da Allah na ƙauna, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana: “Yahweh mai adalci ne, yana ƙaunar ayyukan adalci.” (Zabura 11:7) Jehobah ya ce game da kansa: “Ni Yahweh ina ƙaunar yin gaskiya.” (Ishaya 61:8) Ba abin ƙarfafa ba ne mu sani cewa Allah yana farin ciki wajen yin abin da yake nagari?—Irmiya 9:24.
Jinƙai da Kuma Kamiltacciyar Shari’a ta Jehobah
9-11. (a) Wace dangantaka ce take tsakanin shari’ar Jehobah da kuma jinƙansa? (b) Ta yaya shari’ar Jehobah da kuma jinƙansa suka bayyana a hanyar da yake bi da mutane masu zunubi?
9 Shari’ar Jehobah, kamar kowanne cikin mutuntakarsa ba ta da ta biyu, kamiltacciya ce, ba ta bukatar gyara. Da yake ɗaukaka Jehobah, Musa ya rubuta: “Dutse ne shi, aikinsa cikakke ne, kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Allah mai aminci ne, ba ya ruɗu, mai adalci ne shi, mai gaskiya kuma.” (Maimaitawar Shari’a 32:3, 4) Kowacce shari’ar Jehobah ba ta da aibi—ba ta da sauƙin banza kuma ba ta da azaba.
10 Da akwai dangantaka ta kusa tsakanin shari’ar Jehobah da kuma jinƙansa. Zabura 116:5 ta ce: “Yahweh mai tausayi ne mai gaskiya kuma, Allahnmu mai jinƙai ne.” Hakika, Jehobah mai adalci ne kuma mai jinƙai. Halaye biyun ba su saɓa ba. Yin jinƙansa ba rage shari’arsa ba ne, kamar a ce shari’arsa idan ba haka ba za ta kasance da tsanani ƙwarai. Maimakon haka, halaye biyun sau da yawa yana nuna su a lokaci ɗaya, har ma a aukuwa iri ɗaya. Alal misali.
11 Dukan mutane sun gāji zunubi kuma domin haka sun cancanci sakamakon zunubi, wato mutuwa. (Romawa 5:12) Amma Jehobah baya farin ciki a mutuwar masu zunubi. Shi Allah “mai yin gafara ne, mai alheri, kuma mai jinƙai.” (Nehemiya 9:17) Duk da haka, domin shi mai tsarki ne, ba zai ƙyale rashin adalci ba. To, ta yaya zai nuna jinƙai ga mutane da suka gāji zunubi? An samu amsar a cikin ɗaya daga cikin muhimmiyar gaskiya ta Kalmar Allah: tanadin Jehobah na fansa domin ceton ’yan Adam. A Babi na 14 za mu sami ƙarin bayani game da wannan tsarin ƙauna. A karo ɗaya, adalci ne ƙwarai kuma jinƙai ne mai girma. Ta wajen su, Jehobah zai nuna jinƙai ga masu zunubi da suka tuba yayin nan kuma yana riƙe da mizanansa na kamiltacciyar shari’a.—Romawa 3:21-26.
Adalcin Jehobah Tana Daɗaɗa Zuciya
12, 13. (a) Me ya sa shari’ar Jehobah take jawo mu gare shi? (b) Yaya Dauda ya kammala game da shari’ar Jehobah, kuma ta yaya wannan zai ƙarfafa mu?
12 Shari’ar Jehobah ba hali ba ce na rashin tausayi da take korarmu, amma hali ne mai kyau da yake jawo mu kusa da shi. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta tausayi na shari’ar Jehobah, ko kuma adalcinsa. Bari mu bincika wasu hanyoyi masu daɗaɗa zuciya da Jehobah yake yin shari’arsa.
13 Kamiltacciyar shari’ar Jehobah ce take motsa shi ya yi aminci kuma ya manne wa bayinsa. Mai Zabura Dauda ya fahimci wannan fanni na shari’ar Jehobah da kansa. Daga abin da ya fuskanta da kuma nasa nazarin hanyoyin Allah, yaya Dauda ya kammala? Ya ce: “Yahweh yana ƙaunar shari’ar gaskiya, ba zai ƙyale masu ƙaunarsa ba, zai kiyaye masu adalci har abada.” (Zabura 37:28) Wannan tabbaci ne ƙwarai mai ƙarfafawa! Allahnmu ba zai taɓa yasar da wanda ya manne masa ba ko na ɗan lokaci. Saboda haka, za mu iya dogara bisa kusancinsa da kuma kulawarsa mai kyau. Shari’arsa ta ba da tabbacin wannan!—Karin Magana 2:7, 8.
