Bitar Sashe na 2
Ka tattauna tambayoyi na gaba da malaminka:
Mene ne Allah zai yi wa addinan ƙarya?
(Ka duba Darasi na 13.)
Ku karanta Fitowa 20:4-6.
Jehobah yana farin ciki ne sa’ad da mutane suka yi amfani da gumaka don su bauta masa? Me ya sa?
(Ka duba Darasi na 14.)
Wane ne Yesu?
(Ka duba Darasi na 15.)
Waɗanne halayen Yesu ne ka fi so?
(Ka duba Darasi na 17.)
Ku karanta Yohanna 13:34, 35 da Ayyukan Manzanni 5:42.
Su waye ne Kiristoci na gaske a yau? Me ya tabbatar maka cewa su ne Kiristoci na gaske?
(Ka duba Darasi na 18 da 19.)
Wane ne shugaba a ikilisiya, kuma ta yaya yake ja-goranci?
(Ka duba Darasi na 20.)
Ku karanta Matiyu 24:14.
Ta yaya annabcin nan yake cika a yau?
Su wane ne kake yi ma wa’azi?
(Ka duba Darasi na 21 da 22.)
Kana ganin yin baftisma maƙasudi ne da za ka iya cim ma? Me ya sa?
(Ka duba Darasi na 23.)
Ta yaya za ka iya kāre kanka daga Shaiɗan da aljannunsa?
(Ka duba Darasi na 24.)
Me ya sa Allah ya halicce mu?
(Ka duba Darasi na 25.)
Me ya sa mutane suke shan wahala da kuma mutuwa?
(Ka duba Darasi na 26.)
Ku karanta Yohanna 3:16.
Mene ne Jehobah ya yi don ya cece mu daga zunubi da kuma mutuwa?
(Ka duba Darasi na 27.)
Ku karanta Mai-Wa’azi 9:5.
Me ke faruwa da mutum sa’ad da ya mutu?
Mene ne Yesu zai yi wa mutane da yawa da suka mutu?
(Ka duba Darasi na 29 da 30.)
Ta yaya Mulkin Allah ya fi dukan gwamnatocin ’yan Adam?
(Ka duba Darasi na 31 da 33.)
Ka amince cewa Mulkin Allah yana sarauta yanzu? Me ya sa? Yaushe ne ya soma sarauta?
(Ka duba Darasi na 32.)