LABARI NA 16
Ishaku Ya Auri Matar Kirki
KA SAN ko wacece wannan matar da take hoton nan? Sunanta Rifkatu ne. Kuma wurin Ishaku take zuwa. Ta zama matarsa. Ta yaya haka ya faru?
Abin da ya faru shi ne, uban Ishaku Ibrahim yana son ɗansa ya sami matar kirki. Ba ya so Ishaku ya auri ɗaya daga cikin ’yan matan Kan’ana, domin mutanen suna bauta wa allolin ƙarya. Saboda haka, Ibrahim ya kira bawansa ya ce masa: ‘Ina so ka je inda ’yan’uwana suke a Haran ka auro mace wa ɗana Ishaku.’
A take bawan Ibrahim ya ɗauki raƙuma goma ya yi wannan doguwar tafiya. Da ya yi kusa da inda ’yan’uwan Ibrahim suke, ya tsaya a kusa da wata rijiya. La’asar ta yi a lokacin, lokaci ne da ’yan matan garin za su fito jan ruwa daga rijiya. Sai bawan Ibrahim ya yi wa Jehobah addu’a: ‘Duk matar da ta ba ni ruwa da kuma raƙuman nan ita ce ka zaɓa ta zama matar Ishaku.’
Ba da daɗewa ba Rifkatu ta zo jan ruwa. Da bawan ya roƙe ta ta ba shi ruwa, sai ta ba shi. Sai ta je ta ba da isashen ruwa ga raƙuman da suke da ƙishin ruwa. Wannan aiki ne mai wuya domin raƙuma suna shan ruwa da yawa.
Sa’ad da Rifkatu ta gama ba su ruwa, sai bawan Ibrahim ya tambaye ta sunan babanta. Ya kuma tambaya ko zai yiwu ya sami wurin kwana a gidansu. Ta ce: ‘Sunan babana Bethuel ne, kuma akwai masaukin da za ka sauka a gidanmu.’ Bawan Ibrahim ya sani cewa Bethuel ɗan Nahor ne ɗan’uwan Ibrahim. Sai ya durƙusa ya yi wa Jehobah godiya domin ya kawo shi ga ’yan’uwan Ibrahim.
A cikin daren bawan Ibrahim ya gaya wa Bethuel da wan Rifkatu Laban abin da ya kawo shi. Dukansu suka yarda Rifkatu ta bi shi ta auri Ishaku. Menene Rifkatu ta ce sa’ad da aka tambaye ta? Ta ce ‘E’ ta yarda za ta tafi. Saboda haka da gari ya waye suka hau raƙumansu suka fara doguwar tafiyarsu ta komawa Kan’ana.
Da suka isa, yamma ta riga ta yi. Rifkatu ta ga wani mutum yana tafiya a cikin gona. Ishaku ne. Ya yi farin ciki da ya ga Rifkatu. Da farko yana baƙin ciki domin mamarsa Saratu ta mutu shekara uku kafin zuwan ta. Amma yanzu Ishaku ya ƙaunaci Rifkatu ƙwarai, kuma ya fara farin ciki kuma.
Farawa 24:1-67.