BABI NA 12
Allah Yana Yin Rashin Adalci Ne?
1. Ta yaya rashin adalci yake shafanmu?
WATA gwauruwa tsohuwa an damfare ta ajiyar da ta yi a rayuwarta. Uwa marar ƙauna ta yar da ɗan jariri. An ɗaure wani mutum a fursuna bisa laifin da bai yi ba. Yaya ka ji game da irin waɗannan yanayin? Wataƙila, kowanne ya ta da maka hankali, kuma da dalilin haka. Mu mutane muna da azanci mai ƙarfi na bambance abin da yake nagari da kuma mugu. Idan aka yi rashin adalci yana damunmu. Muna son a saka wa wanda aka cuta kuma a hukunta macucin. Idan ba a yi haka ba, wataƙila mu yi tambaya: ‘Allah yana ganin abin da yake faruwa kuwa? Me ya sa bai yi kome ba?’
2. Me Habakkuk ya yi domin rashin adalci, kuma me ya sa Jehobah bai kushe shi ba domin wannan?
2 A cikin dukan tarihi, amintattun bayin Jehobah sun yi irin waɗannan tambayoyi. Alal misali, annabi Habakkuk ya yi wa Allah tambaya: “Me ya sa ka sa na ga mugunta na kuma ga wahala? Halaka da tashin hankali suna gabana. Jayayya da gardama sun taso.” (Habakkuk 1:3) Jehobah bai kushe Habakkuk ba domin tambayarsa ta adalci, domin shi ne wanda ya saka shari’a a zuciyar ’yan Adam. Hakika, Jehobah ya albarkace mu da ɗan azancinsa na shari’a.
Jehobah Yana Ƙyamar Rashin Adalci
3. Me ya sa za a ce Jehobah yana sane da rashin adalci fiye da mu?
3 Jehobah yana damuwa da rashin adalci. Yana ganin abin da yake faruwa. Game da zamanin Nuhu, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh kuwa ya lura cewa muguntar ’yan Adam ta yi yawa a duniya, kuma kowane tunanin zuciyarsu zallar mugunta ce kullum.” (Farawa 6:5) Ka yi la’akari da muhimmancin wannan furuci. Sau da yawa, fahiminmu na shari’a ya dangana ne bisa wasu aukuwa da muka ji ko kuma waɗanda muka fuskanta mu kanmu. Akasin haka, Jehobah yana sane da rashin adalci na dukan duniya. Yana ganin dukansu! Fiye ma da haka, zai iya fahimtar tunanin zuciya—mummunan tunani da yake ƙarƙashin rashin adalci.—Irmiya 17:10.
4, 5. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ya damu da waɗanda aka yi musu rashin adalci? (b) Ta yaya Jehobah kansa rashin adalci ya taɓa shi?
4 Amma, Jehobah yana yi fiye da kawai ya lura da rashin adalci. Yana damuwa da waɗanda ya shafe su. Sa’ad da al’ummai abokan gāba ke azabtar da mutanensa, Jehobah ya ji zafin “nishinsu da suka yi a hannun masu ba su wahala da masu yi musu danniya.” (Alƙalai 2:18) Wataƙila ka lura cewa da zarar wasu mutane suka dinga ganin rashin adalci, hakanan zuciyarsu za ta taurara da shi. Ba haka yake ba da Jehobah! Ya ga rashin adalci a launinsa iri-iri na shekara 6,000, duk da haka bai motsa ba daga ƙyamarsa. Maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Jehobah yana ƙyamar mutane masu yin abubuwa kamar su “harshe mai faɗin ƙarya,” “da hannuwa masu zub da jinin marasa laifi,” “mai shaidar ƙarya wanda ya baza ƙarya.”—Karin Magana 6:16-19.
