Abin da Yara Suke Bukata Daga Wurin Iyaye
DUKAN iyaye suna saka hannu cikin abin da ya fi gaban sanin mutane. Kowannensu yana ba da kaɗan daga jikinsa. Ta haka, abin da ya yi girma a cikin uwa ya zama mutum. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne, sa’ad da aka haifi jariri, mutane sukan ce “mu’ujizar haihuwa.”
Hakika, haihuwar yara ita ce hakkin iyaye na farko. Da farko, jarirai suna dogara ƙwarai ga iyayensu, amma sa’ad da suke girma, suna bukatar fiye da a mai da hankali ga abincinsu kawai. Suna bukatar taimako domin su yi girma a tunaninsu, a motsin rai, a ɗabi’a, da kuma a ruhaniya.
Domin su yi girma da kyau, yara musamman suna bukatar iyayensu su yi ƙaunarsu. Ko da yake yana da muhimmanci a furta kalami na ƙauna, ya kamata ayyuka su tokara hakan. Hakika, yara suna bukatar misali mai kyau daga iyayensu. Suna bukatar ja-gora a ɗabi’a, mizanai da za su bi a rayuwa. Kuma suna bukatar wannan tun suna ƙanƙanana zuwa gaba. Abubuwa masu ɓata rai suna iya faruwa kuma suna faruwa sa’ad da ba a taimaki yara ba har sai da ya makara.
Misalai mafi kyau ana samun su ne cikin Littafi Mai Tsarki. Umurni da suka fito daga Littafi Mai Tsarki suna da amfani na musamman. Ta wurin waɗannan umurnai, yara za su fahimci cewa abin da ake koya musu ba daga wurin wani mutum ba ne ya fito amma daga wurin Mahaliccinsu ne, Ubansu na samaniya. Wannan yana ƙarfafa gargaɗin yadda babu na biyunsa.
Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa iyaye su yi ƙoƙari su dasa mizanai da suka dace a zukatan ’ya’yansu. Sa’ad da yara suke girma yana yi wa iyaye wuya su yi magana da su game da abubuwa da suka fi amfani. An shirya wannan
littafin, Ka Koya Daga Wurin Babban Malami, domin ya hana irin wannan yanayin faruwa. Zai ba ka da ’ya’yanka abubuwa na ruhaniya da za ku karanta tare. Fiye ma da haka, ya kamata ya jawo taɗi tsakanin yara da waɗanda suke karanta musu wannan littafi.Za ka lura cewa littafin yana bukatar yara su ba da amsa. An yi tanadin tambayoyi da yawa a littafin da aka buga. Sa’ad da ka isa wurin za ka ga karan ɗauri (—). Wannan domin ya tuna maka ne ka dakata domin yaron ya yi kalami. Yara suna so a ba su zarafin magana. Idan ba tare da haka ba, ba wuya yaro sai ya ƙi.
Mafi muhimmanci ma, waɗannan tambayoyin za su taimake ka ka fahimci abin da yake zuciyar yaron. Hakika, yaro zai iya ba da amsa da ba daidai ba. Amma abin da ya bi bayan kowacce tambaya domin ya taimaka ne wajen faɗaɗa hanyar tunani mai kyau ga yaron.
Wani fanni na musamman na littafin shi ne hotuna fiye da 230 a ciki. Fiye da kome suna da rubutu da suke bukatar kalami daga yaro bisa abin da ya gani kuma da ya karanta. Saboda haka, ka dubi hotunan tare da yaro. Hanyar koyarwa ce mai kyau domin a fahimta darasi da ake koyarwa.
Sa’ad da yaron ya koyi karatu, ka ƙarfafa shi ya karanta maka littafin kuma ya karanta wa kansa. Da zarar ya karanta haka nan, gargaɗin zai kahu a zuciyarsa. Amma domin ka ƙarfafa dangantaka da take tsakaninka da yaronka, ya kamata ku karanta littafin tare a kai a kai.
A hanyoyin da ba za a ma yi tunaninsa ba a shekaru da suka shuɗe, yara suna ganin lalata, sihiri, da wasu munanan ayyuka. Saboda haka, suna bukatar kāriya, da wannan littafi yake taimakawa a hanya mai daraja kuma ta kai tsaye.
Duk da haka, yara suna bukatar musamman a ja-gorance su zuwa ga Tushen hikima, Ubanmu na samaniya Jehovah Allah. Wannan shi ne abin da Yesu, Babban Malami ya yi kullum. Muna fatan cewa wannan littafin zai taimake ka da kuma iyalinka wajen mulmula rayuwarku domin ta faranta wa Jehovah rai, domin ku sami madawwamiyar albarka.