Gabatarwar Sashe na 6
Sa’ad da Isra’ilawa suka isa Ƙasar Alkawari, mazauni ne ya zama wurin da za su riƙa bauta wa Jehobah. Firistoci ne suke koya musu dokar Allah, alƙalai kuma ne suke musu ja-gorancin. Wannan sashen ya nuna yadda abin da mutum ya yi yake shafen mutane. Kowane mutum a cikinsu yana bukatar ya kasance da aminci ga Jehobah da kuma ɗan’uwansa. Ka ambata yadda halayen Deborah da Naomi da Joshua da Hannatu da ’yar Jephthah da kuma Sama’ila suka shafi mutane a zamaninsu. Ka nanata yadda Rahab da Ruth da Jael da kuma Gibeyonawa suka haɗa kai da Isra’ilawa don sun san cewa Allah yana tare da su duk da cewa su ba Isra’ilawa ba ne.
A WANNAN SASHEN
DARASI NA 30
Rahab Ta Boye ʼYan Leken Asiri
Katangar Yariko ta rushe gabaki daya. Amma gidan Rahab bai rushe ba duk da cewa gidan hade yake da katangar.
DARASI NA 31
Joshua da Gibeyonawa
Joshua ya roki Allah: “Rana ta tsaya cak!” Shin Allah ya amsa wannan addu’ar?
DARASI NA 32
Sabon Shugaba da Mata Biyu Masu Karfin Zuciya
Isra’ilawa sun soma bautar gumaka bayan Joshua ya mutu. Sun sha wahala sosai. Amma Jehobah ya yi amfani da Alkali Barak da annabiya Deborah da kuma Jael don ya cece su!
DARASI NA 33
Ruth da Naomi
Wadannan mata biyu da mazansu sun rasu sun koma Isra’ila. Daya daga cikinsu mai suna Ruth ta je aiki a wani gona. A gonar ce Boaz ya hadu da ita.
DARASI NA 34
Gidiyon Ya Ci Midiyanawa da Yaki
Isra’ilawa sun roki Jehobah ya taimaka musu bayan Midiyanawa sun wahalar da su sosai. Ta yaya sojojin Gidiyon guda 300 suka ci sojojin Midiyanawa guda 135,000 a yaki?
DARASI NA 35
Hannatu Ta Roki Allah Ya Ba Ta Yaro
Elkanah ya kai Hannatu da Peninnah, da kuma yaransa bauta a mazaunin da ke Shiloh. A nan ne Hannatu ta roki Allah ya ba ta yaro. An haifi Sama’ila bayan shekara daya!
DARASI NA 36
Alkawarin da Jephthah Ya Yi
Wane alkawari ne Jephthah ya yi, kuma me ya sa? Ta yaya ʼyar Jephthah ta ji don alkawarin da babanta ya yi?
DARASI NA 37
Jehobah Ya Yi Magana da Sama’ila
Yaran Eli Babban Firist guda biyu suna hidima a mazaunin, amma ba su yi biyayya ga dokokin Allah ba. Sama’ilawa wanda shi matashi ne bai bi halinsu ba, kuma Jehobah ya yi masa magana.
DARASI NA 38
Jehobah Ya Ba Samson Karfi
Allah ya sa Samson karfi sosai domin ya rika yaki da Filistiyawa. Amma sa’ad da ya yanke shawara marar kyau, Filistiyawa sun kama shi.