14. Ta yaya damuwar Jehobah ga matsiyata ya bayyana a cikin Dokar da ya ba wa Isra’ila?
14 Shari’ar Allah tana sane da bukatun waɗanda suke wahala. Damuwa da Jehobah yake yi da matsiyata ya bayyana cikin Dokar da ya ba wa Isra’ila. Alal misali, Dokar ta yi tanadi na musamman ta tabbata cewa an kula da marayu da gwauraye. (Maimaitawar Shari’a 24:17-21) Fahimtar yadda rayuwa za ta kasance da wuya ga irin waɗannan iyalan, Jehobah da kansa ya zama ubansu Alƙali da kuma Mai Kāre su, wanda yake yin “shari’ar gaskiya wa marayu da matan da mazansu suka mutu.” a (Maimaitawar Shari’a 10:18; Zabura 68:5) Jehobah ya yi wa Isra’ilawa gargaɗi cewa idan suka zalunci mata da yara, babu shakka zai saurari kukansu. Ya ce: “Fushina zai tashi da zafi a kanku.” (Fitowa 22:22-24) Ko da yake fushi ba ya cikin hali na musamman na Jehobah, ana sa ya yi fushi na adalci ta wajen ayyuka marasa adalci da gangan, musamman ma idan waɗanda ake zalunta marasa ƙarfi ne marasa taimako.—Zabura 103:6.
15, 16. Mene ne tabbaci mai ban mamaki na rashin son zuciya na Jehobah?
15 Jehobah kuma ya tabbatar mana cewa “ba ya nuna bambanci kuma ba ya karɓar cin hanci.” (Maimaitawar Shari’a 10:17) Ba kamar mutane da yawa ba da suke da iko ko rinjaya, ba a rinjayar Jehobah da dukiya ko kuma siffa. Ba shi da maguɗi ko son kai. Ka ga tabbaci na ban mamaki na rashin nuna son zuciya na Jehobah. Damar zama masu bauta masa na gaske, da begen rai na har abada, ba a keɓe ga masu ilimi kalilan ba kawai. Maimakon haka, “yana karɓar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace al’umma.” (Ayyukan Manzanni 10:34, 35) Wannan dama mai ban sha’awa an ba wa kowa ko yaya matsayinsa, ko yaya launin fatarsa, ko yaya ƙasar da yake zaune cikinta. Wannan ba ita ce shari’a ba mafi kyau?
16 Da akwai wani ɓangaren shari’ar Jehobah da ya isa mu mai da hankali gare shi kuma mu daraja shi: hanyar da yake bi da waɗanda suka taka mizanansa na adalci.
Babu Wanda Za a Ƙyale Babu Horo
17. Ka yi bayanin abin da ya sa zunubi na wannan duniyar ba zai shafi shari’ar Jehobah ba.
17 Wasu za su yi mamaki: ‘Tun da Jehobah ba ya ƙyale rashin adalci, yaya za mu yi bayani game da wahala daga rashin adalci da kuma miyagun ayyuka da suka cika duniya a yau?’ Irin waɗannan zunubi ba za su shafi shari’ar Jehobah ba. Rashin adalci da yawa a wannan muguwar duniya sakamako ne na zunubin da mutane suka gāda daga Adamu. A duniya da mutane ajizai suka zaɓi hanyarsu ta zunubi, rashin adalci ya yi yawa—amma ba na dogon lokaci ba.—Maimaitawar Shari’a 32:5.
18, 19. Mene ne ya nuna cewa Jehobah ba zai ƙyale waɗanda suke taka dokokinsa na adalci da gangan har abada ba?
18 Yayin da Jehobah yake nuna jinƙai ga waɗanda suka matso kusa da shi cikin gaskiya, ba zai ƙyale yanayin da yake ɓata masa suna ba har abada. (Zabura 74:10, 22, 23) Allah mai shari’a ba za a yi masa ba’a ba; ba zai kāre masu zunubi da gangan daga shari’a mai tsanani ba domin ayyukansu. Jehobah “Allah mai jinƙai ne, mai alheri, marar saurin fushi, mai yawan ƙauna marar canjawa, cike da aminci kuma, . . . Duk da haka ba mai kāsa hukunta mai laifi ba ne.” (Fitowa 34:6, 7) Cikin jituwa da waɗannan kalmomin, a wasu lokatai Jehobah ya ga ya zama dole ya hukunta waɗanda da gangan suka taka dokokinsa na adalci.
