17-23 ga Disamba
AYYUKAN MANZANNI 15-16
Waƙa ta 96 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“An Ɗauki Mataki da Ya Yi Daidai da Kalmar Allah”: (minti 10)
A. M 15:1, 2—Batun kaciya ya so ya raba kan Kiristocin ƙarni na farko (mwbr18.12-HA an ɗauko daga bt 102-103 sakin layi na 8)
A. M 15:13-20—Hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a lokacin ta ɗauki mataki da ya jitu da Kalmar Allah (w12 1/15 5 sakin layi na 6-7)
A. M 15:28, 29; 16:4, 5—Hukuncin da hukumar ta yanke ya ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiya (mwbr18.12-HA an ɗauko daga bt 123 sakin layi na 18)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
A. M 16:6-9—Mene ne wannan labarin ya koya mana game da yin ƙwazo a hidimarmu? (w12 1/15 10 sakin layi na 8)
A. M 16:37—Ta yaya Bulus ya yi amfani da matsayinsa na ɗan Roma don ya yaɗa bishara? (mwbr18.12-HA an ɗauko daga nwtsty)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) A. M 16:25-40
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka fara da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Mutumin ya ba da hujja ta ƙin jin wa’azi da mutanen yankin suka saba bayarwa.
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Ka gabatar da kuma tattauna bidiyon nan (kada ka saka shi) Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?
Bidiyon Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 5) Ka nuna bidiyon kuma ku tattauna shi.
RAYUWAR KIRISTA
“Mu Yabi Jehobah Ta Wurin Rera Waƙa da Farin Ciki”: (minti 15) Tattaunawa. Ka nuna bidiyon nan Yara na Yabon Jehobah da Waƙoƙi. Sa’ad da kake kammalawa, ka gayyaci ’yan’uwa su tashi kuma su rera waƙa ta 084 Yin Hidima a Inda Akwai Bukata ta wajen bin sautin bidiyon.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 17 sakin layi na 11-22
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 102 da Addu’a