Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Yadda Ma’aurata Za Su Karfafa Aurensu

Yadda Ma’aurata Za Su Karfafa Aurensu

Ibrahim da Saratu sun nuna yadda ya kamata ma’aurata su ƙaunaci juna su kuma daraja kansu. (Fa 12:​11-13; 1Bi 3:6) Duk da haka, su ma sun fuskanci matsaloli a aurensu, amma sun jimre sa’ad hakan ya faru. Waɗanne darussa ne ma’aurata za su koya idan suka bincika labarin Ibrahim da Saratu?

Ku riƙa tattaunawa da juna. Zai dace ma’aurata su amsa cikin lumana idan wani cikinsu ya yi magana cikin fushi. (Fa 16:​5, 6) Ya kamata su riƙa keɓe lokaci don su riƙa shakatawa tare. Zai dace su riƙa nunawa ta furucinsu da abubuwan da suke yi cewa suna ƙaunar juna. Mafi muhimmanci ma, zai dace su riƙa nazari da addu’a da ibada tare don Jehobah ya riƙa taimaka musu. (M. Wa 4:12) Idan ma’aurata suka ƙarfafa aurensu, hakan yana ɗaukaka Jehobah wanda ya kafa aure.

KU KALLI BIDIYON NAN YADDA ZA KU ƘARFAFA GAMIN AURE, SA’AN NAN KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • A bidiyon nan, me ya nuna cewa Shaan da Kiara ba sa ba wa juna lokaci kamar yadda suka saba?

  • Me ya sa bai dace ma’aurata su riƙa ɓoye abin da yake damunsu ba?

  • Ta yaya labarin Ibrahim da Saratu ya taimaka wa Shaan da Kiara?

  • Waɗanne matakai ne Shaan da Kiara suka ɗauka don su ƙarfafa aurensu?

  • Me ya sa bai kamata ma’aurata su zata cewa ba za su fuskanci matsaloli a aurensu ba?

Za ku iya ƙarfafa aurenku!