19 Alal misali, ka lura da yadda Allah ya bi da Isra’ila ta dā. Har bayan sun zauna cikin Ƙasar Alkawari, Isra’ilawa suka riƙa faɗawa cikin rashin aminci. Ko da yake miyagun ayyukansu ya sa Jehobah ya yi ‘fushi,’ ba kawai nan da nan ya yasar da su ba. (Zabura 78:38-41) Maimakon haka, ya yi musu jinƙai ya ba su zarafin su canja tafarkunsu. Ya roƙe su: “Ba na jin daɗin mutuwar mugun mutum, amma na fi so mugun mutum ya juyo ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo! Ku juyo daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya ku Gidan Isra’ila?” (Ezekiyel 33:11) Ganin tamanin rai, Jehobah ya yi ta aika musu da annabawa saboda Isra’ilawan su juyo daga miyagun hanyoyinsu. Amma galibinsu, mutanen masu taurin zuciya suka ƙi su saurara kuma su tuba. A ƙarshe, domin sunansa mai tsarki da kuma dukan abin da yake nufi, Jehobah ya bayar da su ga hannun abokan gabansu.—Nehemiya 9:26-30.
20. (a) Yadda Jehobah ya bi da Isra’ilawa ya koya mana Mene ne game da shi? (b) Me ya sa zaki alama ce da ta dace na bayyanar Jehobah da kursiyinsa?
20 Yadda Jehobah ya bi da Isra’ilawa ya koya mana abubuwa da yawa game da shi. Mun koyi cewa Jehobah idanunsa da suke ganin ko’ina suna lura da rashin adalci kuma abin da yake gani suna damunsa. (Karin Magana15:3) Kuma ya ba da ƙarfafa mu sani cewa yana neman hanyar da zai yi jinƙai idan da dalilin yin haka. Bugu da ƙari, mun koyi cewa shari’arsa ba a cikin hanzari ba ne. Domin haƙurin Jehobah, mutane da yawa suna kammala cikin kuskure cewa ba zai hukunta miyagu ba. Amma wannan ya yi nesa da gaskiya, domin yadda Allah ya bi da Isra’ilawa ya koya mana cewa haƙurin Allah yana da iyaka. Jehobah yana riƙe adalci ƙwarai. Ba kamar mutane ba, waɗanda sau da yawa suna janyewa daga nuna shari’a, bai taɓa rashin gaba gaɗi ba domin ya tsaya ga abin da yake nagari. Kamar yadda ya dace, zaki alamar gaba gaɗi na shari’a yana da mahaɗi da bayyanar Jehobah da kuma kursiyinsa. b (Ezekiyel 1:10; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:7) Domin haka za mu tabbata cewa zai cika alkawarinsa na share rashin adalci daga duniya. Hakika, hanyar shari’arsa za a iya cewa: tsayin daka a dukan inda ya dace, jinƙai a dukan inda ya yiwu.—2 Bitrus 3:9.
Matsowa Kusa da Allah Mai Shari’a
21. Sa’ad da muka yi bimbini bisa yadda Jehobah yake yin shari’a, a wace hanya ce ya kamata mu yi tunaninsa, kuma me ya sa?
21 Sa’ad da muka yi bimbini bisa yadda Jehobah ya nuna shari’a, bai kamata ba mu yi tunaninsa kamar marar tausayi, alƙali mai zalunci da ya damu da hora marasa laifi kawai. Maimakon haka, ya kamata mu yi tunaninsa kamar Uba ne mai tsayawa tsayin daka wanda koyaushe yana bi da yaransa ta hanya mafi kyau. Tun da shi ne Uba mai adalci, Jehobah yana daidaita tsayawa tsayin dakarsa game da abin da yake nagari da tausayi ga ’ya’yansa na duniya, waɗanda suke bukatar taimakonsa da kuma gafara.—Zabura 103:10, 13.
22. Ta ja-gorar shari’arsa, Jehobah ya sa me ya yiwu mana domin mu sami wace dama, kuma me ya sa yake bi da mu ta wannan hanyar?
22 Kai, muna godiya cewa shari’ar Allah ta wuce yanke hukunci bisa masu laifi kawai! Ta wajen ja-gorar shari’arsa, Jehobah ya sa ya yiwu mana mu samu dama mai ban sha’awa—kamiltacciya, rai madawwami a duniya inda “adalci zai kasance kullum.” (2 Bitrus 3:13) Allahnmu yana bi da mu ta wannan hanyar domin shari’arsa tana neman ta yi ceto ne maimakon ta halaka. Hakika, fahimtar zurfin shari’ar Jehobah tana jawo mu gare shi! A babi na gaba, za mu bincika yadda Jehobah yake nuna wannan hali mai ban sha’awa.
a Kalmar nan “marayu” ta nuna cewa Jehobah yana kula da yara maza da mata. A cikin Dokar Jehobah ya haɗa da ƙa’ida da ta ba da tabbacin bai wa ’ya’yan Zelophehad marayu mata gadō. Wannan hukuncin ya kafa ƙa’ida, saboda haka ya ba wa marayu mata hakkinsu.—Littafin Ƙidaya 27:1-8.
b Daidai fa, Jehobah ya kwatanta kansa da zaki wajen yin hukunci bisa Isra’ilawa marasa adalci.—Irmiya 25:38; Hosiya 5:14.