LABARI NA 94
Yesu Yana Ƙaunar Yara Ƙanana
DUBI Yesu a nan ya riƙe yaron nan ƙarami. Za ka ga cewa Yesu yana ƙaunar yara ƙanana. Mutane da suke kallonsa manzanninsa ne. Menene Yesu yake gaya musu? Bari mu gani.
Ba da daɗewa ba Yesu da manzanninsa suka dawo daga wata tafiya mai nisa. A kan hanya manzanni suka yi musu a tsakaninsu. Daga baya Yesu ya tambaye su: ‘Menene kuke musu a kai a kan hanya?’ Hakika, Yesu ya san abin da suke musu a kai. Amma ya yi tambaya ne domin ya ga ko manzanni za su gaya masa.
Manzanni ba su amsa ba, domin a kan hanya sun yi musu game da wanda ya fi girma a tsakaninsu. Wasu manzanni suna so su fi wasu muhimmanci. Ta yaya Yesu zai gaya musu cewa ba daidai ba ne su nemi zama mutane da suka fi muhimmanci?
Ya kira yaron, ya tsayar da shi a gabansu duka. Sai ya ce wa almajiransa: ‘Ina so ku sani cewa, sai kun canja kun zama kamar wannan yaron, ba za ku shiga mulkin Allah ba. Babban mutum a mulkin shi ne wanda yake kama da wannan yaron.’ Ka san abin da ya sa Yesu ya faɗi haka?
Domin yara ƙanana ba sa damuwa da zama babba ko kuma masu muhimmanci fiye da wasu ba. Saboda haka manzanni dole ne su koyi su zama kamar yara ƙanana kuma kada su riƙa musu game da wanda ya fi girma ko kuma ya fi muhimmanci.
Da wani lokaci kuma, da Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar yara ƙanana. Bayan ’yan watanni wasu mutane suka kawo yaransu su ga Yesu. Manzanni suna so su hana su. Amma Yesu ya gaya wa manzanninsa: ‘Ku ƙyale yaran su zo gare ni, kada ku hana su, domin mulkin Allah ga mutane ne kamarsu.’ Sai Yesu ya rungumi yaran, ya kuma albarkace su. Yana da kyau da muka sani cewa Yesu yana ƙaunar yara ƙanana, ko ba haka ba?
Matta 18:1-4; 19:13-15; Markus 9:33-37; 10:13-16.