Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 86

Yesu Ya Tayar da Li’azaru Daga Matattu

Yesu Ya Tayar da Li’azaru Daga Matattu

Yesu yana da wasu abokai uku da suke zama a garin Bait’anya. Sunayensu Li’azaru da Maryamu da kuma Martha. Dukansu ’yan’uwa ne. Wata rana da Yesu yake wani gari da ke hayin kogin Urdun, sai Maryamu da Martha suka aika wa Yesu saƙo cewa: ‘Li’azaru bai da lafiya. Don Allah, ka zo da sauri!’ Amma Yesu bai je wurin da sauri ba, ya ƙara kwana biyu a wurin. Bayan haka, ya ce wa almajiransa: ‘Mu je Bait’anya. Li’azaru yana barci, zan je in tashe shi.’ Sai almajiran suka ce: ‘Idan Li’azaru yana barci, hakan zai taimaka masa ya warke.’ Yesu ya gaya musu kai tsaye: ‘Li’azaru ya mutu.’

Yesu ya isa Bait’anya bayan an yi kwana huɗu da binne Li’azaru. Mutane da yawa sun zo su yi wa Martha da Maryamu ta’aziya. Da Martha ta ji cewa Yesu ya iso, sai ta je wajensa da sauri. Ta ce: “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.” Amma Yesu ya ce mata: ‘Ɗan’uwanki zai sake rayuwa. Martha, kin yi imani da haka?’ Sai ta ce: ‘Na yi imani cewa zai tashi a ranar da za a tayar da matattu.’ Yesu ya ce mata: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai.”

Sai Martha ta koma ta gaya wa Maryamu cewa: ‘Yesu ya zo.’ Da ta ji haka, sai ta fita a guje, kuma mutanen suka bi ta. Sai ta faɗi a ƙafafunsa, tana kuka. Ta ce: ‘Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwanmu bai mutu ba!’ Da Yesu ya ga irin baƙin cikin da take yi, sai shi ma ya soma kuka. Sa’ad da mutanen suka ga yadda Yesu yake kuka, sai suka ce: ‘Dubi yadda yake ƙaunar Li’azaru.’ Amma wasu suka yi mamaki cewa: ‘Me ya sa bai taimaka wa abokinsa ba?’ Ka san abin da Yesu ya yi bayan haka?

Yesu ya je kabarin Li’azaru kuma an rufe ƙofar da babban dutse. Sai ya ce: ‘Ku cire dutsen.’ Martha ta ce: ‘Amma yanzu kwanansa huɗu ke nan da mutuwa! Gawarsa ta soma ɗoyi.’ Duk da haka, sun cire dutsen. Yesu ya yi addu’a, ya ce: ‘Ya Uba, na gode da ka ji ni. Na san cewa kullum kana ji na. Amma ina roƙo domin mutanen nan su san cewa kai ne ka aiko ni.’ Sai ya kira da babbar murya: “Li’azaru, ka fito!” Wani abin mamaki ya faru. Li’azaru ya fito daga kabarin, kuma yana ɗaure da zanen da aka binne shi da shi. Yesu ya ce: ‘Ku kwance shi, ya tafi.’

Hakan ya sa mutane da yawa sun yi imani da Yesu. Amma wasu suka je suka gaya wa Farisawa. Daga ranar, Farisawan suka soma neman su kashe Li’azaru da kuma Yesu. Sai wani cikin manzannin Yesu mai suna Yahuda Iskariyoti, ya je wajen Farisawan a ɓoye. Ya ce musu: ‘Nawa za ku biya ni idan na nuna muku wurin da za ku ga Yesu?’ Suka ce za su biya shi kuɗin azurfa 30. Sai Yahuda ya soma neman zarafin da ya dace don Farisawan su kama Yesu.

“Allah a garemu Allah mai-yawan ceto ne; makuɓutan mutuwa kuma suna ga Yahweh Ubangiji.”​—Zabura 68:20