LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Disamba 2017
Gabatarwa
Yadda za a iya ba da mujallar Awake! da kuma koya wa mutane gaskiya game da matattu. Ka yi amfani da misalan nan don ka rubuta taka gabatarwar.
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Bidi Jehobah Kafin Ranar Fushinsa
Wajibi ne mu bi umurnin da Zafaniya ya ba wa Isra’ilawa idan muna son Jehobah ya cece mu a ranar fushinsa.
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
‘Ku Rike Rigar Bayahude’
Mutane daga al’ummai dabam-dabam suna bauta wa Jehobah tare da shafaffun Kiristoci. A wadanne hanyoyi ne kuma za ka iya taimaka ma shafaffun Kiristoci?
RAYUWAR KIRISTA
Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Wa’azi ga Kowa a Yankinmu
Muna son mu gaya wa kowa albishiri a yankinmu. Amma ta yaya za mu iya yin hakan?
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Kasance a “Kwarin Duwatsu”
Mene ne “kwarin duwatsu” yake nufi? Ta yaya mutane suke gudawa zuwa wurin?
RAYUWAR KIRISTA
Wani Sabon Fasali a Taron Tsakiyar Mako
Ka yi amfani da karin bayanai da hotuna da kuma bidiyoyin da ke New World Translation of the Holy Scriptures na nazari don ka inganta nazarinka kuma ka kara kusantar Jehobah.
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Aurenku Na Faranta wa Jehobah Rai Kuwa?
A zamanin Malakai, Jehobah bai amince da ibadar mutanen da suka ci amanar matarsu ko mijinsu ba. Ta yaya ma’aurata a yau za su kasance da aminci?
RAYUWAR KIRISTA
Mece ce Kauna ta Gaskiya?
Jehobah yana son ma’aurata su zauna tare bar abada. Ya ba mu ka’idodin da zai taimaka mana mu nemi abokin aure da ya dace da kuma zai sa mu ji dadin aurenmu.