Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Rika Ajiye “Wani Abu”

Ku Rika Ajiye “Wani Abu”

Bai kamata mu riƙa yin gudummawa yadda muka ga dama kawai ba. A maimakon haka, kamar yadda manzo Bulus ya gaya mana, mu riƙa ajiye “wani abu” don yin gudummawa a kai a kai. (1Ko 16:2) Idan muna bin wannan shawarar, ibadarmu za ta sami ci gaba kuma za mu yi farin ciki. Ko da muna ganin abin da za mu bayar bai da yawa, Jehobah yana alfahari da ƙoƙarin da muke yi wajen ba da abin da za mu iya bayarwa.—K. Ma 3:9.

KU KALLI BIDIYON NAN MUN GODE DA SHIRIN DA KUKE YI DON BA DA GUDUMMAWA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne amfanin yin shiri kafin mu ba da gudummawa?

  • Ta yaya wasu suke ajiye “wani abu” don ba da gudummawa?