Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ayyukan Kirki da Jehobah Ba Zai Manta da Su Ba

Ayyukan Kirki da Jehobah Ba Zai Manta da Su Ba

Dukan bayin Jehobah za su iya yin ayyukan da Jehobah ba zai manta da su ba har abada. Kamar yadda uba ba ya mantawa da ayyuka masu kyau da yaransa suka yi, haka ma Jehobah ba zai manta da ayyuka masu kyau da muka yi da kuma ƙaunar da muka nuna masa ba. (Mt 6:20; Ibr 6:10) Ko da yake yanayinmu ya bambanta, amma idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu bauta ma Jehobah, za mu yi farin ciki sosai. (Ga 6:4; Kol 3:23) Shekaru da yawa yanzu, dubban ’yan’uwa maza da mata sun yi hidima a Bethel. Shin za ka iya yin hidima a Bethel? Idan ba za ka iya ba, za ka iya ƙarfafa wani ya yi hidima a Bethel ko ka taimaka ma wani da yake hidima a Bethel ya ci gaba da yin hidimarsa?

KU KALLI BIDIYON NAN KU BA DA KANKU DON KU YI HIDIMA A BETHEL, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Wane abu ne ya kamata ya sa mutum ya so yin hidima a Bethel?

  • Wace albarka ce wasu suka ce sun samu don hidimar da suke yi a Bethel?

  • Waɗanne abubuwa ne za su sa mutum ya cancanci yin hidima a Bethel?

  • Me za ka yi don ka iya yin hidima a Bethel?