RAYUWAR KIRISTA
Yadda Za Ka Iya Yin Nazari Mai Zurfi
Kamar Daniyel, za ka so ka riƙe amincinka sa’ad da aka jarraba ka? Daniyel ya yi nazari mai zurfi na Kalmar Allah har da annabci masu wuya sosai. (Da 9:2) Za ka iya riƙe amincinka idan kana nazari mai zurfi na Littafi Mai Tsarki. Ta yaya? Nazari zai sa ka ƙara gaskata da alkawuran Allah. (Jos 23:14) Zai sa ka ƙaunaci Allah sosai, kuma za ka riƙa yin abin da ya dace. (Za 97:10) Amma daga ina za ka soma nazarin? Ka lura da waɗannan shawarwarin.
-
Mene ne zan yi nazari a kai? Nazari mai kyau ya haɗa da yin shiri don taro. Za ka ji daɗin karatun Littafi Mai Tsarki da ake yi kowane mako idan kana nazari da kuma bincika abubuwan da ba ka gane ba. Ban da haka, wasu suna yin nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki ko ’ya’yan ruhu mai tsarki ko tafiye-tafiyen da Bulus ya yi ko kuma halittun Jehobah. Idan ka yi tunani a kan wata tambaya ta Littafi Mai Tsarki, ka rubuta ta a ranar kuma ka sa ta zama abin da za ka yi bincike a kai.
-
Da mene ne zan yi bincike? Don ka ga wasu cikinsu, ka kalli bidiyon nan Kayan Bincike Don Nazarin Littafi Mai Tsarki. Ka yi bincike a kan dabbobin da aka ambata a Daniyel sura 7 don ka san mulkokin da dabbobin suke wakilta.
-
Awa nawa ne zan yi ina nazari? Yin nazari a kai a kai yana ƙarfafa dangantakarmu da Allah. Da farko, kana iya amfani da gajeren lokaci wajen yin nazari. Daga baya, kana iya ƙara yawan lokacin da kake amfani da shi. Yin nazarin Kalmar Allah kamar neman gwal yake. Idan kana samun bayanai masu tamani, za ka ci gaba da nema! (Mis 2:3-6) Za ka so Kalmar Allah sosai kuma za ka riƙa nazarinta a kai a kai.—1Bi 2:2.
MENE NE DABBOBIN DA KE DANIYEL SURA 7 SUKE WAKILTA?
-
Da 7:4
-
Da 7:5
-
Da 7:6
-
Da 7:7
ƘARIN TAMBAYA:
Ta yaya Daniyel 7:8, 24 suka cika?
AIKI NA GABA:
Mene ne dabbobin da ke Ru’ya ta Yohanna sura 13 suke wakilta?