Ta Hannun Matiyu 26:1-75

  • Firistoci sun ƙulla su kashe Yesu (1-5)

  • An zuba wa Yesu mān ƙamshi (6-13)

  • Bikin Ƙetarewa na ƙarshe da cin amanar Yesu (14-25)

  • Yesu ya kafa Abincin Yamma na Ubangiji (26-30)

  • Yesu ya ce Bitrus zai yi mūsun sanin sa (31-35)

  • Yesu ya yi adduꞌa a Getsemani (36-46)

  • An kama Yesu (47-56)

  • An yi masa shariꞌa a gaban membobin Sanhedrin (57-68)

  • Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu (69-75)

26  Saꞌad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwan, sai ya ce wa almajiransa: 2  “Kamar yadda kuka sani, nan da kwana biyu, za a yi Bikin Ƙetarewa, kuma za a ba da Ɗan mutum don a kashe shi a kan gungume.” 3  Sai manyan firistoci da dattawan jamaꞌa suka taru a farfajiyar* gidan shugaban firistoci mai suna Kayafa. 4  Sun ƙulla yadda za su kama Yesu da wayo kuma su kashe shi. 5  Amma suna cewa: “Kada mu kama shi a lokacin bikin, domin kada mutane su ta da hayaniya.” 6  Da Yesu yake Betani a gidan Siman, wanda a dā kuturu ne, 7  sai wata mata ta zo wurin Yesu da kwalba* da ke ɗauke da mān ƙamshi mai tsada sosai, kuma ta soma zuba mān a kansa yayin da yake cin abinci. 8  Da almajiransa suka ga haka, sai suka yi fushi sosai suka ce wa junansu: “Wace irin ɓarna ce wannan? 9  Ai da za a iya sayar da mān da tsada sosai, kuma a ba wa talakawa kuɗin.” 10  Da yake Yesu ya san abin da suke faɗa, sai ya ce musu: “Me ya sa kuke damun matar nan haka? Abu mai kyau ne ta yi mini. 11  Domin a kullum kuna tare da talakawa, amma ni ba zan kasance da ku kullum ba. 12  Saꞌad da ta zuba mān ƙamshin nan a jikina, ta yi hakan ne don ta shirya jikina da za a binne. 13  A gaskiya ina gaya muku, a duk inda za a yi shelar labari mai daɗin nan a dukan duniya, za a riƙa faɗin abin da matar nan ta yi don tunawa da ita.” 14  Sai ɗaya daga cikin almajiransa goma sha biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyoti ya je wurin manyan firistoci, 15  kuma ya ce musu: “Mene ne za ku ba ni, idan na taimaka muku ku kama shi?” Sai suka ce za su ba shi azurfa talatin. 16  Don haka, daga lokacin, ya ci-gaba da neman dama mai kyau da zai ci amanar Yesu. 17  A ranar farko ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran Yesu suka zo wurinsa suka ce masa: “Ina kake so mu je mu shirya maka ka ci abincin Bikin Ƙetarewa?” 18  Sai ya ce musu: “Ku shiga cikin gari wurin wani mutum kuma ku ce masa, ‘Malam ya ce: “Lokacina ya yi kusa, kuma zan yi Bikin Ƙetarewa a gidanka tare da almajiraina.”’” 19  Sai almajiran kuwa suka yi yadda Yesu ya ce su yi, suka kuma shirya Bikin Ƙetarewa. 20  Da yamma ta yi, ya zauna yana cin abinci a teburi tare da almajiransa goma sha biyu. 21  Yayin da suke cin abinci, sai ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, ɗaya daga cikinku zai ci amanata.” 22  Sai almajiran suka damu sosai, kuma suka soma tambayar sa ɗaya bayan ɗaya, suna cewa: “Ubangiji ni ne?” 23  Sai ya amsa ya ce: “Wanda yake cin abinci tare da ni a kwano ɗaya, shi ne wanda zai ci amanata. 24  Hakika, Ɗan mutum zai mutu kamar yadda aka rubuta game da shi, amma kaiton wanda ta wurin shi ne za a ci amanar Ɗan mutum, zai fi wa mutumin nan da ma ba a haife shi ba.” 25  Yahuda, wanda yake dab da cin amanarsa ya ce: “Malam ni ne?” Sai Yesu ya ce masa: “Kai da kanka ma ka faɗa.” 26  Yayin da suka ci-gaba da cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, bayan ya yi godiya ga Allah, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, ya ce: “Ku karɓa ku ci, wannan yana wakiltar jikina.” 