Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Yadda Za A Yi Taron Fita Wa’azi da Kyau

Yadda Za A Yi Taron Fita Wa’azi da Kyau

Kamar sauran taronmu, Jehobah yana so mu riƙa halartar taron fita wa’azi don mu ƙarfafa juna. (Ibr 10:24, 25) Ya kamata a riƙa taron cikin minti biyar zuwa bakwai, kuma haka ya haɗa da shirya yadda za a yi wa’azin da wuraren da za a je da kuma addu’a. (Idan kuma bayan taron ikilisiya ne za a yi, zai dace a yi shi kasa da minti biyar zuwa bakwai.) Ya kamata mai gudanar da taron ya shirya abin da zai ƙarfafa waɗanda za su je wa’azi. Alal misali, zai yi kyau a tattauna abin da za a faɗa a wa’azi a ranar Asabar a lokacin da mutane da yawa da suka zo taron ba su je wa’azi ba har na mako guda. Waɗanne batutuwa ne kuma zai dace a tattauna?

  • Yadda za mu yi wa’azi daga Littafin Taro Don​—Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu

  • Yadda za a yi amfani da labarai ko abubuwan da ke faruwa don a soma tattaunawa da mutum

  • Yadda za mu amsa sa’ad da mutum ya ba da wata hujjar da aka saba bayarwa a yankin

  • Yadda za mu amsa wa mutumin da ya ce ba Allah, ko wanda ya yi imani da juyin halitta, ko wanda yake yin wani yare, ko kuma wanda addininsa ya yi dabam da wanda aka saba gani a yankinku

  • Yadda za mu yi amfani da wani shafi a dandalin jw.org ko manhajar JW Library® ko kuma Littafi Mai Tsarki a wa’azi

  • Yadda za mu yi amfani da littattafan da ke Kayan Aiki don Koyarwa

  • Yadda za mu yi wa’azi da waya ko rubuta wasiƙu ko wa’azi ga jama’a ko yadda za mu koma ziyara ko kuma nazari da mutane

  • Tunasarwa game da yadda za mu kāre kanmu ko yin wa’azi bisa ga yanayin da muka sami mutanen ko yadda za mu nuna halin kirki ko ra’ayin da ya dace da dai sauransu

  • Wani darasi ko bidiyo daga ƙasidar, Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa

  • Yadda za mu ƙarfafa kuma mu taimaka wa wanda muke wa’azi tare

  • Wani nassi da ya yi magana game da wa’azi ko wani labari da zai ƙarfafa ’yan’uwa