Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA HUƊU

Alhakin Laifi—“Ka Tsarkake Ni Daga Zunubina”

Alhakin Laifi—“Ka Tsarkake Ni Daga Zunubina”

Wata ’yar’uwa mai suna Martha ta ce: “Aikin da nake yi ya inganta rayuwar iyalinmu, amma ya sa ni yin ayyukan da suka saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Na soma yin wasu bukukuwa kuma na shiga harkar siyasa, har ma na soma zuwa coci. Ni Mashaidiyar Jehobah ce amma na yi shekara 40 ban yi tarayya da ’yan’uwa a ikilisiya ba. Yayin da lokaci yake wucewa, sai na soma gani kamar Jehobah ba zai gafarta min zunubaina ba. Na ɗauka cewa zunubaina sun yi yawa ainun. Na san Shaidun Jehobah ne ke bin addini na gaskiya, amma na bijire.”

ALHAKI yana kamar kaya mai nauyi. Sarki Dauda ya ce: “Kurakuraina sun sha kaina: kamar kaya mai-nauyi sun fi ƙarfina.” (Zabura 38:4) Wasu Kiristoci sun yi baƙin ciki ainun har suka soma tunani cewa Jehobah ba zai taɓa gafarta musu zunubansu ba. (2 Korintiyawa 2:7) Shin hakan gaskiya ne? Ko da ka yi zunubai masu tsanani, hakan ba ya nufin cewa Jehobah ba zai taɓa yafe maka ba.

Ku Zo Mu Daidaita

Jehobah ba ya yin watsi da waɗanda suka yi zunubi. A maimakon haka, yana so ya shirya da su. A cikin almarar ɗa mubazzari, Yesu ya kwatanta Jehobah da Uba mai ƙauna da ɗansa ya bar gida kuma ya yi rayuwar banza. Daga baya, ɗan ya yanke shawara cewa zai koma gida. “Tun yana da nisa tukuna, ubansa ya hange shi, ya yi juyayi na tausayi, ya sheƙa a guje, ya faɗa ma wuyansa, ya yi ta yi masa sumba.” (Luka 15:11-20) Shin kana so ka kusaci Jehobah amma kana gani cewa kana da “nisa” daga inda yake? Jehobah yana kamar wannan Uba da Yesu ya ba da labarinsa kuma yana ƙaunarka. Yana so ka dawo gare shi.

Shin idan kana ganin kamar Jehobah ba zai yafe maka zunubanka ba don suna da yawa da kuma tsanani sosai fa? Ka yi la’akari da abin da Jehobah ya gaya wa mutanensa a littafin Ishaya: Ku “zo yanzu, mu yi bincike tare,” don yana so su daidaita. Ya daɗa da cewa: “Ko da zunubanku sun yi baƙi kamar mulufi, za su yi fari kamar kankara: ko da suna ja wur kamar garura, za su zama fari kamar auduga.” (Ishaya 1:18) Ko da zunubanka suna kamar garura da ta ɓata farin kaya, Jehobah zai yafe maka.

Jehobah ba ya son lamirinka ya riƙa damunka saboda laifin da ka yi. Mene ne za ka yi don Jehobah ya gafarce ka kuma ka sami kwanciyar hankali? Ka yi la’akari da wasu matakai biyu da Sarki Dauda ya ɗauka. Na farko, ya ce: ‘Zan faɗi laifofina ga Ubangiji.’ (Zabura 32:5) Ka tuna cewa Jehobah ya riga ya gaya maka cewa ka zo gare shi a cikin addu’a kuma ‘ku yi bincike tare,’ wato ku daidaita. Ka amince kuma ka yi addu’a. Ka gaya wa Jehobah zunubanka, kuma ka bayyana masa abin da ke zuciyarka. Abin da Dauda ya yi ke nan kuma ya roƙi Jehobah cewa: “Ka tsarkake ni daga zunubina. . . . karyayyar zuciya mai-tuba ba za ka rena ta ba, ya Allah.”—Zabura 51:2, 17.

Na biyu, Dauda ya amfana daga taimakon wani da Jehobah ya aika, wato annabi Nathan. (2 Sama’ila 12:13) A yau Jehobah ya tanadar da ƙwararrun ’yan’uwa maza, wato dattawan ikilisiya don su taimaka wa masu zunubi su sake ƙulla dangantaka da Jehobah. Idan ka je wurin dattawa, za su ƙarfafa ka da Littafi Mai Tsarki kuma za su roƙi Allah a madadinka. Hakan zai sa ka rage ko kuma ka daina tunanin cewa Jehobah ba zai yafe maka ba. Ƙari ga haka, za su taimaka maka ka soma bauta masa.—Yaƙub 5:14-16.

Jehobah yana so ka kasance da lamiri mai kyau kuma ka daina damuwa

“Mai Albarka Ne Mutum Wanda An Gafarta Masa Laifinsa”

A gaskiya, za ka iya ɗauka cewa gaya wa Jehobah zunubanka da kuma zuwa wurin dattawa jan aiki ne. Yanayin da Dauda ya sami kansa a ciki ke nan. Saboda haka, ya “yi shuru” na ɗan lokaci. (Zabura 32:3) Amma daga baya, ya gane cewa yin ikirari da kuma gyara halinsa yana da amfani sosai.

Ta yaya Dauda ya amfana? Ya sami kwanciyar hankali kuma ya ce: “Mai albarka ne mutum wanda an gafarta masa laifinsa, wanda an rufi zunubinsa.” (Zabura 32:1) Ya daɗa cewa: “Ka buɗe leɓunana, ya Ubangiji; Bakina kuwa za ya bayana yabonka.” (Zabura 51:15) Da yake Jehobah ya gafarta masa zunubansa kuma ya sami kwanciyar hankali, hakan ya motsa shi ya gaya wa mutane game da Jehobah.

Jehobah yana so ka kasance da lamiri mai kyau kuma ka daina damuwa. Ƙari ga haka, ba ya so ka yi fargaba yayin da kake sanar da mutane game da shi da kuma nufinsa. A maimakon haka, yana so ka yi hakan da zuciya ɗaya da kuma farin ciki. (Zabura 65:1-4) Ka tuna cewa ya gayyace ka zuwa wurinsa ‘domin a shafe zunubanka’ kuma ka sami “wartsakewa daga wurin Ubangiji.”—Ayyukan Manzanni 3:19.

Abin da ya faru da Martha ke nan. Ta ce: “Ɗana ya riƙa aika min mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Da sannu a hankali, sai na soma gyara dangantakata da Jehobah. Abin da ya fi min wuya shi ne gaya wa Jehobah dukan zunuban da na yi. Amma, a ƙarshe na yi addu’a kuma na roƙi Jehobah ya gafarta mini zunubaina. Na yi mamaki cewa shekaru 40 sun wuce kafin na komo ga Jehobah. Na fahimci cewa mutum zai iya sake bauta wa Jehobah kuma ya sami kwanciyar hankali ko da ya yi shekaru da yawa da barin ƙungiyar Jehobah.”