DARASI NA 14
Me Ya Sa Allah Yake da Ƙungiya?
1. Me ya sa Allah ya zaɓi Isra’ilawa ta dā su zama mutanensa?
Allah ya kafa zuriyar Ibrahim ta zama al’umma kuma ya ba ta dokoki. Ya ba al’ummar suna Isra’ila kuma ya ɗora mata nauyin kāre bauta ta gaskiya da kuma kalmarsa. (Zabura 147:19, 20) Hakan ya sa mutane daga dukan al’ummai suka amfana daga al’ummar Isra’ila.—Karanta Farawa 22:18.
Allah ya zaɓi Isra’ilawa su zama shaidunsa. Sa’ad da suka yi biyayya, sun amfana daga dokokin Allah. (Kubawar Shari’a 4:6) Ta wajen sanin Isra’ilawa na dā, mutane za su san Allah na gaskiya.—Karanta Ishaya 43:10, 12.
2. Me ya sa Allah yake son bayinsa a yau su kasance da haɗin kai?
Bayan wani lokaci, Isra’ila ta juya wa Allah baya, kuma Jehobah ya sauya al’ummar da ikilisiyar Kirista. (Matta 21:43; 23:37, 38) A dā, Isra’ilawa shaidun Jehobah ne. Amma, yanzu Kiristoci na gaskiya ne suka zama shaidun Jehobah.—Karanta Ayyukan Manzanni 15:14, 17.
Yesu ya koya wa mabiyansa su yi wa’azi game da Jehobah kuma su yi almajirai a dukan al’ummai. (Matta 10:7, 11; 24:14; 28:19, 20) An kusan kammala wannan aikin yanzu, a wannan kwanaki na ƙarshe. Wannan shi ne lokaci na farko da Jehobah ya sa miliyoyin mutane daga dukan ƙasashen duniya su kasance da haɗin kai a bauta ta gaskiya. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10) Kiristoci na gaskiya suna cikin ƙungiya ɗaya kuma suna ƙarfafa juna da kuma taimaka wa juna. A faɗin duniya, suna bin tsari guda wajen koyar da umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki a taronsu.—Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.
3. Ta yaya ƙungiyar Shaidun Jehobah ta zamani ta soma?
Somawa daga shekara ta 1870, wani ƙaramin rukuni na ɗaliban Littafi Mai Tsarki ya soma gano gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki wadda aka daina koyarwa tun da daɗewa. Sun san cewa Yesu ya umurci waɗanda ke cikin ikilisiyar Kirista su yi wa’azi. Hakan ya sa suka soma yin wa’azin Mulki a dukan ƙasashen duniya. Sun soma amsa sunan nan Shaidun Jehobah ne a shekara ta 1931.—Karanta Ayyukan Manzanni 1:8; 2:1, 4; 5:42.
4. Ta yaya Shaidun Jehobah suke gudanar da ayyukansu na wa’azi?
A ƙarni na farko, ikilisiyoyin Kirista a ƙasashe da dama sun amfana daga Hukumar Mulki da ke Urushalima wadda ta ɗauki Yesu a matsayin Shugaban ikilisiya. (Ayyukan Manzanni 16:4, 5) Hakazalika a yau, Shaidun Jehobah a dukan duniya suna samun ja-goranci daga Hukumar Mulki. Hukumar Mulki wani rukunin dattawa ne da suka ƙware sosai. Ana fassara da buga da kuma rarraba littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a harsuna fiye da 600 a ofisoshin reshe na Shaidun Jehobah. Hukumar Mulkin ce take tsara ayyukan da ake yi a waɗannan rassan. Ta hakan, tana ba da ƙarfafawa da kuma ja-gora daga Nassi ga ikilisiyoyi fiye da 100,000 a dukan duniya. A kowace ikilisiya, maza da suka ƙware suna hidima a matsayin dattawa ko masu kula. Waɗannan mazajen suna kula da tumakin Allah cikin ƙauna.—Karanta 1 Bitrus 5:2, 3.
Shaidun Jehobah suna yin wa’azi a ko’ina a duniya. Don mu taimaka wa mutane a ko’ina, muna wa’azi gida-gida, yadda manzannin Yesu suka yi. (Ayyukan Manzanni 20:20) Kuma muna yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutanen da ke son su koyi gaskiya. Shaidun Jehobah ba ƙungiya ba ce kawai. Muna kamar iyali ne da ke bauta wa Allah mai ƙauna. Mu ’yan’uwa ne da ke kula da juna. (2 Tasalonikawa 1:3) Tun da yake mutanen Jehobah sun mai da hankali ne ga faranta wa Allah rai da kuma taimaka wa mutane, su ne suka fi farin ciki a duniya.—Karanta Zabura 33:12; Ayyukan Manzanni 20:35.