Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 56

Saul, Sarkin Isra’ila Na Farko

Saul, Sarkin Isra’ila Na Farko

DUBI Sama’ila yana zuba mai a kan wannan mutumin. Abin da suke yi wa mutum ke nan su nuna cewa an zaɓe shi ya zama sarki. Jehobah ya gaya wa Sama’ila ya zuba mai a kan Saul. Mai ne na musamman mai ƙamshi.

Saul yana ganin bai cancanta ya zama sarki ba. ‘Na fito daga zuriyar Banyamin mafi-ƙanƙanta cikin dukan Isra’ila,’ ya gaya wa Sama’ila. ‘Me ya sa ka ce zan zama sarki?’ Jehobah yana son Saul domin bai nuna kamar shi babban mutum ko mutum mai muhimmanci ba ne. Abin da ya sa ke nan ya zaɓe shi ya zama sarki.

Amma Saul ba matalauci ba ne ko kuma mutum marar muhimmanci. Ya fito daga iyali mai arziki ne, kuma shi dogon mutum ne mai kyau. Ya fi kowa tsayi a Isra’ila! Saul yana da gudu, kuma mutum ne mai ƙarfi. Mutanen sun yi farin ciki da Jehobah ya zaɓi Saul ya zama sarki. Sai duka suka fara ihu suna cewa: ‘Ran sarki ya daɗe!’

Abokan gaba na Isra’ila suna da ƙarfinsu kamar dā. Har ila suna faɗa da Isra’ilawa kamar yadda suka saba. Ba da daɗewa ba bayan da aka naɗa Saul ya zama sarki, Ammonawa suka zo su yaƙe su. Amma Saul ya tara sojoji masu yawa, kuma ya ci nasara bisa Ammonawa. Wannan ya sa mutanen suka yi farin ciki domin Saul ne ya zama sarkinsu.

Da shigewar shekaru, Saul ya ja-goranci Isra’ila wajen nasarori masu yawa bisa abokan gabansu. Saul kuma yana da yaro marar tsoro Jonathan. Jonathan ya taimaki Isra’ila ta ci yaƙoƙi masu yawa. Har yanzu Filistiyawa su ne suka fi ƙiyayya da Isra’ila. Wata rana Filistiyawa masu dubun yawa suka zo su yaƙi Isra’ilawa.

Sama’ila ya gaya wa Saul ya jira har sai ya zo ya yi hadaya ko kuma ya ba da kyauta ga Jehobah. Amma Sama’ila yana jinkirin zuwa. Saul yana tsoron cewa Filistiyawa za su fara yaƙin, sai ya je ya yi hadayar da kansa. Sa’ad da Sama’ila ya zo, ya gaya wa Saul cewa ya yi rashin biyayya. Sama’ila ya ce: ‘Jehobah zai zaɓi wani mutum dabam ya zama sarkin Isra’ila.’

Daga baya Saul ya sake wani rashin biyayya. Saboda haka Sama’ila ya gaya masa: ‘Yi wa Jehobah biyayya ya fi ka ba shi kyautar tunkiya mai lafiya. Domin ka ƙi yi wa Jehobah biyayya, Jehobah ba zai ƙyale ka ka ci gaba da sarautar Isra’ila ba.’

Za mu iya koyon darasi mai kyau daga wannan. Ya nuna mana yadda yake da muhimmanci mu yi wa Jehobah biyayya kullum. Ya kuma nuna mana cewa mutumin kirki zai iya canja ya zama mugu. Ba ma so mu zama miyagun mutane, ko muna so ne?

1 Samuila surori 9 zuwa 11; 13:5-14;; 14:47-52; 15:1-35; 2 Samuila 1:23.