FARAWA 6-8
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH |“Ya Yi Kome Daidai”
6:9, 13-16, 22
Nuhu da iyalinsa ne suka gina babban jirgin kuma a lokacin, babu kayan aiki ko tsarin gini na zamani. Hakan ba ƙaramin aiki ba ne.
-
Jirgin yana da girma sosai. Tsawonsa wajen kafa 437 ne, faɗinsa kafa 73 ne, tsayinsa kuma kafa 44 ne
-
Suna bukatar su sare bishiyoyi, su gyara su yadda yakamata kuma su saka su a inda ya dace
-
Suna bukatar su shafa kwalta a ciki da waje na jirgin
-
Suna bukatar su tara abincin da su da kuma dabbobin za su ci har na shekara ɗaya
-
Mai yiwuwa sun yi shekara 40 zuwa 50 kafin su kammala wannan aikin
Ta yaya wannan labarin zai taimaka mana mu yi wa Jehobah biyayya a lokacin da yin hakan yake da wuya?