DARASI NA 18
Bishiya Mai Cin Wuta
Musa ya yi shekara 40 a ƙasar Midiya. Ya yi aure kuma ya haifi yara. Wata rana sa’ad da yake kiwon tumakinsa kusa da Dutsen Sinai, sai ya ga wani abin mamaki. Ya ga wata bishiya tana cin wuta amma ba ta ƙone ba. Sa’ad da Musa ya je kusa don ya ga abin da ya sa, sai ya ji wata murya ta ce: ‘Musa! Kada ka zo kusa. Ka cire takalmanka domin kana tsaye a wuri mai tsarki.’ Jehobah ne ya yi amfani da mala’ika don ya yi masa magana.
Musa ya ji tsoro sai ya rufe fuskarsa. Muryar ta ci gaba da cewa: ‘Na ga irin wahalar da Isra’ilawa suke sha. Zan cece su daga ƙasar Masar kuma zan kawo su cikin wata ƙasa mai kyau. Kai ne za ka yi musu ja-gora daga ƙasar Masar.’ Hakan ya ba Musa mamaki, ko ba haka ba?
Musa ya yi tambaya, ya ce: ‘Me zan faɗa idan mutanen suka ce wane ne ya aiko ni?’ Sai Allah ya ce: ‘Ka gaya musu cewa Jehobah, Allahn Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yakubu ne ya aiko ka.’ Musa ya ce: ‘Idan mutanen ba su yarda ba fa?’ Sai Jehobah ya yi wani abu da ya sa Musa ya tabbatar da cewa zai taimaka masa. Ya ce Musa ya jefa sandar da ke hannunsa a ƙasa. Sai sandar ta zama maciji. Sa’ad da Musa ya riƙe wutsiyar macijin, sai ya sake zama sanda. Jehobah ya ce: ‘Idan ka yi wannan abin mamaki, za su san cewa ni na aiko ka.’
Musa ya ce: ‘Ban iya magana ba sosai.’ Sai Jehobah ya yi masa alkawari cewa: ‘Zan gaya maka abin da za ka ce, kuma zan sa ɗan’uwanka Haruna ya taimaka maka.’ Da yake Musa ya san cewa Jehobah yana tare da shi, sai shi da matarsa da kuma yaransa suka koma ƙasar Masar.
“Kada hankalinku ya tashi a kan irin magana da za ku yi, ko kuwa abin da za ku faɗi: gama a cikin saʼan nan za a ba ku abin da za ku faɗi.”—Matta 10:19