Yadda Za Mu Yi Wa’azi
●○○ HAƊUWA TA FARI
Tambaya: Ta yaya muka sani cewa wahalar da muke sha ba horo ba ne daga Allah?
Nassi: Yak 1:13
Tambaya don Ziyara ta Gaba: Me ya sa muke shan wahala?
○●○ KOMAWA ZIYARA TA FARKO
Tambaya: Me ya sa muke shan wahala?
Nassi: 1Yo 5:19
Tambaya don Ziyara ta Gaba: Yaya Allah yake ji game da matsalolin da muke fuskanta?
○○● KOMAWA ZIYARA TA BIYU
Tambaya: Yaya Allah yake ji game da matsalolin da muke fuskanta?
Nassi: Ish 63:9
Tambaya don Ziyara ta Gaba: Ta yaya Allah zai kawo ƙarshen mugunta?