Kammalawa
‘Ka zama mai-koyi da waɗanda ke gādan alkawarai ta wurin bangaskiya da haƙuri.’—IBRANIYAWA 6:12.
1, 2. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da bangaskiya yanzu? Ka kwatanta.
BANGASKIYA kalma ce mai daɗi da ke nufin hali mai kyau. Amma, idan muka ji wannan kalmar, za mu bukaci yin la’akari da wata kalma dabam, wato “Gaggawa!” Domin idan ba mu da bangaskiya, muna bukatar mu kasance da ita da gaggawa. Kuma idan muna da ita, muna bukatar mu kāre da kuma sa ta ci gaba da ƙarfi da gaggawa. Me ya sa?
2 A ce kana tafiya cikin wata babbar Hamada, kuma kana ƙishirwa sosai. Sai daga baya ka samu ruwa. Wajibi ne ka ajiye shi a wuri mai laima don kada rana ta shanye shi kuma za ka bukaci ka riƙa cika gorar ruwan don kada ya ƙare kafin ka isa inda za ka. Duniyar da muke ciki a yau tana kamar hamada domin mutanen da ke cikinta ba sa son bauta wa Jehobah. Ana ƙarancin bangaskiya ta gaske, kamar ruwan da muka ambata ɗazun. Kuma muna bukatar mu riƙa kyautata ta kamar wannan ruwan domin kada ta bushe. Ba za mu iya kasance da dangantaka da Jehobah ba idan ba mu da bangaskiya, kamar yadda ba za mu rayu ba idan ba mu sha ruwa ba.—Rom. 1:17.
3. Wane tanadi ne Jehobah ya yi mana don mu kasance da bangaskiya, kuma waɗanne abubuwa biyu ne ya kamata mu tuna da su?
3 Jehobah ya san cewa muna bukatar bangaskiya da gaggawa, kuma ya san cewa nuna bangaskiya da kuma ci gaba da yin hakan yana da wuya a yau. Babu shakka, shi ya sa ya tanadar mana da misalan mutanen da za mu iya yin koyi da su. Jehobah ya hure manzo Bulus ya ce: ‘Ku zama masu-koyi da waɗanda ke gādan alkawarai ta wurin bangaskiya da haƙuri.’ (Ibran. 6:12) Shi ya sa ƙungiyar Jehobah take ƙarfafa mu mu yi ƙoƙari don yin koyi da maza da mata masu imani, kamar waɗanda muka ambata a wannan littafin. Me ya kamata mu yi yanzu? Ya dace mu tuna da abubuwa biyu: Na ɗaya, muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu. Na biyu kuma, muna bukatar mu tuna da begenmu.
4. Ta yaya Shaiɗan ya nuna cewa ba ya son bangaskiya, amma me ya sa bai kamata mu yi sanyin gwiwa ba?
4 Ka ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarka. Shaiɗan ba ya son mutane su kasance da bangaskiya. Da yake shi ne mai mulkin duniyar nan, ya mayar da ita kamar hamada da ake wuyar samun bangaskiya. Ya fi mu ƙarfi sosai. Shin ya kamata mu ji tsoro cewa ba za mu iya kasance da bangaskiya ba da kuma ci gaba da yin hakan? Ko kaɗan! Jehobah yana ƙaunar dukan waɗanda suke da bangaskiya ta gaske. Ya tabbatar mana cewa tun da yana tare da mu, za mu iya yin tsayayya da Iblis kuma mu kore shi daga wurin mu! (Yaƙ. 4:7) Muna yin tsayayya da Iblis ta wajen ƙarfafa bangaskiyarmu kullum. Ta yaya za mu iya yin hakan?
5. Ta yaya maza da mata masu aminci na Littafi Mai Tsarki suka kasance da bangaskiya? Ka bayyana.
5 Kamar yadda muka koya, ba a haifi waɗannan maza da mata masu bangaskiya da wannan halin ba amma sun koyi kasancewa da shi ne. Sun nuna cewa bangaskiya ’yar ruhu mai tsarki na Jehobah ne. (Gal. 5:22, 23) Sun yi addu’a ga Jehobah ya taimake su kuma ya ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarsu. Ya dace mu yi koyi da su kuma kada mu taɓa manta cewa Jehobah yana ba da ruhunsa a yalwace ga waɗanda suke bukata kuma suka yi ayyukan da suka jitu da addu’o’insu. (Luk 11:13) Shin akwai ƙarin abubuwan da za mu iya yi kuwa?
6. Me ya kamata mu yi don mu amfana sosai daga yin nazari game da mutanen da aka ambata a Littafi Mai Tsarki?
6 A cikin wannan littafin, mun tattauna ƙalilan cikin fitattun mutane masu bangaskiya. Amma akwai wasu masu ɗimbin yawa da ba mu tattauna ba! (Karanta Ibraniyawa 11:32.) Kowanne cikin waɗannan maza da mata sun kafa mana misali mai kyau sosai. Ya kamata mu yi addu’a yayin da muke nazari a kan misalansu. Idan ba ma mai da hankali sosai sa’ad da muke nazari game da waɗannan mutane masu bangaskiya, ba za mu amfana ba sosai. Idan muna so mu amfana sosai sa’ad da muke karatu, ya kamata mu kwashi lokaci sosai muna yin bincike a kan tarihin mutumin da ake magana a kai. Idan muna yawan tuna cewa waɗannan maza da mata ajizai ne kuma suna da “tabi’a kamar tamu,” za mu fi amfana daga misalansu. (Yaƙ. 5:17) Za mu ji tausayinsu sa’ad da muke bimbini a kan ƙalubalen da suka fuskanta da ya yi kama da namu a yau.
