SASHE NA 2
Ta Yaya Za Ka Koyi Gaskiya Game da Allah?
1, 2. Wane misali ne ya nuna ana bukatar mizani domin magance batun addinai?
TA YAYA za mu zo ga sanin Allah? Wajibi ne mu bincika dukan koyarwa na waɗannan addinai da yawa? Hakan ba zai ma yiwu ba. Idan ma za mu iya yin haka, ta yaya za mu san wace koyarwa ce take daidai?
2 Babu shakka, domin ra’ayoyi dabam dabam game da Allah, muna bukatar hanyar sanin abin da ke gaskiya, mizani da mutane za su yarda da shi. Alal misali: A ce ana musu a kasuwa game da tsawon wani yadi. Ɗan kasuwa ya ce yadin yadi uku ne, amma mai ciniki yana ganin bai kai ba. Ta yaya za a magance batun? Ta wajen gwada yadin da ma’auni.
3. Me ya sa aka rubuta Littafi Mai Tsarki?
3 Shin da akwai ma’auni ne, mizani, domin magance batutuwan addini? Hakika, Littafi Mai Tsarki. Allah ya sa an rubuta Littafi Mai Tsarki domin mutane a ko’ina su samu su koyi gaskiya game da shi. An buga biliyoyinsa. An fassara shi, gaba ɗayansa ko kuma rabinsa, cikin fiye da harsuna 2,100. Kusan kowa zai iya karanta gaskiya game da Allah a nasa ko nata harshen.
4. Wane bayani yake cikin Littafi Mai Tsarki?
4 Littafi Mai Tsarki kyauta ce mai tamani daga Allah. Ya yi bayani game da abubuwa da idan ba dominsa ba da ba za mu taɓa sani ba. Ya faɗi game da waɗanda suke zama a duniya ta ruhu. Ya bayyana tunanin Allah, da mutuntakarsa da kuma nufinsa. Ya faɗi game da yadda ya
bi da mutane a cikin shekaru dubbai. Ya yi maganar abubuwa da za su faru a nan gaba. Kuma ya nuna yadda za mu sami hanyar rai na har abada.Abin da Ya Sa Za Ka Gaskata Littafi Mai Tsarki
5. Wane misali ya nuna cewa Littafi Mai Tsarki ya jitu da kimiyya?
5 Da akwai dalilai da yawa da suka sa za mu gaskata cewa Littafi Mai Tsarki da gaske Kalmar Allah ce. Dalili ɗaya shi ne cewa Littafi Mai Tsarki ya jitu da kimiyya. A dā, mutane a dukan duniya sun yi tsammanin cewa duniya tana kan wani abu ne. Alal misali, a Afirka ta Yamma, mutane sun taɓa gaskata cewa duniya tana tsakiyar wani naɗaɗɗen maciji ne, mai naɗi 3,500 a bisa duniyar da kuma naɗi 3,500 a ƙarƙashinta. Duk da haka, cikin jituwa da kimiyya, marubucin Littafi Mai Tsarki ya rubuta fiye da shekara 3,500 da ta shuɗe cewa Allah “ya ratayi duniya ba komi ƙarƙashinta.”—Ayuba 26:7.
6. Menene tabbaci mafi ƙarfi cewa Littafi Mai Tsarki daga Allah ne?
6 Tabbaci mafi ƙarfi cewa Littafi Mai Tsarki da gaske daga Allah ne, shi ne abin da aka sani ya faɗa game da abin da zai faru a nan gaba. Ba kamar malaman duba ba, Allah hakika ya san abin da zai faru a nan gaba; duk abin da ya ce ko da yaushe yana kasancewa gaskiya.
7. Waɗanne ne annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki da suka cika a dā?
7 Ɗarurruwan annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki sun cika a zamanin dā. Alal misali, shekara 700 kafin haihuwarsa, Littafi Mai Tsarki ya ce za a haifi Yesu a birnin Bai’talahmi, kuma hakan ya faru. (Mikah 5:2; Matta 2:3-9) Ƙari ga wasu annabce-annabce game da Yesu, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa budurwa ce za ta haife shi kuma a ƙarshe za a ci amanarsa domin azurfa talatin. Waɗannan annabce-annabce ma sun kasance gaskiya. Hakika babu mutumin da zai iya annabta waɗannan abubuwa!—Ishaya 7:14; Zakariya 11:12, 13; Matta 1:22, 23; 27:3-5.
8. Waɗanne ne annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki da suka cika a yau, kuma me suka tabbatar?
8 Annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki
da yawa sun cika a zamaninmu. Ga kaɗan daga cikinsu:-
“Al’umma za ta tasam ma al’umma, mulki kuwa za ya tasam ma mulki: za a yi manyan rayerayen duniya, wuri dabam dabam kuma yunwa da annoba.”—Luka 21:10, 11.
-
‘Mugunta za ta yawaita.’—Matta 24:12.
-
“Cikin kwanaki na ƙarshe . . . mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, . . . marasa-bin iyaye, . . . marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, . . . masu-kumbura, ma-fiya son annashuwa da Allah.”—2 Timotawus 3:1-5.
Ka yarda cewa waɗannan abubuwa suna faruwa a yau? Gaskiya da kuma hakikancin annabci na Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa ba littafi ba ne kawai. Hurarriyar Kalmar Allah ce!—2 Timotawus 3:16.
An Canja Littafi Mai Tsarki Ne?
9, 10. Me ya nuna cewa Allah bai ƙyale mutane su canja Littafi Mai Tsarki ba?
9 A ce kana da masana’anta kuma ka kafa jerin dokoki a jikin bango ga ma’aikatanka. Idan wasu abokan gāba suka canja abin da ka rubuta, me za ka yi? Ba za ka gyara abin da aka canja ba? Hakanan, Allah bai ƙyale mutane su canja gaskiya da take cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki ba.
10 Waɗanda suka yi ƙoƙari su canja Kalmar Allah ba su yi nasara ba. Idan muka gwada Littafi Mai Tsarki da muke da shi a yau da Littafi Mai Tsarki na dā, babu bambanci. Wannan ya nuna cewa Littafi Mai Tsarki bai canja ba da shigewar lokaci.