FARAWA 38-39
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH |Jehobah Bai Bar Yusuf Ba
39:1, 12-14, 20-23
Duk da matsalolin da Yusuf ya fuskanta, Jehobah ya sa duk abin da ya yi “ya yalwata” kuma ya sa ya yi “farin jini a idon shugaban masu gadin ’yan kurkukun.” (Fa 39:2, 3, 21-23) Wane darasi ne muka koya daga hakan?
-
Idan muna fuskantar matsaloli, hakan ba ya nufin cewa Jehobah bai amince da mu ba.—Za 34:19
-
Zai fi kyau mu riƙa tunani a kan abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi mana kuma mu gode masa.—Fib 4:6, 7
-
Mu roƙi Jehobah ya taimaka mana.—Za 55:22