5 Ka yi la’akari kuma da yadda Jehobah ya kushe ƙwarai shugabannin Isra’ila marasa adalci. “Ashe, bai kamata ku san shari’ar gaskiya ba?” ya hure annabinsa ya tambaye su. Bayan ya kwatanta yadda suka yi ɓarna da ikonsu cikin kalmomi na musamman, Jehobah ya faɗi sakamakon ga waɗannan mutane malalata: “Za ku yi kuka ga Yahweh, amma ba zai amsa muku ba. Zai ɓoye fuskarsa daga gare ku a lokacin, saboda kun aikata mugunta.” (Mika 3:1-4) Jehobah yana ƙyamar rashin adalci ƙwarai! Hakika, shi kansa ma ya fuskanci rashin adalci! Shekaru aru-aru, Shaiɗan yana ta zolayarsa cikin rashin adalci. (Karin Magana 27:11) Bugu da ƙari, mugun aikin rashin adalci ya taɓa Jehobah sa’ad da Ɗansa, wanda “bai taɓa yin laifi ba ko kaɗan,” aka kashe shi kamar mai laifi. (1 Bitrus 2:22; Ishaya 53:9) A bayyane yake, Jehobah ya damu da wahalar waɗanda suke wahala daga rashin adalci.
6. Me muke yi sa’ad da muka fuskanci rashin adalci, kuma me ya sa?
6 Shi ya sa, sa’ad da muka lura da rashin adalci—ko mu kanmu aka yi mana rashin adalci—sai ya kasance kamar mu yi kuka. An halicce mu a kamanin Allah, kuma rashin adalcin akasin dukan abin da matsayin Jehobah yake nufi ne. (Farawa 1:27) To, me ya sa Allah ya ƙyale rashin Adalci?
Batu Mai Muhimmanci
7. Ka kwatanta yadda aka ƙalubalanci sunan Jehobah da ikon mallakarsa.
7 Amsar tambayar ta dangana a kan wani batu mai muhimmanci. Kamar yadda muka gani, Mahalicci yana da hakkin ya yi sarauta bisa duniya da dukan abin da suke cikinta. (Zabura 24:1; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) Amma da farko cikin tarihin ’yan Adam, an ɓata sunan Allah kuma an ƙalubalanci ikon mallakarsa. Ta yaya wannan ya faru? Jehobah ya dokaci mutum na farko, Adamu, kada ya ci daga wani itace a lambun da gidansa ne, Aljanna. Kuma idan ya yi rashin biyayya fa? “Lallai za ka mutu,” Allah ya gaya masa. (Farawa 2:17) Dokar Allah ba wahala ba ce ga Adamu ko kuma matarsa, Hauwa’u. Duk da haka, Shaiɗan ya ruɗi Hauwa’u cewa Allah yana hana su sukuni ne kawai. Me zai faru idan ta ci daga itacen? Shaiɗan ya gaya wa Hauwa’u kai tsaye: “Ko kaɗan, ba za ku mutu ba. Gama Allah ya sani cewa a ranar da kuka ci daga ’ya’yan itacen nan, idanunku za su buɗe. Za ku kuwa zama kamar Allah, masu sanin nagarta da mugunta.”—Farawa 3:1-5.
8. (a) Mene ne manufar furucin Shaiɗan ga Hauwa’u? (b) Mene ne Shaiɗan ya ƙalubalanta game da sunan Allah da ikon mallakarsa?
8 Wannan furucin Shaiɗan yana nufin ba kawai cewa Jehobah ya hana Hauwa’u sani da ya wajaba ba ne amma cewa Ya yi mata ƙarya. Shaiɗan ya sa Hauwa’u ta soma shakkar Jehobah. Ta hakan, ya ɓata sunan Allah. Ya kuma ƙalubalanci ikon mallakar Jehobah. Shaiɗan ya mai da hankali don kada ya tuhumi gaskiyar cewa Allah ne mamallakin dukan halitta. Amma ya ƙalubalanci dacewarsa, cancantarsa, da kuma adalcinsa. Wato, yana nufi ne cewa Jehobah ba ya mulki cikin adalci a hanyar da talakawansa za su amfana.
9. (a) Ga Adamu da Hauwa’u, mene ne sakamakon rashin biyayyarsu, kuma waɗanne tambayoyi ne masu muhimmanci suka taso? (b) Me ya sa Jehobah bai halaka ’yan tawayen nan a take ba?
