Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 13

Wadanda Suka Zama Almajiran Yesu

Wadanda Suka Zama Almajiran Yesu

Wanene wannan mutumin, kuma ta yaya ya zama almajirin Yesu?

WANENE bawan Allah mafi kyau da ya taɓa rayuwa?— Gaskiyarka, Yesu Kristi ne. Kana tsammanin za mu iya zama kamar shi?— E, Littafi Mai Tsarki ya ce ya kafa mana misali mai kyau da za mu bi. Kuma ya gayyace mu mu zama almajiransa.

Ka san abin da ake nufi mutum ya zama almajirin Yesu?— Yana nufin abubuwa da yawa. Da farko, dole ne mu koya daga wurinsa. Amma har yanzu da saura. Kuma dole ne mu gaskata abin da ya ce. Idan muka gaskata abin da ya ce, za mu yi abin da ya gaya mana.

Mutane da yawa suna cewa sun gaskata da Yesu. Kana tsammanin dukansu ne almajiransa da gaske?— A’a, yawancinsu ba almajiransa ba ne. Wataƙila suna zuwa coci. Amma da yawa cikinsu ba su taɓa ba da lokaci su koyi abin da Yesu ya koyar ba. Hakika, waɗanda suka bi misalin Yesu ne kaɗai almajiransa.

Bari mu yi magana a kan waɗanda almajiran Yesu ne sa’ad da yake duniya. Ɗaya cikin waɗanda suka zama almajiran Yesu da farko, Filibbus ne. Filibbus ya je ya nemi abokinsa Natanayilu (wanda ake kira Barthalamawus), wanda kake gani yana zaune a gindin bishiya. Sa’ad da Natanayilu ya zo wajen Yesu, Yesu ya ce: ‘Duba, ga mutumin Isra’ila na gaske.’ Natanayilu ya yi mamaki sai ya yi tambaya: ‘Daga ina ka san ni?’

Su wa Yesu yake kira su zama almajiransa?

“Kafin Filibbus ya yi kiranka, sa’anda kana ƙarƙashin itacen ɓaure, na gan ka,” in ji Yesu. Natanayilu ya yi mamakin cewa Yesu ya san daidai inda yake, saboda haka Natanayilu ya ce: “Kai ne Ɗan Allah, kai ne Sarkin Isra’ila.”—Yohanna 1:49.

Yahuda Iskariyoti, Yahuda (wanda ake kira Taddawus), Siman

Wasu sun riga sun zama almajiran Yesu a ranar da ta gabaci ranar da Filibbus da Natanayilu suke zama. Waɗannan su ne Andarawus da wansa Bitrus da kuma Yohanna; wataƙila wan Yohanna, Yaƙub ma yana cikin waɗanda suka zama almajirai da farko. (Yohanna 1:35-51) Bayan wani lokaci, waɗannan mutane huɗu suka koma sana’arsu ta kama kifi. Wata rana da Yesu yake tafiya kusa da Tekun Galili, ya ga Bitrus da Andarawus suna saka ragarsu ta kama kifi cikin tekun. Yesu ya kira su: “Ku biyo ni.”

Yaƙub (ɗan Alfiyus), Toma, Matta

Da ya yi gaba kaɗan, sai Yesu ya ga Yaƙub da Yohanna. Suna cikin kwalekwale da babansu, suna gyarar ragarsu. Yesu ya kira su su bi shi su ma. Da me za ka yi da Yesu ya kira ka? Da za ka bi shi a take?— Waɗannan mutanen sun san Yesu. Sun sani cewa Allah ne ya aiko Yesu. Ba tare da ɓata lokaci ba suka ƙyale sana’arsu ta kamun kifi suka bi Yesu.—Matta 4:18-22.

Natanayilu, Filibbus, Yohanna

Da waɗannan mutane suka zama mabiyan Yesu, yana nufi ne cewa bayan haka koyaushe abin da suke yi daidai ne?— A’a. Za ka iya tuna cewa waɗannan mutane har ma sun yi musu a tsakaninsu game da wanene cikinsu ya fi girma. Amma sun saurari Yesu, kuma suna shirye su yi gyara. Idan muna shirye mu yi gyara mu ma za mu iya zama almajiran Yesu.

Yakub (dan’uwan Yohanna), Andarawus, Bitrus

Yesu ya gayyaci dukan ire-iren mutane su zama almajiransa. Sau ɗaya, wani saurayi masarauci mai arziki ya zo wajen Yesu ya tambayi Yesu yadda zai samu rai madawwami. Sa’ad da masarauci mai arziki ya ce yana kiyaye dokokin Allah tun yana yaro, Yesu ya gayyace shi: “Ka zo, ka biyo ni.” Ka san abin da ya faru?—

To, da mutumin ya fahimci cewa zama mabiyin Yesu zai zama da muhimmanci fiye da arziki, bai ji daɗi ba. Bai zama almajirin Yesu ba domin yana son kuɗinsa fiye da yadda yake ƙaunar Allah.—Luka 18:18-25.

Bayan Yesu ya yi wa’azi na kusan shekara ɗaya da rabi, ya zaɓi almajirai 12 su zama manzanninsa. Manzannin mutane ne da yake aikansu su yi ayyuka na musamman. Ka san sunayensu?— Bari mu gani ko za mu iya koyon sunayensu. Ga hotunansu a nan, ka faɗi sunayensu. Ka yi ƙoƙari ka faɗi sunayensu da ƙa.

Su wanene waɗannan mata da suka taimaka wa Yesu sa’ad da ya je wa’azi?

A ƙarshe, ɗaya cikin manzannin 12 ya zama mugu. Sunansa Yahuda Iskariyoti. Daga baya, aka zaɓi wani almajiri ya zama manzo. Ka san sunansa?— Sunansa Matiyas. Daga baya, Bulus da Barnaba suka zama manzanni su ma, amma su ba sa cikin manzanni 12 ɗin.—Ayukan Manzanni 1:23-26; 14:14.

Kamar yadda muka koya a Babi na 1 na wannan littafin, Yesu yana son yara ƙanana. Me ya sa ya yi haka?— Domin ya sani su ma za su iya zama almajiransa. Hakika, yara sau da yawa suna faɗan abubuwa a hanyar da yake sa manya su saurara kuma su so su koyi game da Babban Malami.

Mata ma da yawa sun zama almajiran Yesu. Wasu suna binsa sa’ad da ya je wani birni domin ya yi wa’azi. Maryamu Magdaliya, Yuwanna, da kuma Susannatu sun yi wannan. Wataƙila sun taimaka wajen dafa masa abinci da kuma wanke kayansa.—Luka 8:1-3.

Kana so ka zama almajirin Yesu?— Ka tuna, faɗa kawai cewa mu almajiran Yesu ne ba shi ke nan cewa da gaske mu almajiransa ne ba. Dole ne mu yi halin almajiransa a dukan inda muke, ba kawai sa’ad da muka je taro na Kirista ba. Za ka iya tuna wajajen da yake da muhimmanci mu yi halin almajirin Yesu?—

Hakika, ya kamata mu yi haka a gida. Amma har yanzu wani waje kuma shi ne a makaranta. Abin da ni da kai bai kamata mu manta ba, shi ne cewa domin a kasance almajiran Yesu, dole ne mu yi abubuwa kamar yadda ya yi ko da yaushe, kowacce rana, ko ina da muke.

A ina ne yake da muhimmanci mu yi hali irin na almajirin Yesu?

Yanzu bari mu karanta tare abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da almajiran Yesu a Matta 28:19, 20; Luka 6:13-16; Yohanna 8:31; da kuma 1 Bitrus 2:21.