DARASI NA 48
Yaron Wata Gwauruwa Ya Tashi Daga Mutuwa
Sa’ad da ba a yi ruwan sama a ƙasar ba, Jehobah ya ce wa Iliya: ‘Ka je Zarefat. Akwai wata mata a wurin da za ta ba ka abinci.’ Iliya ya ga wata mata a bakin ƙofar birnin tana tattara itace. Sai ya ce ta ba shi ruwa ya sha. Da ta je kawo masa ruwa, sai Iliya ya ƙara ce mata: ‘Don Allah ki kawo mini gurasa.’ Amma gwauruwar ta ce: ‘Ba ni da wata gurasa da zan iya ba ka. Fulawa da māi da zai ishe ni da kuma ɗana ne kawai nake da shi.’ Sai Iliya ya ce mata: ‘Jehobah ya yi alkawari cewa idan kika yi mini gurasa, fulawarki da mānki ba za su ƙare ba har sai an soma ruwan sama.’
Sai gwauruwar ta je gida kuma ta yi wa annabin Jehobah gurasa. Kamar yadda Jehobah ya yi alkawari, wannan gwauruwar da ɗanta ba su rasa abinci ba a lokacin da ba a yi ruwan sama ba. Fulawarta da mānta ba su ƙare ba.
Amma wani mummunan abu ya faru. Yaron gwauruwar ya yi rashin lafiya kuma ya mutu. Sai ta roƙi Iliya ya taimaka mata. Iliya
ya karɓi yaron daga hannunta kuma ya kai shi wani ɗaki a saman gidanta. Ya ajiye shi a kan gado kuma ya yi addu’a: ‘Ya Jehobah, ina roƙonka ka tayar da yaron nan daga mutuwa.’ Ka san dalilin da ya sa tayar da wannan yaron zai zama abu na musamman? Domin a lokacin, babu wanda aka taɓa tayar daga mutuwa. Kuma wannan gwauruwar da yaronta ba Isra’ilawa ba ne.Jehobah ya tayar da yaron daga mutuwa! Sai Iliya ya ce wa gwauruwar: ‘Ki ga, ɗanki yana da rai.’ Ta yi farin ciki sosai kuma ta ce wa Iliya: ‘Babu shakka, kai mutumin Allah ne. Na san da hakan domin abin da Jehobah ya gaya maka kawai kake faɗa.’
“Ku dubi dai hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah yana cishe su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!”—Luka 12:24, Littafi Mai Tsarki