RAYUWAR KIRISTA
Ku Tuna da Matar Lutu
Me ya sa matar Lutu ta kalli baya sa’ad da suke barin Saduma? Littafi Mai Tsarki bai gaya mana dalilin ba. (Fa 19:17, 26) Amma gargaɗin da Yesu ya yi ya nuna cewa wataƙila ta tuna da abubuwan da ta bari a garin Saduma ne. (Lu 17:31, 32) Ta yaya za mu guji bin misalinta? Wajibi ne mu guji saka kayan duniya farko a rayuwarmu. (Mt 6:33) Yesu ya ce ba za mu iya ‘sa ranmu ga bin Allah da kuma son kuɗi a lokaci ɗaya’ ba. (Mt 6:24) Amma me za mu yi idan muka ga cewa kayan duniya sun soma janye hankalinmu daga ibada? Mu yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka mana mu ga inda muke bukatar mu yi gyara kuma ya ba mu ƙarfin hali don mu yi gyarar.
KU TUNA DA BIDIYON NAN KU TUNA DA MATAR LUTU, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
-
Ta yaya matsin da aka yi wa Gloria ya shafi tunaninta da furucinta da kuma ayyukanta?
-
Ta yaya matar Lutu ta zama misali a gare mu yau?
-
Ta yaya bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa Joe da iyalinsa?
-
Ta yaya abokan aikin Anna suka sa ta daina mai da hankali a ayyuka na ibada?
-
Me ya sa muke bukatar ƙarfin hali idan ana matsa mana mu nemi kuɗi ruwa a jallo?
-
Ta yaya Brian da Gloria suka soma bauta wa Jehobah kamar yadda suke yi a dā?
-
Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne aka yi amfani da su a bidiyon nan?