RAYUWAR KIRISTA
Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Tambayoyi a Hanyoyin da Suka Dace
MUHIMMANCINSA: Idan “shawara a cikin zuciyar mutum tana kama da ruwa mai-zurfi,” tambayoyi za su iya jawo su kamar yadda ake jan ruwa daga rijiya da guga. (Mis 20:5) Yin tambayoyi yana sa waɗanda muke musu wa’azi su faɗi ra’ayinsu. Idan muka yi tambayoyi a hanyoyin da suka dace, amsar da mutanen za su bayar zai taimaka mana mu san ra’ayinsu. Yesu ya yi tambayoyi a hanyoyin da suka dace. Ta yaya za mu yi koyi da shi?
YADDA ZA MU CIM MA HAKAN:
-
Ka yi tambayoyin da za su sa mutane su faɗi ra’ayinsu. Yesu ya yi tambayoyi da yawa don ya san abin da ke zukatan almajiransa. (Mt 16:13-16; be-E 238 sakin layi na 3-5) Wace tambaya za ka yi don ka sa mutane su faɗi ra’ayinsu?
-
Ka yi tambayoyin da za su sa mutane su ba da amsar da ta dace. Yesu ya yi tambayoyi kuma ya tanadar da wasu amsoshin da suka taimaka wa Bitrus ya daidaita ra’ayinsa. (Mt 17:24-26) Waɗanne tambayoyi ne za ka yi don ka taimaka wa mutane su daidaita ra’ayinsu?
-
Ka yaba wa mutumin. A lokacin da wani malami ya ba da amsa mai kyau, Yesu ya yabe shi. (Mr 12:34) Ta yaya kai ma za ka yabi mutumin da ya amsa tambayar da ka yi?
KU KALLI SASHE NA FARKO NA BIDIYON NAN KU YI IRIN AIKIN DA YESU YA YI—KU KOYAR DA MUTANE, BAYAN HAKA, KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Me ya sa wannan hanyar koyarwar ba ta dace ba ko da yake abin da yake faɗa daidai ne?
-
Me ya sa bai kamata mu riƙa bayani kawai ba?
KU KALLI SASHE NA BIYU NA BIDIYON, BAYAN HAKA, KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Ta yaya ɗan’uwan nan ya yi tambayoyi a hanyoyin da suka dace?
-
Wane darasi kuma za mu iya koya daga wannan ɗan’uwan?