Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KU YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Yin Koyarwa da Himma

Yin Koyarwa da Himma

Idan muna da himma, hakan zai iya shafan mutane. Zai sa mutane su saurari abin da muke cewa. Ƙari ga haka, yana nuna cewa muna daraja saƙonmu. Ko da yaya al’adarmu ko halinmu yake, za mu iya kasancewa da himma. (Ro 12:11) Ta yaya za mu yi hakan?

Da farko, ka yi tunani a kan muhimmancin saƙon da kake so ka idar. An ba ka babban aiki na kai wa mutane “labari mai daɗi.” (Ro 10:15) Na biyu, ka yi tunani a kan yadda wa’azinka zai kyautata rayuwar mutane. Suna bukatar su ji abin da kake so ka faɗa. (Ro 10:​13, 14) A ƙarshe, ka yi magana da himma kuma yanayin fuskarka da yadda kake motsa hannayenka su yi daidai da abin da kake faɗa.

KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN INGANTA YADDA KUKE WA’AZI​—KU RIƘA KOYARWA DA HIMMA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya sa Anita ta daina kasancewa da himmar yin nazari da Rose?

  • Me ya taimaka wa Anita ta soma kasancewa da himma?

  • Idan muna da himma, hakan zai iya shafan mutane

    Me ya sa ya dace mu mai da hankali ga halaye masu kyau na masu sauraronmu?

  • Ta yaya himmar da muke da ita take shafan ɗalibanmu da kuma wasu?