DARASI NA 55
Ka Taimaka a Ikilisiyarku
A faɗin duniya, miliyoyin mutane suna bauta wa Jehobah a ikilisiyoyi da yawa. Suna farin ciki don umurni da ja-gorancin da ake musu, kuma suna taimakawa a ikilisiya a hanyoyi da yawa. Haka ne kake ji game da ikilisiyarku?
1. A waɗanne hanyoyi ne za ka yi amfani da lokacinka da kuzarinka don ka taimaka a ikilisiyarku?
Dukanmu za mu iya taimakawa a ikilisiya. Alal misali, akwai wasu a ikilisiyarku da suka tsufa ko suke rashin lafiya? Za ka iya taimaka musu su halarci taro? Ko za ka iya taimaka musu yin wasu abubuwa, kamar yin cefane ko kuma aikace-aikacen gida? (Karanta Yakub 1:27.) Za mu kuma iya taimakawa wajen share Majami’ar Mulki da kuma yin gyare-gyare. Ba wanda yake tilasta mana yin waɗannan abubuwa. Amma ƙaunarmu ga Jehobah da ’yan’uwanmu ne take sa mu yi waɗannan abubuwan da “yardan rai.”—Zabura 110:3.
Shaidu da suka yi baftisma suna iya taimakawa a ikilisiya a wasu hanyoyi kuma. ’Yan’uwa maza da suka cancanta za su iya zama bayi masu hidima kuma da shigewar lokaci, su zama dattawa. ’Yan’uwa maza da mata za su iya yin wa’azi a matsayin majagaba. Wasu Shaidu suna iya taimaka wajen gina wuraren ibada ko kuma su ƙaura zuwa wata ikilisiya da ke bukatar taimako.
2. Ta yaya za mu yi amfani da dukiyarmu don mu taimaka wa ’yan’uwa?
Za mu iya “girmama Yahweh da abin da” muke da shi. (Karin Magana 3:9) Muna farin cikin ba da gudummawar kuɗi ko wasu abubuwa don mu taimaka wa ikilisiyoyinmu da kuma wa’azin da ake yi a faɗin duniya. (Karanta 2 Korintiyawa 9:7.) Ana amfani da gudummawarmu wajen taimaka wa ’yan’uwanmu da bala’i ya shafa. Mutane da yawa sun tsai da shawarar “ajiye wani abu” a kai a kai don su yi gudummawa da shi. (Karanta 1 Korintiyawa 16:2.) Za mu iya saka gudummawarmu a akwati da ke wurin ibadarmu ko kuma mu bayar ta intane a donate.jw.org. Jehobah yana ba mu dama mu nuna ƙaunarmu gare shi ta yadda muke amfani da abubuwan da muke da su.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu ga hanyoyin da mutum zai iya taimakawa a ikilisiya.
3. Za mu iya amfani da dukiyarmu
Jehobah da Yesu suna ƙaunar waɗanda suke bayarwa da farin ciki. Alal misali, Yesu ya yaba wa wata gwauruwa da ta ba da gudummawa duk da cewa abin da take da shi bai da yawa. Ku karanta Luka 21:1-4, sai ku tattauna tambayoyin nan:
-
Sai mun yi gudummawa da kuɗi da yawa ne za mu faranta wa Jehobah rai?
-
Yaya Jehobah da Yesu suke ji idan muka ba da gudummawa da son rai?
Don ka san yadda ake amfani da gudummawarmu, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku tattauna tambayar da ke gaba.
-
Ta yaya ikilisiyoyi a faɗin duniya suke amfana don gudummawar da muke yi?
4. Za mu iya taimakawa
A zamanin dā, bayin Jehobah sun yi aiki tuƙuru don su kula da wuraren ibadarsu. Don a cim ma wannan aikin, ba kawai gudummawar kuɗi ake bukata ba. Ku karanta 2 Tarihi 34:9-11, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Ta yaya kowane Ba’isra’ile ya taimaka wajen kula da wurin ibada?
Don ka ga yadda Shaidun Jehobah suke bin misalin bayin Allah na dā, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.
-
Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa tsabtace Majami’ar Mulkinmu kuma mu kula da ita?
-
A waɗanne hanyoyi ne za ka iya taimakawa?
5. ’Yan’uwa maza za su iya biɗan ƙarin aiki a ikilisiya
Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa ’yan’uwa maza su yi iya ƙoƙarinsu don su taimaka a ikilisiya. Don ku ga misalin yadda za su iya yin hakan, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku amsa tambayar da ke gaba.
-
A bidiyon, ta yaya Ryan ya nuna himma wajen taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya?
Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da ’yan’uwa maza za su iya yi don su zama bayi masu hidima da kuma dattawa. Ku karanta 1 Timoti 3:1-13, sai ku tattauna tambayoyin nan:
-
Mene ne ake so ’yan’uwa maza su yi idan suna so su zama bayi masu hidima da kuma dattawa?
-
Mene ne ake so iyalansu su yi?—Ka duba ayoyi na 4 da 11.
-
Idan ’yan’uwa maza suka yi ƙoƙari su cancanci yin hidimar nan, ta yaya kowa a ikilisiya zai amfana?
WANI YANA IYA CEWA: “Daga ina ne Shaidun Jehobah suke samun kuɗin gudanar da ayyukansu?”
-
Me za ka ce?
TAƘAITAWA
Jehobah yana farin ciki sosai a duk lokacin da muka yi amfani da lokacinmu da kuzarinmu da kuma dukiyarmu don mu taimaka a ikilisiya.
Bita
-
Ta yaya za mu yi amfani da lokacinmu da kuzarinmu don mu taimaka a ikilisiya?
-
Ta yaya za mu yi amfani da dukiyarmu don mu taimaka a ikilisiya?
-
A waɗanne hanyoyi ne za ka so ka taimaka a ikilisiya?
KA BINCIKA
Ku karanta talifin nan don ku san dalilin da ya sa Allah ya ce bayinsa su daina biyan zakka.
“Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Biyan Zakka?” (Talifin jw.org)
An ambata wasu ayyuka a Baibul da aka ba maza da suka yi baftisma. Amma me mace za ta yi idan tana so ta kula da ayyukan nan?
Yadda Za Mu Fahimci Shugabanci a Ikilisiya (Hasumiyar Tsaro, Fabrairu 2021)
Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wasu Shaidun Jehobah masu ƙarfin zuciya suke yin sadaukarwa sosai don su kai wa ’yan’uwansu da ke wasu wurare littattafai.
Yadda Ake Rarraba Littattafai da ke Bayyana Littafi Mai Tsarki a Kwango (4:25)
Ku karanta talifin nan don ku ga yadda muke samun kuɗin gudanar da ayyukanmu da ya bambanta da yadda sauran addinai suke yi.
“A Ina Shaidun Jehobah Suke Samun Kuɗin Yin Ayyukansu?” (Talifin jw.org)