9 Daga baya, Adamu da Hauwa’u suka yi wa Jehobah rashin biyayya ta wajen cin itace da aka haramta musu. Domin rashin biyayyarsu horonsu mutuwa ne, kamar yadda Allah ya faɗa. Ƙaryar Shaiɗan ta jawo tambayoyi. Shin da gaske ne cewa Jehobah yana da hakkin ya yi sarauta bisa ’yan Adam, ko dai ya kamata mutum ya mallaki kansa? Shin Jehobah yana amfani da ikon mallakarsa ta hanya mafi kyau kuwa? Da Jehobah zai yi amfani da ikonsa mai girma ya halaka ’yan tawayen nan da nan. Amma tambayoyi da suka taso, game da sunan Allah ne, kuma hakan ya haɗa da sarautarsa, ba ikonsa ba. Saboda haka, kashe Adamu, Hauwa’u da kuma Shaiɗan ba zai tabbatar da adalcin mulkin Allah ba. Akasin haka, sai dai ya ƙara sa a tuhumi sarautarsa. Hanyar da kawai za ta tabbata ko ’yan Adam za su iya nasara wajen mallakar kansu, da ’yanci daga Allah, ita ce a ba su lokaci.
10. Mene ne tarihi ya nuna game da sarautar ’yan Adam?
10 Mene ne ya bayyana da shigewar lokaci? A duk cikin ƙarnuka, mutane sun gwada ire-iren gwamnatoci da yawa, haɗe da sarautar mutum ɗaya, dimokuraɗiyya, rugurguzu, da kuma kwaminis. An taƙaita dukansu cikin furuci na gaskiya na Littafi Mai Tsarki: “Na ga wani yana da iko a kan waɗansu, ikon kuwa ya cuce shi.” (Mai-Wa’azi 8:9) Da kyakkyawar dalili, annabi Irmiya ya ce: “Na sani, Ya Yahweh, hanyar rayuwar ɗan Adam ba a hannunsa take ba. Ba mutum ne yake da iko ya kiyaye tafiyarsa ba.”—Irmiya 10:23.
11. Me ya sa Jehobah ya ƙyale ’yan Adam su sha wahala?
11 Jehobah ya sani tun da farko cewa ’yancin ’yan Adam, ko kuma mallakar kansu, zai kawo wahala ƙwarai. Amma rashin adalci ne a gare shi ya ƙyale wannan yanayi ya cika? A’a! Alal misali: A ce kana da yaro wanda yake bukatar fiɗa domin a yi maganin cuta da take so ta kasance ajalinsa. Ka lura cewa wannan fiɗar za ta ɗan wahalar da yaron, kuma wannan ya dame ka ƙwarai. Amma kuma, ka sani cewa wannan za ta sa yaron ya more rayuwa mafi kyau a nan gaba. Hakazalika, Allah ya sani—har ma ya annabta—cewa ƙyale sarautar ’yan Adam zai kawo ɗan azaba da kuma wahala. (Farawa 3:16-19) Amma ya sani kuma cewa sauƙi mai ma’ana kuma na dindindin zai yiwu ne kawai idan ya ƙyale ’yan Adam suka ga mugun sakamakon tawaye. A wannan hanyar ce kawai za a iya sulhunta wannan batun dindindin, har abada.
Batun Amincin Mutum
12. Kamar yadda aka nuna a batun Ayuba, wace tuhuma ce Shaiɗan ya yi wa ’yan Adam?
12 Da akwai kuma wani ɓangare na wannan batun. Wajen ƙalubalantar dacewar sarautar Allah da kuma adalcinsa, ba kawai Shaiɗan ya yi ƙarya game da ikon mallakar Jehobah da kuma sunansa ba; amma kuma ya yi ƙarya game da bayin Allah da amincinsu. Alal misali, ka lura da abin da Shaiɗan ya gaya wa Jehobah game da mutum mai aminci Ayuba: “A’i, yana jin tsoronka gama kai ka kewaye shi da katanga, da shi, da gidansa, da dukan abin da yake da shi a kowane gefe. Ka kuma albarkaci ayyukan hannuwansa domin abin da ya mallaka sun yaɗu ko’ina a ƙasar. Amma yanzu sai ka miƙa hannunka, ka raba shi da dukan abin da yake da shi, za ka gani lallai zai fito a fili ya yi maka saɓo.”—Ayuba 1:10, 11.
