RAYUWAR KIRISTA
Ku Kasance da Halaye Masu Kyau—Karfin Hali
ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI:
-
Muna bukatar ƙarfin hali a wa’azi.—A. M. 5:27-29, 41, 42
-
Za a san ko muna da ƙarfin hali a lokacin ƙunci mai girma.—Mt 24:15-21
-
Tsoron mutane zai iya jefa mu cikin matsala.—Irm 38:17-20; 39:4-7
YADDA ZA KA KASANCE DA HALIN:
-
Ka yi bimbini a kan yadda Jehobah yake ceton bayinsa.—Fit 14:13
-
Ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin hali.—A. M. 4:29, 31
-
Ka dogara ga Jehobah sosai.—Za 118:6
KU KALLI BIDIYON NAN KU GUJI ABUBUWAN DA ZA SU SA KU ZAMA MARASA AMINCI—JIN TSORON MUTUM, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
-
Me ya sa kasancewa da ƙarfin hali yake da muhimmanci sosai a wa’azi?
-
Mene ne aka ambata a littafin Misalai 29:25?
-
Me ya sa muke bukatar mu kasance da ƙarfin hali tun yanzu?