7-9. (a) Kana ganin da yaya maza da mata masu bangaskiya na zamanin dā za su ji da a ce an umurce su su bauta wa Jehobah yadda muke yi a yau? (b) Me ya sa ya kamata mu ƙarfafa bangaskiyarmu ta ayyukanmu?
7 Muna kuma ƙarfafa bangaskiyarmu ta ayyukanmu. Ballantana ma, “bangaskiya ba tare da ayyuka [ba] matacciya ce.” (Yaƙ. 2:26) Ka yi la’akari da yadda waɗannan maza da mata masu aminci za su yi farin ciki da a ce Jehobah ya ce su yi irin aikin da muke yi a yau!
8 Alal misali, kana ganin da yaya Ibrahim zai ji da a ce an gaya masa cewa zai iya bauta wa Jehobah a Majami’un Mulki da majami’ar manya-manyan taro inda ake tattauna cikar alkawuran da aka yi masa dalla-dalla, amma ba a bagadin da ya gina a cikin jeji da duwatsu ba? (Karanta Ibraniyawa 11:13.) Ko kuma a ce an gaya wa Iliya cewa aikinsa ba na hukunta annabawan Baal ba ne yayin da yake ƙoƙarin ya bauta wa Jehobah a lokacin sarautar sarki mai ridda, amma na yi wa mutane wa’azin ta’aziya da bege ne. Babu shakka, da sun karɓi gatan bauta wa Jehobah da hannu bibbiyu yadda muke yi a yau.
9 Saboda haka, ya dace mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu ta ayyukanmu. Yayin da muke yin hakan, za mu nuna cewa muna yin koyi da misalan maza da mata masu bangaskiya
da aka ambata a cikin hurarriyar Kalmar Allah. Kamar yadda muka ambata a gabatarwar wannan littafin, za mu ɗauke su kamar abokanmu kuma wannan abokantakar za ta daɗa danƙo sosai.10. Mene ne zai sa mu yi farin ciki a Aljanna?
10 Ka tuna da begen da muke da shi. Bege ya ƙarfafa maza da mata masu bangaskiya na zamanin dā. Kai kuma fa? Alal misali, ka yi la’akari da yadda murna za ta cika ko’ina sa’ad da Allah ya ta da amintattun bayinsa a ‘tashin matattu na masu-adalci.’ (Karanta Ayyukan Manzanni 24:15.) Idan ka haɗu da su a nan gaba, waɗanne tambayoyi ne za ka so ka yi musu?
11, 12. Waɗanne tambayoyi ne za ka so ka yi wa (a) Habila? (b) Nuhu? (c) Ibrahim? (d) Ruth? (e) Abigail? (f) Esther?
11 Idan ka haɗu da Habila, za ka so ka tambaye shi yadda iyayensa suke a dā? Ko kuwa za ka tambaye shi: “Ka taɓa yin magana da waɗannan Charubim da suka tare hanyar shigan gonar Adnin? Sun amsa ka kuwa?” Nuhu kuma fa? Za ka iya tambayar sa: “Ka taɓa jin tsoron Kattan kuwa? Ta yaya ka kula da dukan waɗannan dabbobi a cikin jirgin har fiye da shekara guda?” Idan ka haɗu da Ibrahim, za ka iya tambayar sa: “Ka haɗu da Shem kuwa? Wane ne ya koyar da kai game da Jehobah? Shin barin birnin Ur ya yi maka wuya kuwa?”
12 Hakazalika, ka yi la’akari da wasu tambayoyin da wataƙila za ka so ka yi wa amintattun matan da aka ta da daga matattu. “Ruth, mene ne ya motsa ki ki soma bauta wa Jehobah?” “Abigail, kin ji tsoron gaya wa maigidanki Nabal yadda kika taimaka wa Dauda kuwa?” “Esther, me ya faru da ke da Mordekai, bayan an kammala labarinku a cikin Littafi Mai Tsarki?”
13. (a) Waɗanne tambayoyi ne wataƙila waɗanda suka tashi daga matattu za su yi maka? (b) Yaya kake ji domin za ka haɗu da amintattun maza da mata na zamanin dā a nan gaba?
13 Babu shakka, waɗannan maza da mata masu aminci ma suna da tambayoyi da za su yi maka. Za ka yi farin cikin gaya musu abin da ya faru a kwanaki na ƙarshe da kuma yadda Jehobah ya albarkace bayinsa a waɗannan kwanakin! Babu shakka, za su yi murnar ji cewa Jehobah ya cika dukan alkawuransa. A nan gaba a cikin sabuwar duniya, ba za mu riƙa yin ƙoƙarin yin bimbini a kan maza da mata masu aminci da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki ba. Me ya sa? Domin za su kasance tare da mu a cikin Aljanna! Saboda haka, ka ƙoƙarta yanzu don ka san waɗannan mutanen sosai. Ka ci gaba da yin koyi da bangaskiyarsu. Muna fatan cewa za ka ji daɗin bauta wa Jehobah tare da su a matsayin aminai har abadan abadin!