27  Ya kuma ɗauki kofi, ya yi godiya, sai ya ba su, kuma ya ce: “Ku sha dukanku, 28  wannan yana wakiltar ‘jinina na alkawari,’ wanda za a zubar a madadin mutane da yawa don gafarar zunubai. 29  Ina gaya muku: Ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba, sai dai a ranar da zan sha wani sabo tare da ku a Mulkin Ubana.” 30  A ƙarshe, bayan da suka rera waƙoƙin yabo, sai suka fita suka tafi Tudun Zaitun. 31  Sai Yesu ya ce musu: “Dukanku za ku yi tuntuɓe saboda abin da zai faru da ni da daren nan, domin a rubuce yake cewa: ‘Zan bugi makiyayin, kuma tumakin garken za su watse.’ 32  Amma bayan da aka ta da ni daga mutuwa, zan je Galili in jira ku.” 33  Sai Bitrus ya amsa ya ce masa: “Ko sauran sun yi tuntuɓe saboda abin da zai faru da kai, ni kam ba zan taɓa yin tuntuɓe ba!” 34  Yesu ya ce masa: “A gaskiya ina gaya maka, a daren nan, kafin zakara ya yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” 35  Sai Bitrus ya ce masa: “Ko da zan mutu tare da kai ne, ba zan taɓa yin mūsun sanin ka ba.” Sauran almajiran Yesu ma, sun faɗi hakan. 36  Saꞌan nan Yesu ya zo wurin da ake kira Getsemani tare da almajiransa, kuma ya ce wa almajiransa: “Ku zauna a nan, zan je can in yi adduꞌa.” 37  Kuma ya tafi da Bitrus da ꞌyaꞌyan Zabadi guda biyu, sai ya soma damuwa sosai da kuma baƙin ciki. 38  Sai Yesu ya ce musu: “Damuwar da take raina, za ta iya kashe ni. Ku zauna a nan kuma ku ci-gaba da yin tsaro tare da ni.” 39  Da ya je gaba kaɗan, sai ya faɗi da fuskarsa a ƙasa, ya yi adduꞌa yana cewa: “Ubana, idan zai yiwu, ka ɗauke mini wannan kofi. Duk da haka, bari abin da kake so ya faru, ba abin da nake so ba.” 40  Saꞌad da ya dawo wurin almajiransa, kuma ya same su suna barci, sai ya ce wa Bitrus: “Ba za ku iya ci-gaba da yin tsaro da ni ko da na awa ɗaya ba? 41  Ku ci-gaba da yin tsaro da adduꞌa domin kada ku faɗi cikin jarraba. A gaskiya kam, zuciyar tana da niyya sosai, amma jikin ba ƙarfi.” 42  Sai ya sake komawa karo na biyu, ya yi adduꞌa yana cewa: “Ubana, idan ba zai yiwu a ɗauke mini wannan kofi ba tare da na sha shi ba, to, bari abin da kake so ya faru.” 43  Sai ya sake dawowa, ya same su suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi sosai. 44  Sai ya bar su, ya koma ya yi adduꞌa a karo na uku, yana maimaita abin da ya faɗa a baya. 45  Sai ya dawo wurin almajiransa, ya ce musu: “A lokaci kamar haka, kuna barci kuna hutawa! Ga shi! Lokaci ya yi da za a ci amanar Ɗan mutum kuma a ba da shi a hannun masu zunubi. 46  Ku tashi mu tafi. Don mai cin amanata ya yi kusa.” 47  Yayin da yake kan magana, sai ga Yahuda, ɗaya daga cikin almajiransa goma sha biyu, ya zo tare da jamaꞌa riƙe da takubba da sanduna. Manyan firistoci da dattawan jamaꞌa ne suka aiko su. 48  Wanda zai ci amanarsa ya riga ya ba su alama cewa: “Duk wanda na sumbace shi, shi ne mutumin; ku kama shi.” 49  Sai ya je wurin Yesu kai tsaye, ya ce masa: “Ina gaisuwa Malam!”* kuma ya sumbace shi. 50  Amma Yesu ya ce masa: “Abokina, me ya kawo ka nan?” Sai suka zo suka kama Yesu, kuma suka riƙe shi. 51  Amma ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu ya zare takobinsa, ya sari bawan shugaban firistoci kuma ya yanke masa kunne. 