13. Mene ne Shaiɗan yake nufi a tuhumarsa game da Ayuba, kuma ta yaya wannan ya shafi dukan ’yan Adam?
13 Shaiɗan ya ce wai Jehobah yana amfani ne da Ikonsa na kāriya ya yi wa Ayuba toshiya. Watau, wannan yana nufi ne cewa amincin Ayuba riya ce kawai, wai yana bauta wa Allah ne kawai domin abin da zai samu. Shaiɗan ya ce idan aka hana Ayuba albarkar Allah, wannan mutumin zai saɓi Mahaliccinsa. Shaiɗan ya san cewa Ayuba shahararre wajen kasancewa “marar laifi ne kuma mai gaskiya a zuci. Yana jin tsoron [Allah], yana kuma juya baya ga mugunta.” a Saboda haka, idan Shaiɗan zai iya sa Ayuba ya yi rashin aminci, mene ne wannan zai nufa ga sauran ’yan Adam? Saboda haka Shaiɗan yana ƙalubalantar amincin dukan waɗanda suke so su bauta wa Allah ne. Hakika, in aka faɗaɗa batun, Shaiɗan ya ce wa Jehobah: “Ai, lallai mutum zai iya ba da dukan abin da yake da shi domin ya ceci ransa.”—Ayuba 1:8; 2:4.
14. Mene ne tarihi ya nuna game da zargin ’yan Adam da Shaiɗan ya yi?
14 Tarihi ya nuna cewa mutane da yawa, kamar Ayuba, sun kasance da aminci ga Allah sa’ad da suke fuskantar jarraba—akasin da’awar Shaiɗan. Sun faranta wa Jehobah rai ta wajen tafarkinsu na aminci, kuma wannan ya ba wa Jehobah amsa ga zolaya cikin fahariya na Shaiɗan cewa ’yan Adam za su daina bauta wa Allah idan aka azabtar da su. (Ibraniyawa 11:4-38) Hakika, masu zuciyar kirki suna ƙi su juya wa Allah baya. Har lokacin da suka rikice domin yanayi mai wuya, suna dogara ga Jehobah ya ba su ƙarfi da za su jimre.—2 Korintiyawa 4:7-10.
15. Wace tambaya za a yi game da hukuncin Allah na dā da kuma mai zuwa a nan gaba?
15 Amma nuna shari’a na Jehobah ya ƙunshi fiye da batutuwan mulkin mallaka da amincin mutum. Littafi Mai Tsarki ya ba mu tarihin hukuncin Jehobah bisa mutane ɗai-ɗai da har ma da dukan al’umma. Kuma ya ƙunshi annabce-annabce na hukuncin da zai yi a nan gaba. Me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah yana yi kuma zai yi adalci a hukuncinsa?
Dalilin da Ya Sa Shari’ar Allah ta Fi Girma
16, 17. Waɗanne misalai ne suka nuna cewa mutane suna da iyaka wajen fahimi idan ya zo ga shari’a ta gaskiya?
16 Game da Jehobah, da gaske za a iya cewa: “Dukan hanyoyinsa gaskiya ne.” (Maimaitawar Shari’a 32:4) Babu wani cikinmu da zai iya yin wannan da’awar game da kansa, domin sau da yawa fahiminmu mai iyaka zai iya duhunta fahimtar abin da yake nagari. Alal misali, ka yi la’akari da Ibrahim. Ya roƙi Jehobah game da halaka Saduma—duk da mugunta da take ko’ina a can. Ya tambayi Jehobah: “Ashe, za ka halaka mai adalci tare da mai mugunta?” (Farawa 18:23-33) Hakika, a’a. Sai da Lot mai aminci da ’ya’yansa mata suka sauƙa lafiya a birnin Zoar kafin Jehobah ya “yi ta zuba wa Sodom da Gomora wuta da farar wuta mai wari.” (Farawa 19:22-24) Akasin haka, Yunana ya cika da “fushi” sa’ad da Allah ya yi wa mutanen Nineveh jinƙai. Tun da Yunana ya riga ya sanar da halakarsu, da zai yi farin ciki ya ga an shafe su—ko yaya tubar zuciyarsu.—Yona 3:10–4:1.
