RAYUWAR KIRISTA
“Ba da Kyauta ga Jehobah”
Ta yaya za mu yi “bayarwa ta yardar rai” ga Jehobah a yau? (1Tar 29:5, 9, 14) Ga hanyoyi dabam-dabam da za mu iya bi don mu tallafa wa ayyukan da ƙungiyar Jehobah take yi a ikilisiyarmu da ma na faɗin duniya.
GUDUMMAWA DA AKE YI TA INTANE KO WANDA AKE SAKAWA A AKWATUNA SUNA TALLAFA WA:
-
AYYUKA DA MUKE YI A DUK DUNIYA
gina da kuma kula da manyan ofisoshinmu da ofisoshin fassara
kula da makarantunmu
kula da masu hidima ta musamman
tanadar da kayan agaji
shirya bidiyoyi, buga littattafai da kuma abubuwan da muke wallafawa a intane
-
KUƊAƊEN DA IKILISIYOYI SUKE KASHEWA
gyare-gyaren da ake yi da kuma kula da Majami’ar Mulki
wa’adi da ikilisiyoyi suka yi a kan yawan kuɗin da za a riƙa aika wa ofishinmu don:
-
gina Majami’un Mulki da kuma Majami’un manyan taro a dukan duniya
-
tsarin tallafawa a faɗin duniya
-
wasu ayyukan da ƙungiyar take yi a faɗin duniya
-
TARON YANKI DA NA DA’IRA
Ana amfani da duk gudummawar da aka yi a lokacin taron yanki wajen tallafa wa ayyukanmu a faɗin duniya. Daga cikin wannan gudummawar ne ake kula da dukan bukatun da suka taso a lokacin taron yanki ko taro na musamman ko kuma taro na ƙasashe.
Ana amfani da gudummawa da ake yi don taron da’ira wajen yin rancen wurin da za a yi taron, da kuma kula da wurin da dai sauransu. ’Yan’uwa a wannan da’irar suna iya zaɓan su ba da ƙarin kuɗi don a tallafa wa aikin da ake yi a faɗin duniya.