DARASI NA 93
Yesu Ya Koma Sama
Yesu ya haɗu da almajiransa a Galili. Ya ba su wani aiki mai muhimmanci kuma ya ce: ‘Ku je ku yi wa dukan mutane a faɗin duniya wa’azi. Ku koya musu abubuwan da na koya muku kuma ku yi musu baftisma.’ Sai ya yi musu alkawari cewa: ‘Ku tuna, ina nan tare da ku a koyaushe.’
A cikin kwanaki 40 bayan an ta da Yesu daga mutuwa, ya bayyana ga mabiyansa a Galili da kuma Urushalima. Ya koya musu abubuwa masu muhimmanci kuma ya yi mu’ujizai da yawa. Sai ya haɗu da su a lokaci na ƙarshe a Dutsen Zaitun. Yesu ya ce: ‘Kada ku bar Urushalima. Ku jira alkawarin da Ubana ya yi.’
Almajiransa ba su san abin da yake nufi ba. Sai suka ce masa: ‘Za ka zama Sarkin Isra’ilawa ne yanzu?’ Yesu ya ce: ‘Lokacin da ya kamata na zama Sarki bai kai ba tukun. Ba da daɗewa ba, za a aiko muku da ruhu mai tsarki kuma za ku soma wa’azi game da ni. Ku je ku yi wa’azi a Urushalima da Yahuda da Samariya da kuma dukan duniya.’
Sai Yesu ya koma sama. Almajiransa sun duba sama ko za su gan shi amma ba su gan shi ba.
Almajiransa sun bar Dutsen Zaitun kuma suka tafi Urushalima. Suna yawan haɗuwa a wani babban ɗaki don su yi addu’a. Suna jiran Yesu ya gaya musu abin da za su yi.
“Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’an nan matuƙa za ta zo.”—Matta 24:14