Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYYUKAN MANZANNI 27-28

Bulus Ya Je Roma

Bulus Ya Je Roma

27:23, 24; 28:1, 2, 16, 17

Duk da cewa an saka Bulus a fursuna, bai daina yin wa’azi ba. Sa’ad da yake cikin jirgin ruwa, ya yi wa masu tuƙa jirgin da kuma abokan tafiyarsa wa’azi. Bayan jirgin ya kife a Tsibirin Malta, babu shakka Bulus ya yi wa waɗanda ya warkar da su wa’azi. Bayan kwana uku da isar sa Roma, ya kira malaman Yahudawa da yawa don ya yi musu wa’azi. A lokacin da aka tsare Bulus a wani gida har na shekara biyu, ya yi wa duk waɗanda suka zo wurin sa wa’azi.

Me za ka iya yi don ka yi wa’azi duk da mawuyanci yanayin da kake ciki?