52  Sai Yesu ya ce masa: “Ka mai da takobinka gidansa, domin duk waɗanda suka ɗauki takobi, da takobi ne za a kashe su. 53  Ko kana ganin ba zan iya roƙan Ubana ya turo mini da rundunonin malaꞌiku fiye da goma sha biyu yanzu-yanzu ba? 54  Amma idan na yi haka, ta yaya za a cika Nassosi da suka ce hakan zai faru?” 55  A lokacin, sai Yesu ya ce wa jamaꞌar: “Shin kun fito ne ku kama ni da takubba da sanduna, sai ka ce ɗan fashi? A kullum, ina koyarwa a haikali, amma ba ku kama ni ba. 56  Duk abubuwan nan sun faru ne don rubuce-rubucen* annabawa su cika.” Sai dukan almajiran suka bar shi suka gudu. 57  Waɗanda suka kama Yesu, sun kai shi gidan Kayafa shugaban firistoci, wurin da marubuta da dattawa suka taru. 58  Amma Bitrus ya ci-gaba da bin su daga nesa, har zuwa farfajiyar gidan shugaban firistoci. Bayan da ya shiga gidan, ya zauna tare da masu hidima a gidan don ya ga abin da zai faru. 59  Manyan firistoci, da dukan membobin Sanhedrin* suna neman waɗanda za su zo su ba da shaidar ƙarya a kan Yesu da zai ba su damar kashe shi. 60  Amma ba su samu ko ɗaya ba, duk da cewa masu ba da shaidar ƙarya da yawa sun zo. Daga baya mutane biyu suka fito 61  kuma suka ce: “Mutumin nan ya ce, ‘Zan iya rushe wannan haikalin Allah, kuma in gina shi cikin kwana uku.’” 62  Sai shugaban firistoci ya tashi ya ce masa: “Ba za ka ce kome ba? Ba ka ji abin da mutanen nan suke faɗa a kanka ba?” 63  Amma Yesu ya yi shuru. Sai shugaban firistoci ya ce masa: “Na haɗa ka da Allah mai rai, ka gaya mana ko kai ne Kristi Ɗan Allah!” 64  Yesu ya ce masa: “Kai da kanka ma ka faɗa hakan. Amma ina gaya muku: Daga yanzu, za ku ga Ɗan mutum yana zaune a hannun dama mai iko kuma yana zuwa a cikin gajimaren sama.” 65  Sai shugaban firistoci ya yage mayafinsa, yana cewa: “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma muke bukata? Ga shi! Kun dai ji saɓon. 66  To, mene ne raꞌayinku?” Suka amsa suka ce: “Ya kamata a kashe shi.” 67  Sai suka tofa masa miyau a fuska, kuma suka yi ta masa naushi. Wasu kuma sun mammare shi, 68  suna cewa: “Tun da kai Kristi ne, ka gaya mana, wa ya mare ka?” 69  Bitrus yana zaune a wajen farfajiyar gidan, sai wata yarinya mai hidima a gidan ta zo ta same shi ta ce: “Kai ma kana tare da Yesu wannan mutumin Galili!” 70  Amma ya yi mūsu a gabansu duka, yana cewa: “Ban san abin da kike magana a kai ba.” 71  Saꞌad da ya fita zuwa ƙofar gidan,* sai wata yarinya dabam ta gan shi, ta ce ma waɗanda suke wurin: “Wannan mutumin ma yana tare da Yesu mutumin Nazaret.” 72  Sai ya sake yin mūsun sanin sa, har da rantsuwa yana cewa: “Ban san mutumin nan ba!” 73  Bayan ɗan lokaci, waɗanda suke tsaye a wurin suka zo suka sami Bitrus suka ce: “Ba shakka, kai ma ɗaya daga cikinsu ne, domin yadda kake magana* ya nuna hakan.” 74  Sai ya soma zagi da rantsuwa yana cewa: “Ban san mutumin nan ba!” Nan da nan zakara ya yi cara. 75  Sai Bitrus ya tuna abin da Yesu ya ce masa: “Kafin zakara ya yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi kuka sosai.

Hasiya

Ko kuma “filin da ke tsakiyar gidan.”
A yaren Girka, “kwalbar alabasta.” Wata ƙaramar kwalba ce da asali aka yi da dutse da ake samuwa kusa da yankin Alabastron a Masar.
A yaren Girka, “Rabbai.”
Ko kuma “nassosin.”
Sanhedrin shi ne Kotun Ƙolin Yahudawa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “zaure.”
Ko kuma “harshenka.”