Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

16-22 ga Yuni

KARIN MAGANA 18

16-22 ga Yuni

Waƙa ta 90 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Ku Riƙa Ƙarfafa Waɗanda Suke Fama da Rashin Lafiya

(minti 10)

Ku yi magana da hikima (K. Ma 18:4; w22.10 22 sakin layi na 17)

Ku yi ƙoƙari ku fahimci yadda mutumin yake ji (K. Ma 18:13; mrt-E talifi na 19 akwati)

Ka zama aboki mai taimako da kuma haƙuri (K. Ma 18:24; wp23.1 14 sakin layi na 3–15 sakin layi na 1)

KA TAMBAYI KANKA, ‘Mene ne zan yi don in taimaka wa matata ko mijina da yake fama da ciwo?’

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • K. Ma 18:18—Me ya sa ake jefa ƙuriꞌa a zamanin dā? (it-2-E 271-272)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) K. Ma 18:​1-17 (th darasi na 11)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 1) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Mutumin ba ya jin yaren da kake yi. (lmd darasi na 2 batu na 5)

5. Komawa Ziyara

(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Mutumin ya ce ka taƙaita saƙon don bai da lokaci. (lmd darasi na 7 batu na 4)

6. Komawa Ziyara

(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka koya wa mutumin wani abu game da Mulkin Allah. (lmd darasi na 9 batu na 5)

7. Ka Bayyana Imaninka

(minti 4) Gwaji. ijwfq talifi na 29—Jigo: Kun Yarda da Cewa Allah Ya Halicci Kome Cikin Sa’o’i 24 a Kwana Shida? (lmd darasi na 5 batu na 5)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 144

8. Ku Taimaka ma Waɗanda Kuke Ƙauna Su Kusaci Jehobah ta ‘Halinku Mai Kyau’

(minti 15) Tattaunawa.

Da yawa a cikinmu mun san wani da za mu ji daɗi da a ce yana bauta wa Jehobah, kamar abokin aurenmu ko ɗanmu ko abokanmu da suka bar Jehobah. Shin, akwai lokacin da ka taɓa tilasta ma wani da ba ya bauta ma Jehobah ko ka yi masa wani furuci ba tare da basira ba don kana ganin hakan zai sa ya soma bauta wa Jehobah? Ko da yake burinmu shi ne mu taimaka musu, amma idan muka yi magana ba tare da tunani ba, hakan ba zai taimaka musu ba. (K. Ma 12:18) To, wace hanya ce ta fi dacewa mu taimaka musu?

Kalmar Allah a 1 Bitrus 3:1 ta bayyana cewa waɗanda mazansu ba sa bauta wa Jehobah za su iya soma bauta ma Jehobah “ko ba a yi musu magana ba.” Ta yaya? Idan mazan sun lura da halaye masu kyau na matansu kamar ƙauna da alheri da kuma hikima, hakan zai iya sa su canja raꞌayinsu kuma su soma bauta ma Jehobah. (K. Ma 16:23) Halayenmu masu kyau da kuma alherin da muke yi zai iya sa wanda ba ya bauta wa Jehobah ya soma yin hakan.—w10 6/15 20-21 sakin layi na 4-6.

Ku kalli BIDIYON Suna Dagewa Wajen Kiyaye Bangaskiyarsu—Wadanda Abokan Aurensu Ba Shaidu Ba. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Me ka koya daga labarin ꞌYarꞌuwa Sasaki?

  • Me ka koya daga labarin ꞌYarꞌuwa Ito?

  • Me ka koya daga labarin ꞌYarꞌuwa Okada?

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 60 da Adduꞌa