28 ga Agusta–3 ga Satumba
EZEKIYEL 39-41
Waƙa ta 107 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Yadda Wahayin Ezekiyel Game da Haikali Ya Shafe Ka”: (minti 10)
Eze 40:2—An ɗaukaka bautar Jehobah fiye da dukan sauran bauta (w99 3/1 17 sakin layi na 16)
Eze 40:3, 5—Jehobah zai cika alkawarinsa na maido da bauta ta gaskiya (w07 8/1 30 sakin layi na 9)
Eze 40:10, 14, 16—Wajibi ne mu bi ƙa’idodin Jehobah idan muna so mu bauta masa yadda ya kamata (w07 8/1 31 sakin layi na 6)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Eze 39:7—Ta yaya ’yan Adam suke ɓata sunan Allah sa’ad da suke ɗora masa laifi don wahalar da muke sha? (w12 10/1 12 sakin layi na 2)
Eze 39:9—Bayan yaƙin Armageddon, mene ne zai faru da makaman yaƙi da al’ummai suka ƙera? (w90 6/1 11 sakin layi na 20)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Eze 40:32-47
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) fg darasi na 1 sakin layi na 1—Ka soma da gabatar da bidiyon nan Za Ka So Ka Ji Albishiri? (kada ka nuna bidiyon) Sai ka ba da ƙasidar.
Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) fg darasi na 1 sakin layi na 2—Ka yi shiri don ziyara ta gaba.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) fg darasi na 1 sakin layi na 3-4
RAYUWAR KIRISTA
Waƙa ta 145
“Yaushe Ne Zan Sake Yin Hidimar Majagaba Na Ɗan Lokaci?”: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka bidiyon nan Da Taimakon Jehobah, Zan Iya Yin Kome.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) kr babi na 17 sakin layi na 1-9
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 92 da Addu’a