17 Jehobah ya tabbatar wa Ibrahim cewa nuna shari’arsa ya ƙunshi ceton masu adalci ba halaka miyagu kawai ba. A wani ɓangare kuma, Yunana dole ya koyi cewa Jehobah yana da jinƙai. Idan miyagu suka tuba, Jehobah yana “yin gafara.” (Zabura 86:5) Ba kamar mutane ba waɗanda suke cike da tsoro, Jehobah ba ya yin hukunci mai tsanani kawai domin ya nuna ikonsa, ko kuma ya ƙi tausayawa domin yana tsoron za a ce da shi raunane. Hanyarsa ta nuna jinƙai ne a dukan wurin da akwai dalilin yinsa.—Ishaya 55:7; Ezekiyel 18:23.
18. Ka nuna daga cikin Littafi Mai Tsarki cewa Jehobah ba ya aikata abu bisa motsin zuciya.
18 Duk da haka, motsin zuciya ba ta rufe wa Jehobah idanu. Sa’ad da mutanensa suka bunƙasa cikin bautar gumaka, Jehobah ya ce: “Zan yi miki shari’a bisa ga hanyoyinki, zan hukunta ki saboda dukan abubuwan ban ƙyamar da kika yi. Ba zan bar ki ba, ba kuwa zan ji tausayinki ba. Zan hukunta ki bisa ga hanyoyinki.” (Ezekiyel 7:3, 4) Idan mutane suka taurara cikin ayyukansu, Jehobah yana hukunci hakanan. Amma hukuncinsa bisa ƙarfafar tabbaci ne. Saboda haka, sa’ad da ƙara ta faɗa kunnuwansa game da Saduma da Gwamrata, Jehobah ya ce: “Zan gangara in gani in bincika ko kukan da ya zo gare ni haka yake.” (Farawa 18:20, 21) Muna godiya ƙwarai da yake Jehobah ba kamar mutane ba ne waɗanda suke hukunci cikin gaggawa kafin ma su ji gaskiyar! Hakika, Jehobah yana nan kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta shi: “Allah mai aminci ne, ba ya ruɗu.”—Maimaitawar Shari’a 32:4.
Ka Dogara Bisa Shari’ar Jehobah
19. Mene ne za mu yi sa’ad da muke da tambaya domin rikicewa game da yadda Jehobah ya nuna shari’a?
19 Littafi Mai Tsarki bai amsa kowacce tambaya ba game da ayyukan Jehobah a dā; kuma bai ba da bayani dalla-dalla ba game da yadda Jehobah zai yi hukunci game da mutane da kuma rukuninsu a nan gaba. Sa’ad da muka rikice domin tarihi ko kuma annabci na Littafi Mai Tsarki domin babu ƙarin bayani, za mu nuna irin aminci da annabi Mikah ya nuna, wanda ya rubuta: “Zan zuba ido ga Yahweh zan jira Allah mai cetona.”—Mika 7:7.
20, 21. Me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah zai yi abin da yake nagari ko da yaushe?
20 Za mu tabbata cewa a kowane yanayi, Jehobah zai yi abin da yake daidai. Ko lokacin da kamar mutane sun ƙyale rashin adalci, Jehobah ya yi alkawari: “Ramuwa tawa ce, ni kuwa zan rama.” (Romawa 12:19) Idan muka nuna halin haƙuri, za mu maimaita tabbaci da manzo Bulus ya furta: “Allah bai yi daidai ba ke nan? Ina! Ko kaɗan!”—Romawa 9:14.
21 A yanzu dai, muna rayuwa a zamanin da ake shan “wahala sosai.” (2 Timoti 3:1) Rashin adalci da “danniya” ya kai ga zalunci iri-iri. (Mai-Wa’azi 4:1) Duk da haka, Jehobah bai canja ba. Har yanzu yana ƙyamar rashin aminci, kuma yana damuwa ƙwarai da waɗanda aka yi musu rashin aminci. Idan muka manne wa Jehobah da ikon mallakarsa, zai ba mu ƙarfin da za mu jimre har zuwa lokacin da ya ƙa’ide zai gyara dukan rashin aminci a ƙarƙashin Mulkinsa.—1 Bitrus 5:6, 7.
a Jehobah ya ce game da Ayuba: “Babu wani mai kama da shi a duniya.” (Ayuba 1:8) Wataƙila, Ayuba ya rayu ne bayan mutuwar Yusufu kuma kafin Musa ya zama naɗaɗɗen shugaban Isra’ila. Saboda haka, a wannan lokacin za a iya cewa daidai babu wanda yake da aminci kamar na Ayuba.