LABARI NA 43
Joshua Ya Zama Shugaba
MUSA yana so ya shiga ƙasar Kan’ana tare da Isra’ilawa. Saboda haka ya yi roƙo: ‘Ka bari mana in haye Kogin Urdun, Jehobah, domin in ɗan ga albarkar ƙasar.’ Amma Jehobah ya ce: ‘Ya ishe ka haka! Akul ka sake wannan maganar!’ Ka san abin da ya sa Jehobah ya faɗi haka?
Domin abin da ya faru ne sa’ad da Musa ya bugi dutse. Ka tuna, shi da Haruna ba su daraja Jehobah ba. Ba su gaya wa mutanen ba cewa Jehobah ne ya ba su ruwa daga dutsen. Domin wannan Jehobah ya ce ba zai ƙyale su su shiga ƙasar Kan’ana ba.
’Yan watanni bayan Haruna ya mutu, Jehobah ya gaya wa Musa: ‘Ka ɗauki Joshua, ka tsayar da shi a gaban Eleazar firist da kuma mutanen. Kuma a gaban su duka, ka gaya musu duka cewa Joshua ne sabon shugaba.’ Musa ya yi kamar yadda Jehobah ya ce, kamar yadda kake gani a wannan hoton.
Sai kuma Jehobah ya gaya wa Joshua: ‘Ka ƙarfafa, kada ka ji tsoro. Za ka ja-goranci Isra’ilawa zuwa ƙasar Kan’ana da na yi musu alkawari, kuma zan kasance tare da kai.’
Daga baya Jehobah ya gaya wa Musa ya hau can saman Dutsen Nebo a ƙasar Mowab. Daga nan Musa zai iya ganin ketaren Kogin Urdun kuma ya ga kyakkyawar ƙasar Kan’ana. Jehobah ya ce: ‘Wannan ita ce ƙasar da na yi alkawari zan bai wa ’ya’yan Ibrahim, da Ishaku da Yakubu. Na ƙyale ka ka gani, amma ba zan ƙyale ka ka shiga ba.’
A can kan Dutsen Nebo Musa ya mutu. Yana da shekara 120. Har ila yana da ƙarfi, kuma idanunsa ba su dushe ba. Mutane suka yi baƙin ciki suka yi ta kuka domin Musa ya mutu. Amma sun yi farin ciki da Joshua ne ya zama sabon shugabansu.
Litafin Lissafi 27:12-23; Kubawar Shari’a 3:23-29; 31:1-8, 14-23; 32:45-52; 34:1-12.